Aminiya:
2025-12-03@13:17:41 GMT

CBN ya kara yawan kudin da mutum zai iya cirewa a mako zuwa N500,000

Published: 3rd, December 2025 GMT

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya soke iyakance adadin kuɗin da mutum ko kamfani za su iya ajiyewa a banki sannan ya ƙara yawan kudin da za a iya fitarwa a mako da ₦100,000 zuwa ₦500,000.

Wannan na cikin wata sanarwa da Daraktar Sashen Tsarin Kuɗi da Dokoki ta bankin, Dr. Rita Sike, ta sanya wa hannu kuma ta fitar ranar Laraba.

Gobara ta kashe mata da miji da ’ya’yansu 3 a Katsina Mako mai Majalisa za ta kada ƙuri’a kan ƙudurin ƙirƙirar sabbin jihohi

A cewar bankin, an yi sauye-sauyen manufofin ne da nufin rage tsadar sarrafa kuɗi, magance matsalolin tsaro, da kuma dakile haɗarin safarar kuɗi ba bisa ka’ida ba da ke da alaƙa da dogaro da mu’amalar kuɗi kai tsaye.

CBN ya ce manufofin da suka gabata kan kuɗi an gabatar da su ne domin rage amfani da kuɗi kai tsaye da ƙarfafa amfani da hanyoyin biyan kuɗi ta intanet.

Sai dai, sauye-sauyen tattalin arziki da na gudanarwa sun sa dole a sake duba dokokin domin daidaita su da halin da ake ciki a yanzu.

Daga ranar 1 ga watan Janairun 2026, an soke iyakance adadin kuɗin da za a iya ajiye gaba ɗaya, kuma ba za a sake cajin kuɗin da ake ɗauka a kan ajiya mai yawa ba.

Sabbin dokokin sun jingine iyakance fitar kuɗi na mako gaba ɗaya ga mutum ɗaya zuwa ₦500,000, yayin da na kamfanoni ya koma ₦5m.

Kazalika, dokar ta ce fitar kuɗin da ya wuce waɗannan iyakokin zai jawo ƙarin caji na kaso cikin 100 ga mutum ɗaya da kuma kaso biyar cikin 100 ga kamfanoni, inda za a raba kuɗin da aka tara da bankuna bisa tsarin 40:60 tsakanin CBN da bankunan da abin ya shafa.

CBN ya kuma umarci bankuna da su tabbatar da cewa sun saka dukkan nau’o’in kuɗi a cikin na’urar ATM domin sauƙaƙa samun kuɗi.

Babban bankin ya kuma umarci bankuna da su rika gabatar da rahoton wata-wata ga Sashen Kula da Bankuna, Sashen Kula da Sauran Hukumomin Kuɗi, da Sashen Kula da Tsarin Biyan Kuɗi domin tabbatar da bin doka.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

An yi garkuwa da manoma 11 a Kudancin Kaduna

Fargaba ta lulluɓe al’ummar Ungwan Nungu da ke gundumar Bokana a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna, bayan wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mazauna yankin 11 a ranar Asabar yayin da suke dawowa daga gonakinsu.

Mazauna yankin sun ce an tare mutanen ne a wata hanyar daji da ke kusa da unguwar da yamma, inda aka tafi da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Lamarin ya tayar da hankula a ƙauyukan da ke kewaye, inda iyalai da dama suka kwana cikin fargaba.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa wasu daga cikin waɗanda aka sace matasa ne da suka tafi gona domin yin roron wake lokacin da aka afka musu.

NAJERIYA A YAU: Matsalar Kansar Mama Da Hanyoyin Magance Shi ’Yan ta’adda sun kashe ɗan sanda a gidan DPO a Jigawa

Ya ce: “An fara kai hari ne ga mutane 15, wasu sun tsere, wasu kuma aka sake su ba tare da sharaɗi ba. Amma har yanzu mutum 11 suna hannun ’yan bindiga, kuma sun buƙaci a biya su kuɗin fansa na naira miliyan biyar,” in ji shi.

Da yake tabbatar da afkuwar lamarin cikin wata sanarwa a ranar Talata, ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazavar Jama’a/Sanga, Hon. Daniel Amos, ya bayyana satar mutanen a matsayin mugunta da rashin tausayi, tare da yin Allah-wadai da kai hari kan talakawa masu aikin halaliya.

“Muna buƙatar kara tsaurara tsaro, yin amfani da dabarun bayanan sirri, da ɗaukar matakan gaggawa da haɗin gwiwa domin kwantar da hankalin jama’a da kuma ceto waxa0nda aka sace,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Nasarawa Za Ta Gurfanar da Iyayen Yaran da Ba Sa Zuwa Makaranta
  • Mako mai Majalisa za ta kada ƙuri’a kan ƙudurin ƙirƙirar sabbin jihohi
  • An yi garkuwa da manoma 11 a Kudancin Kaduna
  • NAJERIYA A YAU: Matsalar Kansar Mama Da Hanyoyin Magance Shi
  • Yawan Yahudawan Da Suke Ficewa Daga HKI Sun Nininka Har Sau 100%
  • MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar
  • Najeriya Ta Kara Ƙaimi Wajen Kawar da Cutar HIV Nan da 2030
  • Gwamnatin Kano Ta Kara Jaddada Dokar Haramcin Yin Haya da Babur a Jihar
  • Mutum 6 sun jikkata a rikici manoma da makiyaya a Jigawa