Tsaro: Gwamnatin Kano za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa a iyakokinta
Published: 3rd, December 2025 GMT
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa na shirin sayen jirage marasa matuƙa da wasu kayan aiki domin kare yankunan da ke iyakar Kano da Katsina.
Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Gobara ta ƙone kasuwar katako a Abuja CBN ya kara yawan kudin da mutum zai iya cirewa a mako zuwa N500,000Gwamna Abba, ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci sansanin rundunar haɗin gwiwa ta JTF, domin ganin yadda suke shirin kare al’umma daga hare-haren ’yan bindiga a yankunan Tsanyawa da Shanono.
Ya roƙi al’ummar yankunan da abin ya shafa da su riƙa bai wa jami’an tsaro bayanai masu amfani game da duk wani motsi na ’yan bindiga.
Gwamnan ya ce ya kai wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ziyara, domin neman taimako kan lamarin, inda shugaban ya amince da buƙatar da aka gabatar masa cikin gaggawa.
Ya umarci dakarun JTF da su yi duk mai yiwuwa wajen ceto mutanen da aka sace a Tsanyawa da Shanono.
“Mun san cewa waɗannan hare-hare sun jawo asarar rayuka, wasu kuma an yi garkuwa da su. Insha Allah za a ceto su,” in ji shi.
Gwamna Abba ya ce sun kai wannan ziyara ne domin fahimtar halin tsaron yankin da kuma ƙarfafa guiwar jami’an tsaro.
Ya ƙara da cewa irin wannan matsalar tsaro sabon abu ne a Kano, amma gwamnati na aiki tare da hukumomin tsaro domin magance ta.
A yayin ziyarar, ya jajanta wa iyalan mutanen da aka sace tare da tabbatar musu cewa gwamnati na ƙoƙarin ganin an dawo da su cikin gaggawa.
Rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutum 10 aka sace a Tsanyawa da Shanono, ciki har da wata tsohuwa da ’yan bindiga suka hallaka.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Gwamna Abba hari Tsanyawa Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun gano zinaren N23m bayan shekara 12 da ɓacewarsu a Borno
’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinwu ta kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 12 da suka gabata a Jihar Borno.
Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren waɗanda suka haɗa da sarƙoƙi da sulallan zinariya a yankin Ƙaramar Hukumar Abadam.
Jami’an Ƙaramar Hukumar ne suka sanar a ranar Asabar a Malam Fatori cewa tsabar zinaren da aka gano, darajarsu ta kai Naira miliyan 23, mallakin wata uwa ce mai ’ya’ya shida.
Matar, wacce ke zaune a gaɓar Tafkin Chadi, ta ce, “A yau ina cike da farin ciki game da gano tsabar zinare na masu daraja da suka ɓace tun 2012, lokacin da ’yan Boko Haram suka ƙona gidaje da shaguna da yawa a cikin al’ummarmu.”
Ta jaddada cewa, “babu daga cikin zinare da aka samu ya ɓace ko ya lalace a lokacin mamayar Malam Fatori da ’yan ta’adda suka yi fiye da nawa.”
Wani babban jami’in Majalisar Ƙaramar Hukumar Abadam da ya sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya yaba wa ’yan sandan da aka tura don kare rayukan mutane da kadarorinsu a yankin Tafkin Chadi.
Bayan gano tsabar zinare na naira miliyan 23, jami’in ya lura cewa martanin ’yan sanda a ayyukan yaƙi da ta’addanci da ake ci gaba da yi wani abin karfafa gwiwa ne ga sojoji da sauran hukumomin tsaro a yankin Tafkin Chadi, wanda ya ƙunshi qananan hukumomi takwas da ke yankin.