Mako mai Majalisa za ta kada ƙuri’a kan ƙudurin ƙirƙirar sabbin jihohi
Published: 3rd, December 2025 GMT
Majalisar Wakilai za ta ƙada kuri’a a ranakun 10 da 11 ga watan Disamba kan muhimman kudurorin gyaran kundin tsarin mulkin 1999, ciki har da kirkirar sabbin jihohi da kafa ’yan sandan jihohi.
Mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Okezie Kalu, ya sanar da jadawalin a zaman majalisar, inda ya ce tattaunawa kan kudirin sauya kundin tsarin mulki za ta gudana yau da gobe kafin kada kuri’ar mako mai zuwa.
Kalu, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar kan nazarin kundin tsarin mulki, ya bukaci ’yan majalisa su halarci zaman.
Ya shaida wa majalisar kwanan nan cewa kwamitin ya kammala aikin da ake bukata a wannan mataki, kuma yana shirin gabatar da takardun da aka daidaita don a yi la’akari da su.
A farko dai an gabatar da jimillar kudirori 87 da ke neman sauya sassa daban-daban na kundin tsarin mulki.
Kudirorin sun shafi gyaran harkokin zabe da shari’a, ’yan sandan jihohi da batutuwan kudi.
Sai dai bayan jin ra’ayin jama’a a matakin jihohi, taron jin ra’ayin jama’a na kasa a Abuja, tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma daidaitawa da kwamitin majalisar dattawa kan kundin tsarin mulki, adadin kudirin da za a kada kuri’a ya ragu zuwa kusan 45.
A ranar Litinin, 24 ga watan Nuwamba, kwamitocin majalisar wakilai da na majalisar dattawa kan gyaran kundin sun gudanar da taron hadin gwiwa da kakakin majalisun jihohi a Abuja yayin da tsarin sauya kundin ya shiga matakin karshe.
Kalu da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, sun shaida wa kakakin majalisun jihohi cewa makomar kudirin sauye-sauyen yanzu ta dogara ne da majalisun jihohi bayan majalisar tarayya ta kammala aikinta. Kalu ya ce taron ya nuna matakin karshe kafin fara kada kuri’a.
Muhimman kudirorin da ake son gyarawaDaga cikin muhimman sauye-sauyen da aka gabatar kirƙirar ’yan sandan jihohi, ware kujeru na musamman ga mata a majalisa, ’yancin tsayawa takara ba tare da jam’iyya ba, karin ayyuka ga sarakunan gargajiya, karfafa ikon majalisar tarayya da ta jihohi wajen kira shugaban ƙasa da gwamnonin jihohi kan harkokin tsaro da sauransu.
Kazalika, wani kudiri na neman sauya kundin domin mayar da gudanar da zaben kananan hukumomi daga hukumar zabe ta jihohi zuwa INEC.
Haka kuma, wani kudiri na neman tabbatar da cewa a kammala dukkan shari’un zabe kafin rantsar da zababbun jami’ai.
Babban kudiri kuma shi ne na neman kafa ’yan sandan jihohi ta hanyar sauya kundin tsarin mulki domin cire su daga jerin dokokin tarayya zuwa jerin dokokin hadin gwiwa.
Masu goyon baya sun ce wannan mataki zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro da suka yi yawa kuma suke neman fin ƙarfin ’yan sandan tarayya.
Kallo zai koma majalisun jihohiBayan an kammala kada kuri’a, za a tura kudirin da aka amince da su zuwa majalisun jihohi 36 don samun amincewa.
Aƙalla majalisun jihohi 24 (wato kashi biyu bisa uku) dole ne su amince da shi kafin a tura su ga shugaban ƙasa don ya sanya hannu.
Duk kudirin da bai samu amincewar jihohi ba zai mutu nan take.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Wakikai kundin tsarin mulki yan sandan jihohi sauya kundin
এছাড়াও পড়ুন:
Jagoran ‘Yan Democrat a Majalisar Dattawa: Trump Ba Shi da Ikon Kaddamar da Yaki Kan Venezuela
Jagoran ‘Yan Jam’iyyar Democrat na Majalisar Dattawa Chuck Schumer ya zargi Shugaban Amurka Donald Trump da shirya yaƙi a ɓoye a kan kasar Venezuela, yana mai jaddada cewa ikon ayyana yaƙi ya rataya ne kawai a kan Majalisa, kuma dan majalisar ya bayyana cewa zai gabatar da kuduri don hana tura sojojin Amurka yaki a Venezuela.
Schumer ya tabbatar da cewa Trump ba shi da ikon aika sojojin Amurka zuwa yaƙi ba tare da izinin Majalisa ba, yana mai bayyana cewa wannan ikon an keɓe shi ne ga Majalisa kaɗai.
A cikin wata sanarwa, Schumer ya zargi Trump da shirin yaƙi a ɓoye da Venezuela, yana mai gargadin cewa Majalisa za ta ɗauki mataki nan take don gabatar da kuduri zai hana hana tura sojojin Amurka zuwa wannan yaki da yake Shirin kaddamarwa.
Schumer ya ce mutanen Amurka ba sa son wani yaƙi da ba a san karshensa ba, ya ƙara da cewa duk wani mataki mai ƙarfi a kan Venezuela ba tare da amincewar majalisa ba zai zama babban kure da kuma sab awa doka.
A wani labarin kuma, Schumer ya bayyana cewa ya sami barazana ta imel, daga abin da ya kira “MAGA” ko kuma (Make America Great Again) wato gungun da ke mara baya ido rufe ga siyasar Trump, kuma ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro a New York sun sanar da shi barazanar da aka yi lokuta daban-daban na dana bam a ofisoshinsa.
A ranar Asabar da ta gabata, shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa za a rufe sararin samaniyar Venezuela da yankin da ke kewaye da ita gaba daya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya: Matatar Dangote Za Ta Mika Tataccen Mai Lita Biliyan 1.5 A Watan Disamba December 2, 2025 Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Trump na ware Afirka ta Kudu daga G20 December 2, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 165 December 1, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan 164 December 1, 2025 Baqaei: Amurka Ce Babbar Barazana Ga Zaman Lafiya Da Tsaro A Duniya December 1, 2025 Paparoma Leo Na 14 Yana Ziyarar Aiki Na Kwanaki 3 A Kasar Lebanon December 1, 2025 Kamaru: Madugun Adawa Ya Rasu A Gidan Kaso December 1, 2025 Tawagar ECOWAS Ta Bar Guinea – Bissau bayan da shugaban kasar yayi barazanar korarsu Da Karfi December 1, 2025 Yawan Yahudawan Da Suke Ficewa Daga HKI Sun Nininka Har Sau 100% December 1, 2025 Gaza: Fiye da Falasdinawa 350 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila tun bayan tsagaita wuta December 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci