Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 165
Published: 1st, December 2025 GMT
165-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku, kissoshi wadanda suka zo cikin Alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Mrtada Muttahari, ko kuma cikin littafan Mathnawa na maulana Jalaluddeen Rumi.
////… Ma dalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Haddan dan Aliyu (a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun yi maganar cewa Imam Al-Hassan ya rasa samun amintattun sojojin da zasu goya masu baya don yakar Mu’awiya dan Abusufyan. Saboda yadda suka ga cewa Mu,awiya yaudari kwamandojin sojojinsa da cin hanci da rashawa.
Amma su Ahlulbaiti musamman Amirulmuminina shugabansu, ma’abuta addini ne wadanda basa sabawa Allah ko da na kebtawar ido ne. Amma mutanen Iraki sun rena abinda suke samu a karkashin ikonsu na kudade da dukiyoyi. Da sun yi hakuri suka bisu, da sunci ta sama da kasansu ba tare da ganimar yaki ba.
Saboda Allah yana arzuta muminai ta sama da kasa hanyoyi daban-daban, musamman ta hanyoyin raya kasa. Da sun yi hakuri suka yi biyayya a gareshi da sai sun isa wani lokacinda basa bukatar yaki don samun ganimar dukiya. Zaman lafiya da za’a samar zai bude masu hanyoyin samun kudade da dukiyoti masu yawa.
Amma sun ki biyayya a gareshi, a duk lokacinda ya kirasu zuwa jihadi don tabbatar da zaman lafiya a cikin al-ummar musulmi basa bada hadin kai.
Imam Ali (a) yana sifinta mutanen Kufa a cikin khudubobinsa, inda yake bayyana rashin bada hadin kansu a duk lolacinda ya kirasu zuwa ga jihadi da kuma yakar mutanen sham kamar inda yake cewa.
{Na kirasu a asirce da bayyana, na kirasu na sake kiransu, daga cikinsu akwai wadanda suke amsa kira amma ba da son ransu ba, daga cikinsu akwai wadanda suke kariyar rashin lafiya, daga cikinsi akwai wadanda suka zauna bas u fitoba ba tare da dalili ba. Ina rokon Allah mai girma da daukaka yayi mani mafita daga garesu da gaggawa. Na rantse da Allah, ba don ina kodayin samun shahada a lokacin haduwa da abokan gaba ba, da kuma tanajin kaina don mutuwa da na so ace ban hadu da wadan nan ba ko da na kwana guda, kuma b azan sake haduwa da su ba har abada}.
A wani wuri Imam Ali (a) yana fada dangane da mutanen Kufa yana cewa {Wallah, wanda aka yaudara, shi wanda ya rudu da ku, wanda ya sami nasara da ku, wallahi shi ne ya sami nasara da mafi tabewar rabo. Wanda ya yi jifa da ku kamar wanda yayi jifa da kibiyan da bai da wurin harbawa, Kuma na kasance bana gasgata zancenku, bana kodayin samun taimakonku, ba zan gargadi makiyi da ku ba, me ya sameku ne? menene maganinku ne? menen waraka a gareku ne?}.
Khudubobin Amirul muminina (a) dangane da sojojinsa suna da yawa a cikin littafin Nahjulbalagha. Inda yak e bayyana yadda suka tabar da shi, suka bakanta ransa, kuma sun ci gaba da hakan har zuwa shahadarsa.
A lokacinda al-amura suka koma hannun Imam Al-Hassan (a) sai al-amarinsu ya kara bayyana, da mafi muninsa. Saboda a lokacinda ya bayyana masu abinda Mu’awiya ya kirashi zuwa gareshi na sulhu, sai dukaninsi ko mafi yawansu sun daga murya suna cewa (muna sun rayuka muna son rayuwa). Wannan ya nuna yadda suke kin mutuwa, suke kuma tsoron jihadi. Basa son duk wani abu wanda zai kai ga yaki da Mu’awiya dan Abusufyan.
Sannan sojojin Imam Al-Hassan (a) sun rasa wadanda suka fahinci addinin musulunci kekyawar fahinta, wadanda suka san matsayin iyalan gidan manzon Allah (s) a cikin musulmi. Mafi yawansu daga baya ne suka musulunt suka shiga addinin musulunci.
Malaman tarihi sun bayyana cewa sahabban manzon Allah (S) wadanda suka musulunta tun farkon bayyanar addinin musulunci kuma suka halarci yakin badar basu fi 63 ne a cikin rundunar Imam Hassan Almujaba (a) ba.
Amma a lokacin yakin Jamal da siffin Imam Ali (a) yana tare ragowarsu daga cikin da manya manyan sahabban manzon Allah (s) wadanda suka san matsayinsa suka san matsayin iyalan gidan manzon Allah (s) basa saba masa kan duk abinda ya umurcesu. Sahabbai kamar, Ammar dan Yasir, Hashimul Murkal,thabit dan qais, da zuzshahadataini, da makamantarsu, duk sun yi shahada a yake-yaken Jamal da siffin kuma sune suke jagorantar rundunar Imam Ali (a), har zu lokacin shahadarsu.
Da a ce wadan nan sahbban da masu kama da su, suna cikin rundunar Imam Al-Haasan (a) da baya bukatar dogaro da wadanda basu san matsayinsa basu san matsayin iyalan gidan manzon Allah(s) a cikinsu ba.
Abu na gaba wanda ya jawo Rauni ciki rundunar Imam Al-Hassan sun hada da kiraye-kirayen Mu\awiya dan Abu Sufyan da Sulhu da kuma zaman lafiya. Wannan bayan da kwamandoji da shuwagabanni kabilu da dama daga rundunar Imam Hassan (a) suka koma bangaren Mu’awiya saboda rashawa da ya basu ko kuma alkawulan da yayi masu.
Wadan nan kiraye-kiraye basu da bambanci da daga Mushafi da sojojin mu’awiya suka yi a siffin. Inda Imam Ali (a) ya bayyana masu cewa makirce kada su kula da su, amma suka saba masa suka ki biyayya a gareshi banda haka suka yi masa barazanan zasu kasheshi kamar yadda suka kashe Uthman.
Haka al-amarin yake a rundunar Imam Al-Hassan, sun amince da kiraye-kirayen da Mu’awiya yake yin a sulhuntawa, basu fahinci sharrin da ke ciki ba, amma kamar yadda zamu gani, daga karshe da aka yi sulhun suka kuma dandani masifa daga sarakunan banu Umayya sai da suka gommace Khalifa Uthman a kansa. Saboda musibar da Mu’awiya dan abu sufyan ya shuka a cikin daular Musulunci, da kuma azbatar da su da yayi, da shi da danginsa na tsawon kimani shekaru 80, musibar ta kai ga ba wanda zai iya sauke su daga kan wuyoyin musulmi sai da musulmi ajamawa daga yankin Khurasan na kasar Iran karkashin jagorancin Abu Muslimul Khurasani ne ya sami nasarar kifar da daularsu a kan musulmi.
Don haka sojojin Imam Hassan (a) sun rasa mutanen kirki wadanda suka san matsayinsa, suka fahinci addinin kamar wadanda suka sansu cikin sahabban manzon Allah (s). Don haka jahilcinsu ne yasa suke maraba da neman sulhun Mu’awiya.
Don haka daga karshe rundunar Imam Al-Hassan (a) ta zami sulhu da Mu’awiya kuma Imam Al-Hassan (a) ba zai iya tursasu yaki da shi ba. Don haka bai da zabi in banda sulhu da Mu,awiya, da kuma kare wadanda suka rage daga cikin iyalan gidan manzon Allah da kuma mabiyansu da gaske da suka rage.
Kha’incin Ubaidullahi dan Abbas, yana daga cikin manya-manyan al-amura da suka jawo kashe guiwar sojojin Imam Al-Hassan (a), da raunanat, saboda ganin yadda ya kasance babban kwamandan sojojin gaba daya, ko kuma runduna mafi girma daga cikin rundunonin Imam Al-Hassan (a) banda haka yana daga cikin Imam Alhassan wato Banu Hashim. Kowa na ganin idan da kowa zai bar Imam Al-Hassan (a) irinsa bai kamata su kha’inci Imam Al-Hassan ba saboda shi dan amminsa ne. Kuma a wayewarsa da saninsa matsayin iyalan gidan manzon Allah (s), ha rya taba zama gwamnan kasar Yemen a lokacin khalifancin Amirul muminina (a) . To bai kamata a ce ya guda zuwa wajen Banu Umayya makiya Banu Hashin a tarihi, kafin da kuma bayan bayyanar addinin musulunci. Wannan abinda ya aikata ya zama abin kunya kuma babban tabo ne ga yan gidan Abbas ammin manzon Allah (s).
Kamar yadda wani mawaki yake cewa.
Idan na kusa wanda kai dan kungiyarsa ne ya kubuce maka* To kada kayi mamaki idan wadanda suke nesa da kai su mika ga Makiya.
Abinda Ubaidullahi dan Abbas ya yi ya cusa bakin ciki a cikin zuciyar Imam Al-Hassan, bakin ciki mai yawa. Don bai mutunta duk abubuwan mutuntawa tsakaninsa da Imam Hassan, a ko wani bangare. Bai mutunta dankon addinin wanda ya fito daga gidansu Banu Hashim ba, bai mutunta dankon zumncin da ke tsakaninsa da Imam Al-Hassan na cewa shi dan ammin manzon Allah (s). banda haka shi ne babban kwamandan sojojin Imam Alhassan (a), kuma a matsayin wanda y afara kiran a yi masa bai’a sannan wanda ya fara yi masa bai’a ba. Kuma bai ji tsoron yanda wannan abinda yayi zai zama tabo ga zuriyyarsa har duniya ta nade ba.
Idan zaku tuna Kais dan Sa’adu dan Ubada, bayan da Ubaidullahi ya koma bangaren Mu’awiya shi ya bada sallar Asubaha, sannan yayi khuduba, yana cewa: Wannan da dan’uwansa da babansa basu taba aikin alkhairi ba. Yace Abbas ammin manzon Allah (s) ya yake shi a Abadar sai da aka kamashi a matsayin fursinan yaki. Ya kuma karbi kudi a wajensa don ya fanshi kansa.
Sannan Imam Ali ya nada dan’uwansa a matsayin wali a Basra, ya sace kudade ya sayi bayi, yana ganin sun halatta a gareshi. Sannan shi Ubaidullahi, a matsayinsa na gwamnan Imam Ali (a) a Yemen, a lokacinda Busru ya kai hare-hare kan kasar Yemen ya gudu ha ya bar yayansa a hannun makiya suka kashesu, maimakon ya nuna turjiya ko da kuwa zai mutune. Sannan gashi ya kara da abinda yayi na Kha’inci ga Imam Al-Hassan (a).
Abinda Ubaidullahi yayi ya shafi danginsa da suka yi Mulki bayan banu Umayya, har sai da ya kai suna boye abubuwan kunyan da ya faru a cikin danginsu a farko farkon Musulunci.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan 164 December 1, 2025 Baqaei: Amurka Ce Babbar Barazana Ga Zaman Lafiya Da Tsaro A Duniya December 1, 2025 Paparoma Leo Na 14 Yana Ziyarar Aiki Na Kwanaki 3 A Kasar Lebanon December 1, 2025 Wani Dan Adawa Da Gwamnatin Paul Biya Ya Mutu A Gidan Yari A Kasar Kamaru December 1, 2025 Tawagar ECOWAS Ta Bar Guinea – Bissau bayan da shugaban kasar yayi barazanar korarsu Da Karfi December 1, 2025 Yawan Yahudawan Da Suke Ficewa Daga HKI Sun Nininka Har Sau 100% December 1, 2025 Gaza: Fiye da Falasdinawa 350 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila tun bayan tsagaita wuta December 1, 2025 Hamas : Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta December 1, 2025 Nijar : zamu sayar da uranium dinmu ga wanda muka ga dama_ Janar Tiani December 1, 2025 Tawagar ECOWAS za ta je Guinea-Bissau, bayan juyin mulkin soji December 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: matsayin iyalan gidan manzon Allah suka san matsayin wadanda suka san rundunar Imam Al da Mu awiya
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun kashe tsohuwa, sun sace mutum 3 a Kano
’Yan bindiga sun harbe wata tsohuwa har lahira a wani sabon hari da suka kai ƙauyen Yankamaye da ke Ƙaramar Hukumar Tsanyawa a Jihar Kano.
Sun kai harin ne a daren ranar Asabar, a lokacin da mutanen ƙauyen ke kwance.
Likitoci sun gindaya sabon sharaɗi bayan janye yajin aiki Tinubu ya sake aike wa majalisa ƙarin sunayen jakadu 32Yayin kai harin, ’yan bindigar sun kuma sace aƙalla mutum uku.
Yankamaye, wani ƙaramin ƙauyen manoma ne, ’yan bindiga da ke tserewa daga maƙwabtan jihohin Kano ne suka fara kai musu hare-hare.
Kakakin rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an tura jami’ai domin bin diddigin maharan.
Mazauna ƙauyen sun ce ’yan bindigar sun isa ne a kan babura inda suka ajiye su daga nesa, sannan suka shiga ƙauyen a ƙafa.
A yayin taron majalisar zartarwa da aka gudanar kwanan nan, Gwamna Abba Yusuf, ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na magance matsalar tsaro.
Ya kuma ce hare-haren ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da ɓarayi shanu a wasu yankunan Arewacin jihar, babban abin damuwa ne.
Gwamnan, ya ce suna aiki tare da hukumomin tsaro don magance barazanar da kuma tabbatar da zaman lafiya.
Ya bayyana ƙananan hukumomin da abin ya shafa; Kunchi, Tsanyawa, Gwarzo, Kabo, Sumaila, Shanono, Tudun Wada, Doguwa, da Rogo.
Amma ya ce hukumomi na ci gaba da ayyuka domin toshe hanyoyin shigowar ’yan bindiga da kuma kare al’ummomin ƙauyuka.
“Duk da wasu ƙalubale da ake fuskanta a nan da can, jama’a su kwantar da hankalinsu, gwamnati tana aiki domin magance duk wata barazana ga zaman lafiya,” in ji Yusuf.
Gwamnan, ya kuma goyi bayan matakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na ayyana dokar ta-ɓaci a harkar tsaro a faɗin ƙasar nan.