Jihar Jigawa Za Ta Hada Gwiwa Da Liberia Don Inganta Noman Shinkafa
Published: 13th, August 2025 GMT
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya karbi bakuncin Mataimakin Ministan Noma na Jamhuriyar Liberia, David Akoi, a wata ziyara ta musamman domin nazarin dabarun noman shinkafa a jihar, wadda ita ce kan gaba a fitar da shinkafa a Najeriya.
A yayin ziyarar ban girma a fadar gwamnati da ke Dutse, Mista Akoi ya ce wannan ziyara za ta ba tawagarsa damar fahimtar dabarun noma da sarrafa shinkafa, samun horo a aikace, tare da koyo game da dukkan sassan harkar noman shinkafa.
“A Liberia muna cin shinkafa safe, rana da dare. A shekarar 1979, an yi tarzomar shinkafa da ta kifar da gwamnatin Shugaba William R. Tolbert bayan yunkurin kara farashin shinkafa,” in ji shi. “Yanzu haka muna shigowa da kimanin kashi 70 cikin dari na shinkafar da muke ci.”
Ya ce gwamnatin Liberia ta kuduri aniyar samar da aƙalla kashi 70 cikin dari na bukatar shinkafar cikin gida. Ya bayyana cewa Shugaba Joseph Boakai ya zabi Najeriya, musamman Jihar Jigawa, saboda irin ci gaban da ta samu a harkar noman shinkafa.
“Mun zo ne domin koyo daga Jigawa yadda ta samu wannan nasara, da dabarun da ta yi amfani da su wajen shawo kan matsalolin noma.” In ji shi. “Manufarmu ita ce mu aiwatar da irin wannan nasara a kasarmu.”
Da yake mayar da martani, Gwamna Namadi ya yaba wa Liberia bisa zaben Jigawa, yana mai cewa wannan hadin gwiwa zai bai wa bangarorin biyu damar musayar dabaru da gogewa da za su amfani bangarorin noman su. Ya jaddada cewa noma ita ce ginshikin tattalin arzikin Jigawa.
“A shekarar 2023, Jigawa na noman kadada 60,000 zuwa 70,000 na shinkafa. Amma a 2024, mun kai sama da kadada 200,000, kuma bana muna fatan kaiwa kadada 300,000. Burinmu shi ne mu samar da kashi 50 cikin dari na shinkafar da Najeriya ke bukata nan da 2030,” in ji shi.
Gwamnan ya bayyana cewa jihar na mai da hankali kan noman rani domin rage illar sauyin yanayi. “Muna gyara madatsun ruwa 10 da ke jihar, wanda hakan ke kara fiye da kadada 4,500 ga filayen noma,” In ji shi.
Don kara yawan amfanin gona, gwamnatin jihar ta samar da sababbin taraktoci 300 da kayayyakin aikin su, injinan girbi 60, injinan shuka 150, da sauran kayan noma na zamani. Kowacce cikin mazabu 30 a jihar tana da akalla taraktoci 10 da ake ba manoma kananan haya a farashi rahusa rahusa.
Gwamna Namadi ya tabbatar da cewa Jigawa za ta ci gaba da zuba jari a harkokin noma na zamani don karfafa sashen shinkafa, tare da bai wa Liberia goyon baya a yunkurinta na cimma wadatar shinkafa a cikin gida.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Ta’adda Sun Kashe Jama’a A Kauyukan Sakkwato
Wani sabon rikici ya barke a jihar Sokoto inda ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a kauyen Marnouna da ke karamar hukumar Wurno, inda suka kashe akalla mutum daya tare da yin awon gaba da wasu da ba a tantance adadinsu ba a lokacin da ake sallar isha.
Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Sokoto, Alhaji Isah Sadik Achida, wanda ya fito daga yankin ya tabbatar da faruwar harin inda ya jaddada cewa maharan sun kuma kashe shugaban kungiyar masu sayar da babura na yankin a yayin farmakin.
Achida ya ci gaba da cewa, kwana biyu kacal kafin harin masallacin, ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyuka biyu da ke makwabtaka da su, Gidan Taru da Kwargaba, inda suka yi garkuwa da wasu mazauna garin tare da jaddada cewa ‘yan bindigar sun kuma kashe wani dan uwa tare da kama iyalansa baki daya.
A cewar shugaban jam’iyyar APC, ‘yan ta’addan na kokarin kafa sansani a yankin domin fadada ayyukansu.
Achida ya tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnatin jihar da jami’an tsaro suna bakin kokarinsu domin yakar matsalar.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato, ASP Abubakar Rufa’i, ya tabbatar wa gidan rediyon Najeriya faruwar lamarin inda ya ce a yanzu ‘yan fashin na kai hare-hare a lokutan damina domin kai hare-haren ba tare da an gano su ba.
NASIR MALALI