An Bude Taron Bikin Cika Shakaru 41 Da Kafa Kungiyar Tattalin Arziki Ta ECO A nan Tehran
Published: 2nd, December 2025 GMT
An gudanar da bikin cika shekaru 41 da kafa kungiyar hadin guiwa ta tatalin arziki ta ECO a nan birnin Tehran ne a jiya litinin inda sakatare janar din kungiyar Eco Majeed khan da ministan aladu reza salihi –amiri suka gabatar da jawabai a wajen, da ya shafi irin ci gaba da kungiyar ta samu a cikin wadannan shekaru da kuma bayyana muhimmancin yin aiki tare .
Kungiyar Eco tana daga cikin mihimmiyar hanya ta duniya da ta fara daga yankin tekun fasha zuwa tsakiyar asiya , kuma kasashen dake mambobin kungiyar sun kai kusan rabin biliyan dake da arzikin makamashi da ma’adinai kasa, baya ga batun tattalin arziki , kungiyar tana matsayin jigo mai muhimmanci wajen huldodin diplomasiya a yankin. Musamman ma ga kasar iran,da take bada dama ga mambobinta yin huldar kasuwanci, zirga-zirga da kuma abubuwan da suka shafi al’adu.
Kungiyar da iran ta kirkiro tare da turkiya da Pakistan kafin daga baya aka fadadata zuwa mambobi guda 10 wato Iran, turkiya, Pakistan ,Azarbaijan ,Afghanistan , turkuminstan, Uzbakestan da kyargistan da kuma kasar Tajikistan, kasashen suna fatan kara ingantan kasuwanci dake tsakaninsu, da kuma kafa hanyoyin sadarwa , da hadin guiwa a bangaren makamashi da wutar lantarki da shinfida bututu da kuma karfafa bangaren aladu da yawon bude ido.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araghchi: Halayyar Amurka ce yin matsin lamba maimakon diflomasiyya a dangantaka ta kasa da kasa December 2, 2025 Aljeriya: Taron Kasashen Afirka Don Amincewa Da Mulkin Mallaka A Matsayin Laifi December 2, 2025 Lebanon: An Gudanar Da Taron Musulunci da Kiristanci a Beirut tare da halartar Paparoma December 2, 2025 Chuck Schumer: Trump Ba Shi da Ikon Kaddamar da Yaki Kan Venezuela December 2, 2025 Najeriya: Matatar Dangote Za Ta Mika Tataccen Mai Lita Biliyan 1.5 A Watan Disamba December 2, 2025 Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Trump na ware Afirka ta Kudu daga G20 December 2, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 165 December 1, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan 164 December 1, 2025 Baqaei: Amurka Ce Babbar Barazana Ga Zaman Lafiya Da Tsaro A Duniya December 1, 2025 Paparoma Leo Na 14 Yana Ziyarar Aiki Na Kwanaki 3 A Kasar Lebanon December 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
N750,000 kuɗin bikin yaye ɗaliban Jami’ar MAAUN ya tayar da ƙura a Kano
Ana ci gaba da ta ƙaddama kan Naira dubu ɗari bakwai da hamsin da Jami’ar Amurka ta Maryam Abacha (MAAUN) da ke Jihar Kano ta wajabta wa ɗalibanta da suka kammala karatu biya a matsayin kuɗin bikin yaye ɗalibai.
Jami’ar MAAUN ta sanya wa kowane ɗalibin da ya kammala karatu biyan Naira dubu ɗari bakwai da hamsin a matsayin kuɗin bikin yaye ɗalibai, kafin ta ba shi takardar shaidar kammala karatu da gabatar da bayanansa domin samun damar halartar aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC).
Sai dai kuma, Hukumar Karɓar Ƙorafi ta Jihar Kano (PCACC) ta umarci iyayen ɗaliban cewa su dakata da biyan kuɗin har sai ta kammala bincike kan ƙorafin da suka gabatar mata a kan lamarin.
Sanarwar da Shugaban Sashen Ayyuka na PCACC, Salisu Saleh, ya fitar bayan samun ƙorafi daga iyayen ɗaliban, ta umarci hukumar gudanarwar Jami’ar MAAUN da ta jingine shirinta na riƙe takardar kammala karatun ɗaliban ko tura sunayensu domin shirye-shiryen NYSC, saboda rashin biyan kuɗin.
’Yan bindiga sun sace amarya da ƙawenta 14 a Sakkwato Sojoji sun ceto mutum 7 da ’yan bindiga suka sace a Kano Sojoji sun ceto ’yan mata 12 da ISWAP suka sace a BornoA gefe guda kuma, hukumar gudanarwar Jami’ar MAAUN ta dage a kan cewa, za ta gudanar da bikin yadda ta riga ta tsara, wanda bai gamsu ba ya tafi kotu.
Mai mallakar Jami’ar MAAUN, Farfesa Abubakar Adamu Gwarzo, ya shaida wa wakilinmu cewa jami’ar za ta gudanar da taron bikin yaye ɗaliban nata kamar yadda ta tsara a cikin wannan wata na Disamba, 2025.
Ya jaddada cewa jami’ar zaman kanta take, don haka tana da ikon sanya kuɗin bikin yaye ɗalibanta.
A cewarsa, kuɗin da MAAUN ta sanya bai kai abin da wata jami’a mai zaman kanta a Jihar ba ta sanya, amma bai ambaci suna ba. Don haka ya kalubalanci Hukumar kan rashin dakatar da biyan kuɗaɗen a ɗaya jami’ar ba.
Ya ce, “Za mu gudanar da bikin a watan Disamba a kamar yadda muka tsara, kuma za mu gayyaci ’yan jarida su ɗauki rahoto.”
Wata wasiƙar ƙorafi a madadin ɗalibai ta nuna damuwa kan yunƙurin tattaunawa da ɗalibai a ɗaiɗaikunsu domin neman ragin kuɗin da jami’ar ta sanya.
Ta bayyana cewa wannan ya saɓa wa abin da aka tsara cewa tattaunawar za ta ƙunshi iyayen ɗalibai da hukumomin jami’ar da kuma wakilan gwamnati.
A yayin da iyaye ke jiran samun tabbacin tsarin da aka yi a hukumance, hukumar gudanarwar Jami’ar MAAUN ta nace cewa babu gudu, babu ja da baya wajen gudanar da taron kamar yadda ta riga ta tsara — duk wanda bai gamsu ba ya tafi kotu.