Ministan Tsaro Badaru Abubakar Ya Yi Murabus
Published: 2nd, December 2025 GMT
Daga Bello Wakili
Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa nan take.
Sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce wasikar da Badaru ya aika wa Shugaba Bola Tinubu mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Disambar 2025, ta yi bayanin cewa, ya ajiye aikin ne saboda dalilan lafiya.
Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin tare da gode wa Badaru Abubakar bisa irin gudummawar da ya bai wa ƙasa.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai sanar da Majalisar Dattawa sunan wanda zai maye gurbin Badaru nan da ƙarshen wannan makon.
Badaru Abubakar, mai shekara 63, ya taɓa zama gwamnan jihar Jigawa har sau biyu daga 2015 zuwa 2023. An kuma naɗa shi minista ne a ranar 21 ga watan Agustan 2023.
Murabus ɗinsa ya zo ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkokin tsaron ƙasa, kuma ana sa ran zai fayyace cikakkun matakan da za a ɗauka a nan gaba.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Badaru Badaru Abubakar
এছাড়াও পড়ুন:
Barau ya musanta zargin gwamnatin Kano, ya soki gwamna Abba
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya buƙaci Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya daina siyasantar da harkar tsaro a jihar.
Ya ce kamata ya yi gwamnan ya mayar da hankali kan matsalolin da ke damun jihar.
Yadda ’yan mata ke kuɗancewa da kasuwancin fara a Kano DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed kan zargin kalaman tayar da hankaliBarau, ya yi wannan bayani ne bayan gwamnatin Kano ta zarge shi da yin magana inda ya nemi gwamnatin ta mayar da hankali kan tsaro.
Ya ce matsalolin tsaro a ƙasar nan, ciki har da hare-haren ’yan bindiga a wasu yankunan Kano, suna buƙatar haɗin kai daga kowa.
A cikin wata sanarwa daga mai taimaka masa, Ismail Mudashiru, ya fitar, Barau ya ce zargin gwamnatin ba gaskiya ba ne.
Ya ƙalubalanci gwamnatin ta nuna bidiyon da ya yi maganar da za ta iya haddasa matsalar tsaro.
Ya ce wannan zargi ƙarya ne kuma na da nufin ɓata masa suna.
Ya ƙara da cewa bai taɓa yin wata magana da za ta kawo tangarɗa ga harkar tsaro ba.
A maimakon haka, ya ce yana aiki tare da sauran jami’ai domin inganta tsaro a Kano da sauran sassan Najeriya.
Barau, wanda shi ne Mataimakin Kakakin ECOWAS, ya buƙaci Gwamna Abba da ya “farka daga bacci” ya jagoranci jihar yadda ya kamata.
Ya ce a baya Kano na gogayya da Legas wajen ci gaba, amma rashin kyakkyawan shugabanci ya janyo mata koma baya.
Ya ce ya bai wa rundunonin ’yan sanda motocin aiki, ya bai wa jami’an ’yan sanda babura a Kano ta Arewa, sannan ya gyara wasu sassan hedikwatar ’yan sanda ta Kano.
Haka kuma, ya gina ofisoshin ’yan sanda a wurare daban-daban, ya tallafa wa hukumar DSS, sannan ya taimaka wajen kafa makarantu na horar da jami’an NSCDC, Hukumar Ayyukan ’Yan Sanda, da Hukumar Shige da Fice a wasu yankunan Kano.
Ya ce ya sanya fitilu masu amfani da hasken rana a yankinsa domin taimaka wa zirga-zirga da daddare.
A cewarsa, waɗannan ayyukan suna nuna irin gudunmawar da yake bayarwa wajen inganta tsaro, don haka ya kamata gwamnatin jihar ta yi koyi da shi maimakon ɓata masa suna.