HausaTv:
2025-12-02@07:16:11 GMT

Aljeriya: Taron Kasashen Afirka Kan Amincewa Da Mulkin Mallaka A Matsayin Laifi

Published: 2nd, December 2025 GMT

Wakilan kasashen Afirka da suka hallara a birnin Algiers sun sabunta wani yunkuri don amincewa da laifukan ‘yan  mulkin mallaka a hukumance, tare da ayyana mulkin mallaka a matsayin laifi kan bil’adama, da kuma tabbatar da an biya diyya bisa ga barna da cin zarafi da aka yi wa al’ummomin Afirka.

Taron, wanda aka gudanar a babban birnin Aljeriya, an gudanar da shi  ne bisa wani kuduri na Tarayyar Afirka (AU) da aka amince da shi a farkon wannan shekarar wanda ke kira da a yi adalci wajen biyan diyya don magance illolin siyasa, tattalin arziki, da zamantakewa da suka faru sakamakon mulkin mallaka.

Ministan Harkokin Wajen Aljeriya Ahmed Attaf ya ce tarihin Aljeriya a karkashin mamayar Faransa ya sanya kasar ta zama muhimmin wuri na taron. Ya jaddada cewa dole ne a dauki diyya a matsayin wajibi na shari’a, ba wata alama ta alheri ko taimako ba.

Ya kuma jaddada cewa Afirka tana da ikon neman a amince da laifukan da aka aikata wa al’ummarta a lokacin mulkin mallaka,” wanda ke ci gaba da aifar da matsaloli da koma baya a bangarori daban-daban a nahiyar sakamakon illoli na mulkin mallaka.

Tsakanin 1954 da 1962, Aljeriya ta sheda daya daga cikin yaƙe-yaƙe mafi muni da kuma zubar da jini da aka yi tsakaninta da  masu mulkin mallaka. An kashe dubban daruruwan mutanen kasar .

Attaf ya ce wahalhalun da Aljeriya ta fuskanta sun  kasance “abin koyi ne amma mai wahala, kuma ya zama wajibi ya zama mafari na soma neman hakkokin da aka saryar na al’ummar Afirka sakamakon zalunci na ‘yan mulkin mallaka.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Lebanon: An Gudanar Da Taron Musulunci da Kiristanci a Beirut tare da halartar Paparoma December 2, 2025 Chuck Schumer: Trump Ba Shi da Ikon Kaddamar da Yaki Kan Venezuela December 2, 2025 Najeriya: Matatar Dangote Za Ta Mika Tataccen Mai Lita Biliyan 1.5 A Watan Disamba December 2, 2025 Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Trump na ware Afirka ta Kudu daga G20 December 2, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 165 December 1, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan 164 December 1, 2025 Baqaei: Amurka Ce Babbar Barazana Ga Zaman Lafiya Da Tsaro A Duniya December 1, 2025 Paparoma Leo Na 14 Yana Ziyarar Aiki Na Kwanaki 3  A Kasar Lebanon December 1, 2025 Kamaru: Madugun Adawa Ya Rasu A Gidan Kaso December 1, 2025 Tawagar ECOWAS Ta Bar Guinea – Bissau bayan da shugaban kasar yayi barazanar korarsu Da Karfi December 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Ministan Harkokin Wajen Turkiya Ya Isa Birnin Tehran Kuma Ya Gana Da Takwaransa Na Iran

Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Turkiya ya iso birnin Tehran a jiya lahadi kuma  ya samu kyakkyawar tarba daga takwaransa na kasar iran Abbas Araqchi.

Ziyarar tasa ana saran za ta kara fadada dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ganin cewa dukkan kasashen biyu suna taka rawa a batutun da suka shafi yanki dama duniya baki daya.

Bugu da kari bayan ganawarsa da Araqchi da musayar ra’ayoyi kan batutuwa daban daban, zai gana da sauran manyan jami’an gwammnatin kasar, da ake saran za su tattauna kan alakar dake tsakaninsu da kuma irin ci gaban da aka samu a yankin da dai sauran batutuwa na kasa da kasa.

Ana sa bangaren shugaban kasar iran Masud pezeshkiyan a lokacin ganawarsa da Hakan fidan ministan harkokin wajen kasar turkiya ya jaddada game da muhimmancin hadin kan kasashen musulmi cikin gaggawa, yace ya kamata kasashen musulmi su rike duba yanayi da yan uwansu suke ciki, kuma a nisanci tsaurara alamura, adaidai lokacin da suke fuskantar matsin lamba daga kasashen waje.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Pezeshkian: Makiya na neman kawo cikas ga ci gaban kasashen Musulmi December 1, 2025 Shugaban Venezuela Ya Gargadi Amurka Game Da Kokarin Da Take yi Na Karbe Ikon Kula Da Rijiyoyin Mai Na Kasar December 1, 2025 Zanga zanga Ta Barke A Isra’ila Yayin Da Natanyaho Ke Neman Afuwa Kan Batun Cin Hanci Da Rashawa December 1, 2025 Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar Saudiya Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran. December 1, 2025 Lebanon: Sakon Kungiyar Hizbullah Ga Paparoma December 1, 2025 Ireland Ta Sauya Sunan Wurin Shakatawa Daga Na Shugaban  “Isra’ila” Zuwa Na Shahidiyar Falasdinu November 30, 2025  Gaza: Sau 590 “Isra’ila” Ta Keta Tsagaiwa Wutar Yaki November 30, 2025 Washington Post: Shirin Trump Na Kai Sojojin Gaza Yana Fuskantar Matsala November 30, 2025 MDD: Kasar Somaliya Tana Fuskantar Mawuyacin Yanayi Saboda Fari November 30, 2025 An Yi Ganawa A Tsakanin Ministocin Harkokin Wajen Iran Da Turkiya November 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Lebanon: An Gudanar Da Taron Musulunci da Kiristanci a Beirut tare da halartar Paparoma
  • Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Trump na ware Afirka ta Kudu daga G20
  • Tawagar ECOWAS za ta je Guinea-Bissau, bayan juyin mulkin soji
  • Ministan Harkokin Wajen Turkiya Ya Isa Birnin Tehran Kuma Ya Gana Da Takwaransa Na Iran
  • Pezeshkian: Makiya na neman kawo cikas ga ci gaban kasashen Musulmi
  • Cinikin Kasashen Waje na Iran Ya Zarce Dala Biliyan 76.5
  • An sake zabar Eto’o a matsayin Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Kamaru  
  • Iran da Kasashen Larabawa Sun Yi Allah wadai da kutsen sojojin Isra’ila a Kudancin Siriya
  • AU ta dakatar da Guinea-Bissau daga zama mamba a cikinta bayan juyin mulkin sojoji