Aminiya:
2025-12-03@11:01:54 GMT

Wani ya yi shigar mahaifiyarsa da ta mutu ya je karvar kuxin fanshonta

Published: 3rd, December 2025 GMT

Wani ya yi shigar mahaifiyarsa da ta mutu ya je karvar kuxin fanshonta

Ana binciken wani tsohon ma’aikacin jinya a qasar Italiya bisa zargin ya yi shigar mahaifiyarsa da ta mutu kuma ya je ma’aikatar fansho a matsayin mahaifiyarsa don neman fanshonta. Haka kuma an gano ya voye gawarta a cikin gidansa har tsawon shekaru uku bayan mutuwarta.

Mutumin xan Italiya ya saka tufafin mahaifiyarsa da ta mutu sannan ya yi kwalliya da gazar da jan-baki kamar yada take yi, ya je bankin da take ajiya yana neman a biya shi kuxi fanshonta, bayan ya voye gawarta a gida.

Mutumin mai shekaru 56, ma’aikacin jinya da ya rasa aikinsa a garin Mantua, ya sami damar karvar dubban kuxi na Yuro kafin asirinsa ya tonu, kamar yadda Jaridar Corriere della Sera ta Italiya ta ruwaito.

An kuma yi zargin cewa, ya naxe gawar mahaifiyarsa, Graziella Dall’Oglio, sannan ya voye ta a cikin firji a gidansu har tsawon shekara uku ba tare da ya sanar da ma’aikatar fansho ba, inda ya riqa zuwa yana cire kuxin fanshon da ake tura mata yana bidirin gabansa.

Mis Dall’Oglio ta rasu kimanin shekara uku da suka gabata, tana da shekara 82. Amma xanta bai bayar da rahoton mutuwarta a hukumance ba, maimakon haka ya naxe gawarta a cikin zane, ya saka ta a cikin wata jakar ajiye kaya sannan ya voye ta a gidan.

Rahotanni sun ce, ya yi shigar mahaifiyarsa, sanye da jan-baki da hoda da gazar da kuma sarqa, sannan ya tafi sabunta katin shaidarta da ya qare a ofishin gwamnati da ke wajen Borgo Virgilio.

Bayanai sun nuna cewa, ya yi wa kansa aski sannan ya sanya gashin mata a kansa kamar irin na mahaifiyarsa da ta rasu, kuma ya sanya kayan ado kamar yadda ta saba.

Jaridar ta bayyana cewa, wannan wani sabon salon damfara ce kamar irin na fim xin ‘Mrs Doubtfire’, wanda aka yi a shekarar 1993 da Robin WilliaMis da ya fito a ciki. Mutumin ya bayyana a ofishin gwamnati da ke wajen Mantua a farkon wannan watan, inda aka yi zargin ya bayyana kansa a matsayin Mis Dall’Oglio.

Wani ma’aikacin ma’aikatar fansho ne ya harvo jirginsa, inda ya lura da cewa, akwai alamar tambaya game da ‘matar’ da take neman a canza mata katin. Musamman da yake ya san wacce take da ainihin katin ba ta da kaurin wuya, sannan kuma muryarta ba ta maza ba ce. Wannan ce ta sanya ma’aikacin bai wata-wata ba cikin sauri ya kai rahoto ga ‘yan sanda nan da nan kuma ya sanar da magajin garin Mantua.

’Yan sanda sun ce, da isarsu sai suka kwatanta hotunan Mis Dall’Oglio na gaske da na xanta da ya yi shigar burtu kuma sun fahimci cewa, akwai lauje a cikin naxi.

Bincike ya nuna xan ya karvi kuxin fanshonta na shekaru uku da suka kai kusan Fam 47,000 kuma da mallakar gidaje uku, a cewar rahotanni.

Bayan an kama shi, ‘yan sanda sun je gidansa, inda suka gano gawar Mis Dall’Oglio da aka voye a xakin wanki.

“Ya shigo ofishin ma’aikatar fansho yana sanye da dogon siket, ya yi ado da jan baki da jan-farce da sarqa da ‘yan kunne irin na tsofaffi,” Francesco Aporti, magajin garin Borgo Virgilio ya shaida wa Jaridar Corriere della Sera.

“Amma sai dai yana da kaurin wuya, sannan kuma fatar hannunsa ba ta yi kama da na tsohuwa ‘yar shekara 85 ba.

“Muryarsa kuma ta maza ce duk da yake ya yi shigar mata. Amma da a ce ba a lura da waxannan abubuwa ba da ya ci lalai.”

Da yake magana game da mahaifiyar wanda ake zargin, magajin garin ya ce, “Wataqila ta mutu ne saboda dalilai na rashin lafiya, amma za a tabbatar da hakan ne kawai ta hanyar binciken gawar.” Wannan labari ne mai ban mamaki kuma abin baqin ciki ne qwarai.”

‘Yan sandan Italiya sun ce, gawar mahaifiyar an naxe ta da zanin gado sannan aka saka ta a wata jakar kaya, aka sanya ta cikin firji.

Daga baya ’yan sanda sun xauki gawar zuwa wajen ajiye gawarwaki a asibitin da ke yankin don yin gwajin qwaqwaf da nufin gano musabbabin rasuwarta. Yanzu haka ana binciken mutumin a kan laifukan zamba da voye gawar da ya yi ba bisa qa’ida ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: ya yi shigar mahaifiyarsa mahaifiyarsa da ta mutu ma aikatar fansho

এছাড়াও পড়ুন:

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 165

165-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku, kissoshi wadanda suka zo cikin Alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Mrtada Muttahari, ko kuma cikin littafan Mathnawa na maulana Jalaluddeen Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////… Ma dalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Haddan dan Aliyu (a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun yi maganar cewa Imam Al-Hassan ya rasa samun amintattun sojojin da zasu goya masu baya don yakar Mu’awiya dan Abusufyan. Saboda yadda suka ga cewa Mu,awiya yaudari kwamandojin sojojinsa da cin hanci da rashawa.

Amma su Ahlulbaiti musamman Amirulmuminina shugabansu, ma’abuta addini ne wadanda basa sabawa Allah ko da na kebtawar ido ne. Amma mutanen Iraki sun rena abinda suke samu a karkashin ikonsu na kudade da dukiyoyi. Da sun yi hakuri suka bisu, da sunci ta sama da kasansu ba tare da ganimar yaki ba.

Saboda Allah yana arzuta muminai ta sama da kasa hanyoyi daban-daban, musamman ta hanyoyin raya kasa. Da sun yi hakuri suka yi biyayya a gareshi da sai sun isa wani lokacinda basa bukatar yaki don samun ganimar dukiya. Zaman lafiya da za’a samar zai bude masu hanyoyin samun kudade da dukiyoti masu yawa.

Amma sun ki biyayya a gareshi, a duk lokacinda ya kirasu zuwa jihadi don tabbatar da zaman lafiya a cikin al-ummar musulmi basa bada hadin kai.

Imam Ali (a) yana sifinta mutanen Kufa a cikin khudubobinsa, inda yake bayyana rashin bada hadin kansu a duk lolacinda ya kirasu zuwa ga jihadi da kuma yakar mutanen sham kamar inda yake cewa.

{Na kirasu a asirce da bayyana, na kirasu na sake kiransu, daga cikinsu akwai wadanda suke amsa kira amma ba da son ransu ba, daga cikinsu akwai wadanda suke kariyar rashin lafiya, daga cikinsi akwai wadanda suka zauna bas u fitoba ba tare da dalili ba. Ina rokon Allah mai girma da daukaka yayi mani mafita daga garesu da gaggawa. Na rantse da Allah, ba don ina kodayin samun shahada a lokacin haduwa da abokan gaba ba, da kuma tanajin kaina don mutuwa da na so ace ban hadu da wadan nan ba ko da na kwana guda, kuma b azan sake haduwa da su ba har abada}.

A wani wuri Imam Ali (a) yana fada dangane da mutanen Kufa yana cewa {Wallah, wanda aka yaudara, shi wanda ya rudu da ku, wanda ya sami nasara da ku, wallahi shi ne ya sami nasara da mafi tabewar rabo. Wanda ya yi jifa da ku kamar wanda yayi jifa da kibiyan da bai da wurin harbawa, Kuma na kasance bana gasgata zancenku, bana kodayin samun taimakonku, ba zan gargadi makiyi da ku ba, me ya sameku ne? menene maganinku ne? menen waraka a gareku ne?}.

Khudubobin Amirul muminina (a) dangane da sojojinsa suna da yawa a cikin littafin Nahjulbalagha. Inda yak e bayyana yadda suka tabar da shi, suka bakanta ransa, kuma sun ci gaba da hakan har zuwa shahadarsa.

A lokacinda al-amura suka koma hannun Imam Al-Hassan (a) sai al-amarinsu ya kara bayyana, da mafi muninsa. Saboda a lokacinda ya bayyana masu abinda Mu’awiya ya kirashi zuwa gareshi na sulhu, sai dukaninsi ko mafi yawansu sun daga murya suna cewa (muna sun rayuka muna son rayuwa). Wannan ya nuna yadda suke kin mutuwa, suke kuma tsoron jihadi. Basa son duk wani abu wanda zai kai ga yaki da Mu’awiya dan Abusufyan.

Sannan sojojin Imam Al-Hassan (a) sun rasa wadanda suka fahinci addinin musulunci kekyawar fahinta, wadanda suka san matsayin iyalan gidan manzon Allah (s) a cikin musulmi. Mafi yawansu daga baya ne suka musulunt suka shiga addinin musulunci.

Malaman tarihi sun bayyana cewa sahabban manzon Allah (S) wadanda suka musulunta tun farkon bayyanar addinin musulunci kuma suka halarci yakin badar basu fi 63 ne a cikin rundunar Imam Hassan Almujaba (a) ba.

Amma a lokacin yakin Jamal da siffin Imam Ali (a) yana tare ragowarsu daga cikin  da manya manyan sahabban manzon Allah (s) wadanda suka san matsayinsa suka san matsayin iyalan gidan manzon Allah (s) basa saba masa kan duk abinda ya umurcesu. Sahabbai kamar, Ammar dan Yasir, Hashimul Murkal,thabit dan qais, da zuzshahadataini, da makamantarsu, duk sun yi shahada a yake-yaken Jamal  da siffin kuma sune suke jagorantar rundunar Imam Ali (a), har zu lokacin shahadarsu.

Da a ce wadan nan sahbban da masu kama da su, suna cikin rundunar Imam Al-Haasan (a) da baya bukatar dogaro da wadanda basu san matsayinsa basu san matsayin iyalan gidan manzon Allah(s) a cikinsu ba.

Abu na gaba wanda ya jawo Rauni ciki  rundunar Imam Al-Hassan sun hada da kiraye-kirayen Mu\awiya dan Abu Sufyan da Sulhu da kuma zaman lafiya. Wannan bayan da kwamandoji da shuwagabanni kabilu da dama daga rundunar Imam Hassan (a) suka koma bangaren Mu’awiya saboda rashawa da ya basu ko kuma alkawulan da yayi masu.

Wadan nan kiraye-kiraye basu da bambanci da daga Mushafi da sojojin mu’awiya suka yi a siffin. Inda Imam Ali (a) ya bayyana masu cewa makirce kada su kula da su, amma suka saba masa suka ki biyayya a gareshi banda haka suka yi masa barazanan zasu kasheshi kamar yadda suka kashe Uthman.

Haka al-amarin yake a rundunar Imam Al-Hassan, sun amince da kiraye-kirayen da Mu’awiya yake yin a sulhuntawa, basu  fahinci sharrin da ke ciki ba, amma kamar yadda zamu gani, daga karshe da aka yi sulhun suka kuma dandani masifa daga sarakunan banu Umayya sai da suka gommace Khalifa Uthman a kansa. Saboda musibar da Mu’awiya dan abu sufyan ya shuka a cikin daular Musulunci, da kuma azbatar da su da yayi, da shi da danginsa na tsawon kimani shekaru 80, musibar ta kai ga ba wanda zai iya sauke su daga kan wuyoyin musulmi sai da musulmi ajamawa daga yankin Khurasan na kasar Iran karkashin jagorancin Abu Muslimul Khurasani ne ya sami nasarar kifar da daularsu a kan musulmi.

Don haka sojojin Imam Hassan (a) sun rasa mutanen kirki wadanda suka san matsayinsa, suka fahinci addinin kamar wadanda suka sansu cikin sahabban manzon Allah (s). Don haka jahilcinsu ne yasa suke maraba da neman sulhun Mu’awiya.

Don haka daga karshe rundunar Imam Al-Hassan (a) ta zami sulhu da Mu’awiya kuma Imam Al-Hassan (a) ba zai iya tursasu yaki da shi ba. Don haka bai da zabi in banda sulhu da Mu,awiya, da kuma kare wadanda suka rage daga cikin iyalan gidan manzon Allah da kuma mabiyansu da gaske da suka rage.

Kha’incin Ubaidullahi dan Abbas, yana daga cikin manya-manyan al-amura da suka jawo kashe guiwar sojojin Imam Al-Hassan (a), da raunanat, saboda ganin yadda ya kasance babban kwamandan sojojin gaba daya, ko kuma runduna mafi girma daga cikin rundunonin Imam Al-Hassan (a) banda haka yana daga cikin Imam Alhassan  wato Banu Hashim. Kowa na ganin idan da kowa zai bar Imam Al-Hassan (a) irinsa bai kamata su kha’inci Imam Al-Hassan ba saboda shi dan amminsa ne. Kuma a wayewarsa da saninsa matsayin iyalan gidan manzon Allah (s), ha rya taba zama gwamnan kasar Yemen a lokacin khalifancin Amirul muminina (a) . To bai kamata a ce ya guda zuwa wajen Banu Umayya makiya Banu Hashin a tarihi, kafin da kuma bayan bayyanar addinin musulunci. Wannan abinda ya aikata ya zama abin kunya kuma babban tabo ne ga yan gidan Abbas ammin manzon Allah (s).

Kamar yadda wani mawaki yake cewa.

Idan na kusa wanda kai dan kungiyarsa ne ya kubuce maka* To kada kayi mamaki idan wadanda suke nesa da kai su mika ga Makiya.

Abinda Ubaidullahi dan Abbas ya yi ya cusa bakin ciki a cikin zuciyar Imam Al-Hassan, bakin ciki mai yawa. Don bai mutunta duk abubuwan mutuntawa tsakaninsa da Imam Hassan, a ko wani bangare. Bai mutunta dankon addinin wanda ya fito daga gidansu Banu Hashim ba, bai mutunta dankon zumncin da ke tsakaninsa da Imam Al-Hassan na cewa shi dan ammin manzon Allah (s). banda haka shi ne babban kwamandan sojojin Imam Alhassan (a), kuma a matsayin wanda y afara kiran a yi masa bai’a sannan wanda ya fara yi masa bai’a ba. Kuma bai ji tsoron yanda wannan abinda yayi zai zama tabo ga zuriyyarsa har duniya ta nade ba.

Idan zaku tuna Kais dan Sa’adu dan Ubada, bayan da Ubaidullahi ya koma bangaren Mu’awiya shi ya bada sallar Asubaha, sannan yayi khuduba, yana cewa: Wannan da dan’uwansa da babansa basu taba aikin alkhairi ba. Yace Abbas ammin manzon Allah (s) ya yake shi a Abadar sai da aka kamashi a matsayin fursinan yaki. Ya kuma karbi kudi a wajensa don ya fanshi kansa.

Sannan Imam Ali ya nada dan’uwansa a matsayin wali a Basra, ya sace kudade ya sayi bayi, yana ganin sun halatta a gareshi. Sannan shi Ubaidullahi, a matsayinsa na gwamnan Imam Ali (a) a Yemen, a lokacinda Busru ya kai hare-hare kan kasar Yemen ya gudu ha ya bar yayansa a hannun makiya suka kashesu, maimakon ya nuna turjiya ko da kuwa zai mutune. Sannan gashi ya kara da abinda yayi na Kha’inci ga Imam Al-Hassan (a).

Abinda Ubaidullahi yayi ya shafi danginsa da suka yi Mulki bayan banu Umayya, har sai da ya kai suna boye abubuwan kunyan da ya faru a cikin danginsu a farko farkon Musulunci.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan 164 December 1, 2025 Baqaei: Amurka Ce Babbar Barazana Ga Zaman Lafiya Da Tsaro A Duniya December 1, 2025 Paparoma Leo Na 14 Yana Ziyarar Aiki Na Kwanaki 3  A Kasar Lebanon December 1, 2025 Wani Dan Adawa Da Gwamnatin Paul Biya Ya Mutu A Gidan Yari A Kasar Kamaru December 1, 2025 Tawagar ECOWAS Ta Bar Guinea – Bissau bayan da shugaban kasar yayi barazanar korarsu Da Karfi December 1, 2025 Yawan Yahudawan Da Suke Ficewa Daga HKI Sun Nininka Har Sau 100% December 1, 2025 Gaza: Fiye da Falasdinawa 350 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila tun bayan tsagaita wuta December 1, 2025 Hamas : Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta December 1, 2025 Nijar : zamu sayar da uranium dinmu ga wanda muka ga dama_ Janar Tiani December 1, 2025 Tawagar ECOWAS za ta je Guinea-Bissau, bayan juyin mulkin soji December 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Har yanzu ban bar yin waqa ba-Yusuf Lazio
  • Majalisar Dokokin Akwa Ibom ta yi fatali da ƙudurin neman hana cin naman kare
  • Sharhi:’HKI tana fama da karancin sojojin a dukkan rassan sojojin kasar’.
  • Mutane 9,854 na ɗauke da cutar AIDS a Yobe 
  • An yi garkuwa da manoma 11 a Kudancin Kaduna
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 165
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan 164
  • Wani Dan Adawa Da Gwamnatin Paul Biya Ya Mutu A Gidan Yari A Kasar Kamaru
  • ’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa  masu ibada a Kogi