An tsare tsohuwar shugabar kula da manufofin ketare ta EU Mogherini bisa badakalar cin hanci
Published: 3rd, December 2025 GMT
Wata sabuwar badakala ta sake bata sunan kungiyar Tarayyar Turai, inda ‘yan sanda suka farmawa gidan toshuwar shugaban kula da manufofin harkokin wajen na kungiyar Federica Mogherini, tare da tsare ta a ranar Talata, a Belgium.
Mogherini wacce ta yi aiki a mukamin tun daga 2014 zuwa 2019, Ita da wasu abokan aikinta biyu ana binciken su kan yadda aka yi amfani da kudaden Tarayyar Turai ba bisa ka’ida ba, cin hanci da rashawa.
Federica Mogherini, jami’ar diflomasiyya ‘yar Italiya mai shekaru 52, ana tsare da ita tare da Stefano Sannino, babban jami’i a Hukumar da kuma mataimakin darakta na Kwalejin Turai.
An kama su, su ukun a wani bangare na binciken da Ofishin Mai Gabatar da Kara na Tarayyar Turai ya jagoranta.
Binciken ya shafi zargin nuna fifiko wajen bayar da shirin horo ga jami’an diflomasiyya.
Ofishin Mai Gabatar da Kara na Tarayyar Turai ya zarge su da “zamba wajen bayar da kwangilolin gwamnati, cin hanci da rashawa, inda ‘Yan sandan Belgium suka gudanar da jerin bincike a ranar Talata a hedikwatar Hukumar Kula da Harkokin Waje ta Tarayyar Turai, a gine-gine da dama na Kwalejin Turai da ke Bruges, da kuma gidajen wadanda ake zargin su uku uku.
Dama dai a cfen baya an gano tarin takardun kudi na Yuro a gidajen ‘yan majalisar dokoki na turai, tare da kyaututtuka daga Qatar, Mauritania, da Morocco. Lamarin da ya girgiza Majalisar Dokokin Turai matuka a watan Disamba na 2022. Ana zargin ‘yan majalisar wakilai da mataimakan majalisar dokoki da dama da karbar cin hanci da rashawa a madadin tasirinsu kan wasu shawarwari na majalisar.
Akwai wasu badakaloli da dama da ake yawan samu a cikin kasashen Turai, musamman game da karkatar da kudaden EU.
A cewar sabon rahoto daga Ofishin Mai Gabatar da Kara na Tarayyar Turai, amfani da kudaden EU ba bisa ka’ida ba ya zama ruwan dare a kasashe 27 na Tarayyar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Nijar ta maka kamfanin hakar uranium na Faransa Orano kotu December 3, 2025 Amurka ta soke bada mafaka ga ‘yan kasashen Afirka 10 December 3, 2025 Masar Ta Sanar Da Tattaunawa Da Amurka Don Shirya Sake Gina Gaza December 3, 2025 Isra’ila Ta Hana Motocin Agaji 6000 Shiga Gaza Duk Da Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta December 3, 2025 Kasar Qatar Ta Gargadi Isra’ila Game Da ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza December 3, 2025 Sharhi: HKI tana fama da karancin sojoji a dukkan rassan sojojin kasar December 2, 2025 Shugaba Pizishkiyan: Goyon Bayan Al’ummar Iran Ga Tsarin Musulunci Ne Ya Hana Abokan Gaba Cimma Manufa December 2, 2025 Shugaban Kasar Najeriya Ya Nada Janar Chiristopher Musa ( Ritaya) A Matsayin Ministan Tsaro December 2, 2025 Nigeria Ta Bai Wa Dan Takarar Shugabancin Kasar Guine Bissau Mafakar Siyasa December 2, 2025 Palasdinu: Sojojin “Isra’ila” 3 Su Ka Jikkata Sanadiyyar Taka Su Da Mota December 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Tarayyar Turai na Tarayyar
এছাড়াও পড়ুন:
Araghchi: Halayyar Amurka ce yin matsin lamba maimakon diflomasiyya a dangantaka ta kasa da kasa
Ministan Harkokin Wajen Iran ya ce: “Bayan zagaye biyar na tattaunawa, yayin da muke shirin zagaye na shida, ɓangaren Amurka ya karya hanyar diflomasiyya da kuma ƙoƙarin shiga tsakani da ake yi.”
Seyyed Abbas Araghchi, Ministan Harkokin Wajen Iran, ya ce a wata hira da ya yi da shirin “Ma’a Musa al-Far’ei” a ranar Litinin: “Abin takaici dokokin ƙasa da ƙasa da tsarin duniya sun yi tasiri ga yanayin Amurka na amfani da ƙarfi a dangantakar ƙasa da ƙasa.”
A cewar Pars Today, Araghchi ya ƙara da cewa: “Wannan ya bayyana a cikin tsoma bakin soja na ba bisa ƙa’ida ba da kuma aiwatar da ayyukan kisan kai duk inda suka ga dama.”
Ya jaddada cewa: “Abin da muke gani a yau ya zama tushen damuwa ta duniya.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Aljeriya: Taron Kasashen Afirka Don Amincewa Da Mulkin Mallaka A Matsayin Laifi December 2, 2025 Lebanon: An Gudanar Da Taron Musulunci da Kiristanci a Beirut tare da halartar Paparoma December 2, 2025 Chuck Schumer: Trump Ba Shi da Ikon Kaddamar da Yaki Kan Venezuela December 2, 2025 Najeriya: Matatar Dangote Za Ta Mika Tataccen Mai Lita Biliyan 1.5 A Watan Disamba December 2, 2025 Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Trump na ware Afirka ta Kudu daga G20 December 2, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 165 December 1, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan 164 December 1, 2025 Baqaei: Amurka Ce Babbar Barazana Ga Zaman Lafiya Da Tsaro A Duniya December 1, 2025 Paparoma Leo Na 14 Yana Ziyarar Aiki Na Kwanaki 3 A Kasar Lebanon December 1, 2025 Kamaru: Madugun Adawa Ya Rasu A Gidan Kaso December 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci