Aminiya:
2025-08-13@17:19:03 GMT

Gwamnatin Gombe za ta ƙirƙiri sabbin ƙananan hukumomi 13

Published: 13th, August 2025 GMT

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya miƙa ƙudiri zuwa Majalisar Dokokin Jihar domin neman amincewarta a ƙirƙiri sabbin ƙananan hukumomi 13.

Gwamnan, ya bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wa gwamnati wajen kusantar al’umma, da ayyukan raya ƙasa.

Jama’a sun koka kan rashin kammala aikin titi a Kafanchan Majalisar Kano ta dakatar da ciyaman kan zargin karkatar da taki

Sabbin ƙananan hukumomin da ake shirin ƙirƙira za su fito daga ƙananan hukumomin da ake da a jihar.

A cewar gwamnan sabbin ƙananan hukumomin za su mayar da hankali kan samar da tsaro, ilimi, kiwon lafiya, gina muhalli da sauran muhimman ayyukan jama’a musamman a yankunan karkara.

Za su kuma yi aiki tare da masarautu da shugabannin al’umma wajen tabbatar da zaman lafiya, bunƙasa ci gaba da magance matsalolin tsaro bisa tanadin dokar masarautu ta jihar.

Sabbin ƙananan hukumomin da za a ƙirƙira su ne Akko Arewa mai hedikwata a Amada, Akko Yamma mai hedikwata a Pindiga, Balanga Kudu mai hedikwata a Bambam, Billiri Yamma mai hedikwata a Tal, Dukku Arewa mai hedikwata a Malala, Funakaye Kudu mai hedikwata a Tongo.

Akwai Gombe Kudu mai hedikwata a Bolari, Kaltungo Gabas mai hedikwata a Wange, Kwami Yamma mai hedikwata a Bojude, Nafada Kudu mai hedikwata a Birin Fulani.

Sauran sun haɗa da Pero-Chonge mai hedikwata a Filiya, Yamaltu Gabas mai hedikwata a Hinna, da Yamaltu Yamma mai hedikwata a Zambuk.

Domin tabbatar da nasarar aiwatar da wannan shiri, ƙudirin ya tanadi kafa kwamiti na wucin gadi da zai jagoranci kowace ƙaramar hukuma har zuwa lokacin da za a gudanar da zaɓe.

Za a aiwatar da shirin a matakai tare da tsare-tsaren aiki, tsarin ma’aikata da kasafin kuɗi da zai tabbatar da harkokin gudanarwa.

Gwamnan, ya roƙi majalisar dokokin jihar da ta duba ƙudirin cikin gaggawa tare da amincewa da shi.

Sannan ya kira ga al’ummar jihar da su goyi bayan shirin wanda ya ce zai bunƙasa mulki da ci gaban Jihar Gombe.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gwamna Inuwa Majalisar Dokoki Yamma mai hedikwata a Kudu mai hedikwata a a mai hedikwata a

এছাড়াও পড়ুন:

Rashin aiwatar da doka na bai wa masu laifi ƙwarin guiwa — Ɗan majalisar Gombe

Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Gombe, mai wakiltar Nafada ta Kudu, Adamu A. Musa, ya zargi gwamnati da ‘yan majalisun jihar da kasa aiwatar da dokokin da suke zartarwa.

Ya ce akwai dokar da aka zartar shekaru takwas da suka gabata domin yaƙi da fyaɗe da cin zarafin mata da yara, amma har yanzu ba a aiwatar da ita ba.

Sojoji sun kashe babban Kwamandan ISWAP, Amirul Fiya a Borno Majalisar Kano ta dakatar da ciyaman kan zargin karkatar da taki

A cewarsa, majalisa tana yin doka sannan ta tura wa gwamna ya sanya hannu, amma daga baya a bar ta kamar ba ta da amfani.

Ya yi gargaɗin cewa irin wannan sakaci yana ƙara wa masu aikata laifi ƙwarin guiwa kuma yana haifar da ƙaruwar manyan laifuka.

Ya ce da ana aiwatar da dokokin, da tuni an rage irin waɗannan laifuka, amma a maimakon haka, idan aka kai rahoton laifi, masu kuɗi suna ɗaukar lauyoyi su fito da su ba tare da an hukunta su ba.

Ya kawo misalin wata ɗaliba a Kano da ake zargin shugaban makarantarsu ya kashe ta, inda tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi alƙawarin aiwatar da hukuncin kisa amma bai yi hakan ba har ya sauka daga mulki.

Haka kuma ya nuna cewa babu wani gwamna a jihohin Arewa da ya taɓa aiwatar da hukuncin kisa ga masu aikata irin waɗannan manyan laifuka.

Sai dai, ya ce zai yi duk mai yiwuwa don ganin a fara aiwatar da dokokin a jihar nan gaba kaɗan.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rashin aiwatar da doka na bai wa masu laifi ƙwarin guiwa — Ɗan majalisar Gombe
  • Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Kafa Sabbin Manyan Makarantu Na Tsawon Shekaru 7
  • Ranar Matasa: Ciyaman ya jinjina wa gwamnatin Gombe kan ɗaukar matasa aiki
  • Gwamnatin Neja Ta Tabbatar Da Kama Hatsabibin Ɗan Bindiga, Abubakar Abba
  • Kungiyar SSANU Ta Ba Gwamnatin Taraba Wa’adin Sati Biyu Akan Kudaden Albashin Da Ba A Biya Ba.
  • ‘Yan Ta’adda Sun Kashe Jama’a A Kauyukan Sakkwato
  • Wani Bangaren Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Da Ta Karbe Mulkin Jihar
  • Rundunar ‘Yan Sandan Kano Ta Yi Gargadi Game Da Sabawa Dokokin Fitillun Bada Hannu A Titinan Jihar
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Damina Ke Shafar Masu Ƙananan Sana’o’i