Sojoji sun kashe babban Kwamandan ISWAP, Amirul Fiya a Borno
Published: 13th, August 2025 GMT
Dakarun Sojin Bataliya ta 3 da ke sansanin FOB Rann, a Ƙaramar Hukumar Kala-Balge a Jihar Borno, sun daƙile wani hari da ISWAP suka kai.
Bayan tafka artabu, sojojin sun gano gawar ’yan ta’adda uku, ciki har da babban kwamandansu, Amirul Fiya.
Gwamnatin Gombe za ta ƙirƙiri sabbin ƙananan hukumomi 13 Majalisar Kano ta dakatar da ciyaman kan zargin karkatar da takiSojojin sun bayyana cewa wannan nasara ta zama naƙaso ga shugabancin ISWAP a yankin.
Rundunar, ta ƙara jadadda ƙudirinta na kawo ƙarshen ta’addanci a Arewa maso Gabas.
Sojoji da sauran haɗin gwiwar jami’an tsaro na ci gaba da fatattakar ’yan ta’adda a yankin Arewa Maso Gabas.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Amirul Fiya Artabu hari kwamanda
এছাড়াও পড়ুন:
Za a samu ambaliya da ruwa mai karfi a jihohi 15 a Arewa —NEMA
Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen ruwan sama mai karfi da zai iya haifar da ambaliya a jihohi 15 na Arewacin Najeriya da wasu wurare 68, a cikin kwanaki biyar masu zuwa.
Wannan gargadi ya fito ne daga Cibiyar Lura da Gargadin Ambaliya ta Kasa, karkashin Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, inda aka bukaci hukumomi da al’umma su dauki matakan gaggawa don kare rayuka da dukiyoyi.
Cibiyar ta bayyana jerin jihohi da wuraren da ambaliyar za ta iya shafa sun hada da:
Adamawa: Jimeta, Mubi, Mayo-Belwa, Wuro-Bokki, Yola, Farkumo Bauchi: Jama’a Nasarawa: Keffi Kaduna: Jaji, Kafanchan, Zaria, Birnin-Gwari Katsina: Katsina, Bindawa, Kaita Kebbi: Kamba, Kangiwa, Kalgo, Ribah, Sakaba, Saminaka, Gwandu, Jega, Bunza, Birnin Kebbi, Bagudo, Argungu Kano: Bebeji, Gwarzo, Karaye, Sumaila, Tundun-wada Niger: Rijau, Ibi, Chanchaga, Magama, Mashegu, Minna, Mokwa, New-Bussa, Sarkin Pawa, Wushishi Taraba: Duchi Jigawa: Miga, Ringim, Hadejia, Dutse Yobe: Potiskum, Dapchi, Gasma, Gashua, Jakusko Zamfara: Kaura Namoda, Maradun, Shinkafi, Bungudu, Gusau Sokoto: Sokoto, Gagawa, Gada, Goronyo, Isa, Wamakko, Silame, Makira Borno: Bama Kwara: JebbaHukumar Kula da Halin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta bayyana cewa kawo yanzu mutane 140,228 a jihohi 21 ne ambaliya ta riga ta shafa a shekarar 2025.
NAJERIYA A YAU: Yadda Damina Ke Shafar Masu Ƙananan Sana’o’i Ambaliya: Mutum 165 sun mutu a Nijeriya a bana — NEMAHukumar Kula da Halin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta bayyana cewa kawo yanzu mutane 140,228 a jihohi 21 ne ambaliya ta riga ta shafa a shekarar 2025.
Alkaluman da NEMA ta fitar sun nuna ceaw ambaliyar ta riga ta raba mutane 49,205 da muhallansu, ta lalata gidaje 10,663, da kuma gonaki 9,454 a al’ummomi daban-daban.
Jihohin da ibtila’in ya fi shafa sun hada da:
Imo (28,030), Ribas (22,345), Adamwa (12,613), Abia (11,907), Delta 8,810, Borno (8,164), Kaduna (7,334), Bayelsa (5,868) da Legas (5,793).
Sauran jihohin sun hada da Akwa Ibom (5,409), Niger (3,786), Ondo (3,735), Edo (3,234), Kogi (2,825), Sokoto (1,916), Kwara (2,663), Kano (1,446), Jigawa (1,428), Gombe (972), Anambra (925), da Babban Birnin Tarayya (1,025).
Da haka hukumar ta bukaci jama’a da hukumomi da su dauki matakan gaggawa don rage illar ambaliya da kare lafiyar jama’a.