Mutane 9,854 na ɗauke da cutar AIDS a Yobe
Published: 2nd, December 2025 GMT
Gwamnatin Yobe ta bayyana cewa aƙalla mutane 9,854 ne ke ɗauke da cutar AIDS a jihar, kuma dukkaninsu na karɓar maganin ceton rai.
Hukumar ta tabbatar da cewa waɗannan marasa lafiya suna rayuwa cikin ƙoshin lafiya, tare da rage yiwuwar yaɗa cutar ga wasu.
Babban Daraktan Hukumar Kula da Cutar AIDS ta Jihar Yobe (YOSACA), Dakta Jibril Adamu Damazai, ne ya bayyana cewa Yobe na da mafi ƙarancin adadin masu ɗauke da cutar a ƙasar nan da kashi 0.
“Ba mu tsaya a kan wannan nasara ba, muna ƙara ƙoƙari don rage yawan kamuwa da cutar,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta kashe sama da Naira miliyan 120 wajen sayen kayan gwaji, abin da ya bai wa ƙungiyoyi damar gano mutanen da ba a san suna ɗauke da cutar ba a cikin al’umma, domin a ba su magani.
A cewarsa, Yobe na kan gaba wajen daidaita dabarun yaƙi da cutar AIDS, musamman ganin yadda ake samun sauye-sauye a kuɗaɗen da ake kashewa a duniya.
Dakta Damazai ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta fara shirye-shiryen samar da magungunan ƙwayar cutar HIV a cikin gida.
Ya yaba da jajircewar gwamna Mai Mala Buni, wanda ya ƙara kuɗaɗen da ake bai wa hukumar kula da cutar AIDS da kashi 400%, tare da samar da katafaren ofis na dindindin ga hukumar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ɗauke da cutar da cutar AIDS
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun ceto ’yan mata 12 da ISWAP suka sace a Borno
Sojojin Rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), sun samu nasarar ceto ’yan mata 12 da ’yan ta’addan ISWAP suka sace a gundumar Mussa da ke Ƙaramar Hukumar Askira/Uba a Jihar Borno.
An sace su ne ranar 23 ga watan Nuwamba 2025, yayin da suke girbe amfanin gonakin iyayensu.
Yaran ’yan shekaru 15 zuwa 20 ne.
Wannan ya haifar da firgici a yankin, lamarin da ya sa mazauna yankin da dama suka tsere zuwa wasu garuruwa.
Majiyar tsaro ta tabbatar da cewa an ceto su lafiya, duk da cewa ba a bayyana yadda aka ceto su ba.
Har yanzu ba a san ko an biya kuɗin fansa.
Waɗanda aka ceto sun haɗa da Fatima Shaibu (17), Fatima Umaru (15), Hauwa Abubakar (18), Saliha Muhammad (15), Sadiya Umaru (17), Amira Babel (15).
Sauran sun haɗa da Zara Adamu (17), Nana Shaibu (15), Zainab Musa (18), Zainab Muhammad (17), Jamila Saidu (15) da kuma Hauwa Hamidu (17).
An kai su wani waje na musamman domin duba lafiyarsu kafin a sada su da iyayensu.
Wannan na zuwa ne bayan sojoji sun farmaki maɓoyar ISWAP da ke Kudancin Borno.
Iyayen yaran sun bayyana farin cikinsu, inda suka bayyana hakan a matsayin babbar nasara.