Aminiya:
2025-12-01@15:39:38 GMT

Sarkin Musulmi ya buƙaci gwamnonin Arewa suke saurarar ƙorafin jama’a

Published: 1st, December 2025 GMT

Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya shawarci gwamnonin jihohin Arewa 19 su riƙa sauraron masu sukarsu tare da amfani da shawarwarin da ake ba su domin inganta salon mulkinsu.

Ya bayar da wannan shawara ne a ranar Litinin, yayin taron haɗin gwiwar Gwamnonin Arewa da Sarakunan Gargajiya a Kaduna.

’Yan sanda sun gano zinaren N23m bayan shekara 13 da ɓacewarsu a Borno ’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa  masu ibada a Kogi 

Sarkin Musulmi, ya ce bai kamata shugabanni su yi biris da ƙorafin jama’a ba, musamman a wannan lokaci da Arewa ke fama da matsalolin rashin tsaro, talauci da matsin tattalin arziƙi.

A cewarsa, babu wani gwamna ko shugaban ƙasa da zai nemi ƙuri’un jama’a sannan bayan ya hau mulki ya juya musu baya.

Ya nuna damuwa cewa mutane da dama na zargin gwamnonin da rashin yin aiki, alhali suna fuskantar matsin lamba.

Sarkin ya shawarce su da su rika karɓar ƙorafe-ƙorafe masu amfani tare da gyara inda ya dace, domin hakan na taimakawa wajen yanke shawara mai kyau.

Haka kuma, ya yi kira da a ƙara samun haɗin kai a tsakanin gwamnonin, inda ya ce hakan ne zai taimaka wajen inganta Arewa da daidaita ƙasa baki ɗaya.

Sarkin Musulmi ya tabbatar wa gwamnonin cewa sarakunan gargajiya na tare da su, kuma a shirye suke ba su goyon baya a kowane lokaci.

Ya kuma bayar da shawarar cewa ya kamata gwamnoni da sarakunan gargajiya su riƙa gudanar da taruka akai-akai domin tattauna matsaloli da yanke shawara tare.

A ƙarshe, ya ce sarakunan gargajiya za su ci gaba da bayar da gudummawa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Arewa da Najeriya gaba baki ɗaya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Arewa Gwamnoni Sarkin Musulmi Tsaro Sarkin Musulmi

এছাড়াও পড়ুন:

Pezeshkian: Makiya na neman kawo cikas ga ci gaban kasashen Musulmi

Pars Today – Shugaban Iran, a wata ganawa da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, ya ce a lokacin da maƙiyan ƙasashen Musulmi ke neman ƙara matsin lamba, ana sa ran ƙasashen Musulunci za su sauƙaƙa wa junansu yanayi da kuma guje wa matsaloli masu sarkakiya.

Masoud Pezeshkian, Shugaban Iran, a ranar Lahadi da yamma a ganawarsa da Hakan Fidan, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, ya yi magana game da tarihin dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, al’adu, da kuma ‘yan’uwa. Ya bayyana waɗannan alaƙar a matsayin mai zurfi, na gaskiya, kuma cike da fa’idodi masu yawa na ci gaba. Ya ƙara da cewa idan ƙasashen Musulunci suka yi aiki da niyya ɗaya bisa haɗin kai, haɗin kai, da musayar gogewa, babu wani iko da zai iya haifar da matsala ga ƙasashen Musulmi.

A cewar Pars Today, Pezeshkian ya jaddada buƙatar ƙarfafa dangantaka da haɗuwar dabaru tsakanin ƙasashen Musulunci. Ya dauki wani bangare na rikicin da ke faruwa a yankin a matsayin sakamakon makirci da kuma rura wutar rarrabuwar kawuna daga wasu masu shiga tsakani, yana mai cewa: “Manufar wadannan kungiyoyi ita ce sanya manufofinsu da manufofinsu marasa kyau a yankin da kuma haifar da cikas ga ci gaba da ci gaban kasashen Musulunci.”

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban venuzuwela Ya Gargadi Amurka Game Da Kokarin Da Take yi Na Karbe Ikon Kula Da Rijiyoyin Mai Na Kasar December 1, 2025 Zanga zanga Ta Barke A Isra’ila Yayin Da Natanyaho Ke Neman Afuwa Kan Batun Cin Hanci Da Rashawa December 1, 2025 Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar Saudiya Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran. December 1, 2025 Lebanon: Sakon Kungiyar Hizbullah Ga Paparoma December 1, 2025 Ireland Ta Sauya Sunan Wurin Shakatawa Daga Na Shugaban  “Isra’ila” Zuwa Na Shahidiyar Falasdinu November 30, 2025  Gaza: Sau 590 “Isra’ila” Ta Keta Tsagaiwa Wutar Yaki November 30, 2025 Washington Post: Shirin Trump Na Kai Sojojin Gaza Yana Fuskantar Matsala November 30, 2025 MDD: Kasar Somaliya Tana Fuskantar Mawuyacin Yanayi Saboda Fari November 30, 2025 An Yi Ganawa A Tsakanin Ministocin Harkokin Wajen Iran Da Turkiya November 30, 2025 An yi gangami a fadin duniya a zagayowar ranar Falasdinu November 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Najeriya Ta Kara Ƙaimi Wajen Kawar da Cutar HIV Nan da 2030
  • Gwamnatin Kano Ta Kara Jaddada Dokar Haramcin Yin Haya da Babur a Jihar
  • Ministan Harkokin Wajen Turkiya Ya Isa Birnin Tehran Kuma Ya Gana Da Takwaransa Na Iran
  • Pezeshkian: Makiya na neman kawo cikas ga ci gaban kasashen Musulmi
  • Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar Saudiya Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran.
  • Muna buƙatar taimakon ƙasashen waje kan tsaro a Najeriya — Obasanjo
  • Yadda aka horar da mata 100 sana’o’in dogaro da kai a Gombe
  • Asibitin Kula Da Masu Lalurar Ƙwaƙwalwa Na Kaduna Na Bunƙasa Ta Fannoni Daban-Daban
  • Kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi Ta Soki Shirin Donald Trump Na Bayyanata A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda