Jagoran ‘Yan Jam’iyyar Democrat na Majalisar Dattawa Chuck Schumer ya zargi Shugaban Amurka Donald Trump da shirya  yaƙi a ɓoye a kan kasar Venezuela, yana mai jaddada cewa ikon ayyana yaƙi ya rataya ne kawai a kan Majalisa, kuma dan majalisar ya bayyana cewa zai  gabatar da kuduri  don hana tura sojojin Amurka yaki a Venezuela.

Schumer ya tabbatar da cewa Trump ba shi da ikon aika sojojin Amurka zuwa yaƙi ba tare da izinin Majalisa ba, yana mai bayyana  cewa wannan ikon an keɓe shi ne ga Majalisa kaɗai.

A cikin wata sanarwa, Schumer ya zargi Trump da shirin yaƙi a ɓoye da Venezuela, yana mai gargadin cewa Majalisa za ta ɗauki mataki nan take don gabatar da kuduri zai hana hana tura sojojin Amurka zuwa wannan yaki da yake Shirin kaddamarwa.

Schumer ya ce mutanen Amurka ba sa son wani yaƙi da ba a san karshensa ba,  ya ƙara da cewa duk wani mataki mai ƙarfi a kan Venezuela ba tare da amincewar majalisa ba zai zama babban kure da kuma sab awa doka.

A wani labarin kuma, Schumer ya bayyana cewa ya sami barazana ta imel,  daga abin da ya kira “MAGA” ko kuma (Make America Great Again) wato gungun da ke mara baya ido rufe ga siyasar Trump, kuma ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro a New York sun sanar da shi barazanar da aka yi lokuta daban-daban na dana bam a ofisoshinsa.

A ranar Asabar da ta gabata, shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa za a rufe sararin samaniyar Venezuela da yankin da ke kewaye da ita gaba daya.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya: Matatar Dangote Za Ta Mika Tataccen Mai Lita Biliyan 1.5 A Watan Disamba December 2, 2025 Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Trump na ware Afirka ta Kudu daga G20 December 2, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 165 December 1, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan 164 December 1, 2025 Baqaei: Amurka Ce Babbar Barazana Ga Zaman Lafiya Da Tsaro A Duniya December 1, 2025 Paparoma Leo Na 14 Yana Ziyarar Aiki Na Kwanaki 3  A Kasar Lebanon December 1, 2025 Kamaru: Madugun Adawa Ya Rasu A Gidan Kaso December 1, 2025 Tawagar ECOWAS Ta Bar Guinea – Bissau bayan da shugaban kasar yayi barazanar korarsu Da Karfi December 1, 2025 Yawan Yahudawan Da Suke Ficewa Daga HKI Sun Nininka Har Sau 100% December 1, 2025 Gaza: Fiye da Falasdinawa 350 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila tun bayan tsagaita wuta December 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

An Kammala Gasar ‘Rayan’ Na AI Ta Kasa Da Kasa A Nan Tehran

An kammala gasar gina manhajan komfuta ta kasa da kasa farko a jami’ar Amir Kabir take nan Tehran .

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, an gudanar da gasar ne  tsakanin kasashe 30 daga yankuna daban daban na duniya, kuma an kammala gasar a jiya Jumma’a 28 ga watan Nuwamban da muke ciki.

Gasar Rayan dai ita ce gasa na manhajan AI ko kirkirarren fasaha mafi girma a duniya. Gasa wanda yake samar da mahaja ya kula da ita tare da amfani da fasahar AI.

Gasar sharar fage ta Rayan wanda aka gudanar a dukkan jihohon Iran ya sami halattar mutane 30,000 daga kasashe 137 a duniya. Amma a gasa ta karshe da aka kammala mutane kimani 100 ne daga kasashen 30 suka sami halattar gasar.

Kasashen da suka halarci gasar sun hana da Amurka, Russia, China, India, Italy, Argentina, Chile, Poland, Romania, Singapore, Vietnam, Colombia, Armenia, Pakistan, Bangladesh, Afghanistan, Australia, Belarus, Serbia, Ethiopia, Ukraine, Taiwan, Kazakhstan, Slovakia, da kuma Iran.

Ministan fasaha da technoloji Hussain Afsheen yace Raya ta fi karfin gasa, sai dai shiri ne na adana fahinta da fasaha.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran da Kasashen Larabawa Sun Yi Allah wadai da kutsen sojojin Isra’ila a Kudancin Siriya November 29, 2025 MDD ta yi kira da a gudanar da cikakken bincike kan kisan gillar da aka yi wa Falasdinawa November 29, 2025 Lebanon ta shigar da kara ga Kwamitin Tsaro bayan Isra’ila ta Gina katanga a Yankinta November 29, 2025 AU ta dakatar da Guinea-Bissau daga zama mamba a cikinta bayan juyin mulkin sojoji November 29, 2025 Najeriya : An yi jana’izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi November 29, 2025 Larijani: Da’awar lalata karfin nukiliyar Iran wauta ce November 29, 2025 Babban banki Najeriya Ya Tura Dala Miliyan 50 Don Ƙarfafa Kasuwar Musayar Kudade November 29, 2025 Iran Da Kasashen Larabawa Sun Yi Tir Da Hare-Haren Isra’ila A Kan Kasar Siriya November 29, 2025 Ziyarar Da Larijani Ya Kai Pakistan Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Kara Dankon Zumunci November 29, 2025 Shaikh Niam Qasem: Hizbullah ce Za ta Mayar Da Martani Lokacin Da Ya Dace Kan Kisan Kwamandanta November 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Araghchi: Halayyar Amurka ce yin matsin lamba maimakon diflomasiyya a dangantaka ta kasa da kasa
  • Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Trump na ware Afirka ta Kudu daga G20
  • Baqaei: Amurka Ce Babbar Barazana Ga Zaman Lafiya Da Tsaro A Duniya
  • Shugaban venuzuwela Ya Gargadi Amurka Game Da Kokarin Da Take yi Na Karbe Ikon Kula Da Rijiyoyin Mai Na Kasar
  •  Sau 590 “Isra’ila” Ta Keta Tsagaiwa Wutar Yaki
  • Shugaban Pakistan Yayi Kira Da A Gudanar Da Bincike Kan Laifukan Yaki Da HKI Ke Tafkawa
  • Tinubu ya sake aike wa majalisa ƙarin sunayen jakadu 32
  • Trump Ya Bada Sanarwan Rufe Sararin Samaniyar Kasar Venezuela Gaba Daya
  • An Kammala Gasar ‘Rayan’ Na AI Ta Kasa Da Kasa A Nan Tehran