Aminiya:
2025-12-01@16:41:35 GMT

An kama ’yan bindiga 4 a Kano

Published: 1st, December 2025 GMT

An kama wasu mutum huɗu da ake zargin ’yan bindiga ne ɗauke da makamai da ake zaton bindigogi ne a tashar mota ta Ƙofar Ruwa da ke Jihar Kano.

Tashar motar, wadda ke kusa da kasuwar kayan gini ta Ƙofar Ruwa a Ƙaramar Hukumar Dala.

MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar Sarkin Musulmi ya buƙaci gwamnonin Arewa suke saurarar ƙorafin jama’a

A cewar mazauna yankin, an kama mutanen ne lokacin da suke ƙoƙarin shiga mota domin tafiya zuwa wani waje a cikin Kano.

“Mutanen da ke tashar motar ne suka lura da makaman da suke ɗauke da su. Take suka gaggauta sanar da jami’an tsaro, waɗanda suka kama su. Su huɗu ne gaba ɗaya,” in ji Musa Balarabe, wani mazaunin yankin.

Ya ce an kama su ne da misalin ƙarfe 1 na rana.

Da farko an kai su ofishin ’yan sanda na Ƙofar Ruwa, kafin daga bisani aka mayar da su ofishin Dala.

Wani mazaunin yankin, Umar Nuhu, ya ce yana cikin shagonsa da ke Kwanar Taya, kusa da ofishin ’yan sandan, lokacin da aka kawo mutanen.

Ya ce hakan ya jawo firgici, inda mutane suka fara gudu a ko’ina.

Nuhu, ya ƙara da cewa mutane da yawa sun yi dandazo a ofishin ’yan sandan, yayin da wasu matasan ke son ɗaukar doka a hannu.

Da aka tuntuɓi kakakin ’yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, bai ce komai kan lamarin ba.

Ya ce har yanzu suna tattara bayanai kafin su fitar da sanarwa.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sabuwar sanarwa daga rundunar ’yan sandan jihar.

Tashar Kofar Ruwa, tasha ce da ke jigilar fasinjoji zuwa jihohi irin su Katsina, Jigawa, Sakkwato, Zamfara, Kebbi, har ma da Jamhuriyar Nijar.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Jihar Kano ke fama da hare-haren ’yan bindiga, musamman a yankunan da ke da iyaka da Jihar Katsina.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Yan Sanda Kofar Ruwa mutanen gari

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya sake aike wa majalisa ƙarin sunayen jakadu 32

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya sake aike wa Majalisar Dattawa ƙarin sunayen mutum 32 domin tantance su a matsayin jakadu.

Sunayen sun haɗa da manyan mutane kamar tsohon shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Femi Fani-Kayode, da Reno Omokri.

Muna buƙatar taimakon ƙasashen waje kan tsaro a Najeriya — Obasanjo Yadda aka horar da mata 100 sana’o’in dogaro da kai a Gombe

An raba sunayen zuwa kashi biyu; na farko yana ɗauke da sunan mutum 15 waɗanda suke da gogewar aikin jakadanci da kuma waɗanda ba su gogewar aikin jakadanci mutim 17.

Wasu daga cikin fitattu da suka shiga jerin sun haɗa da tsofaffin gwamnonin kamar Ifeanyi Ugwuanyi da Victor Okezie Ikpeazu, matan tsofaffin gwamnoni kamar Angela Adebayo da Florence Ajimobi, da kuma Sanata Jimoh Ibrahim.

Bayan tantancewa, za a tura jakadun zuwa ƙasashe irin su China, Indiya, Kanada, UAE, Afrika ta Kudu, da Kenya.

Sauran wuraren sun haɗa da manyan cibiyoyi na ƙasa da ƙasa kamar Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), UNESCO, da Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU).

Za a bayyana inda za a tura kowane, bayan Majalisar Dattawa ta tantance su.

A makon da ya gabata ne, Tinubu ya tura sunayen mutum uku da ake sa ran tura su Amurka, Birtaniya ko Faransa.

Shugaban ya ce za a sake fitar da ƙarin sunayen jakadu nan ba da jimawa ba.

Wannan mataki na cikin shirin Tinubu na karfafa hulɗar diflomasiyya ta hannun ƙwararru da gogaggun mutane don wakiltar Najeriya a ƙasashen waje.

Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta fara tantance su cikin makonni masu zuwa, kafin su kama aiki.

Masu sharhi kan sha’anin siyasa suna ganin waɗanda aka zaɓo ƙwararru ne kuma za su taka muhimmiyar rawa a harkokin siyasar gida da waje.

Da dama na ganin cewa waɗannan naɗe-naɗen za su iya taka rawa wajen tsara sabuwar hanyar hulɗa da ƙasashen waje da manufofin diflomasiyyar Najeriya a nan gaba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa  masu ibada a Kogi 
  • Olisa Metuh ya sauya sheƙa zuwa APC, ya ce PDP ta manta da shi
  • Sojoji sun ceto ’yan mata 12 da ISWAP suka sace a Borno
  • ’Yan bindiga sun sace amarya da ƙawenta 14 a Sakkwato
  • Sojoji sun ceto mutum 7 da ’yan bindiga suka sace a Kano
  • ’Yan bindiga sun kashe tsohuwa, sun sace mutum 3 a Kano
  • Tinubu ya sake aike wa majalisa ƙarin sunayen jakadu 32
  • Shaikh Niam Qasem: Hizbullah ce Za ta Mayar Da Martani Lokacin Da Ya Dace Kan Kisan Kwamandanta
  • Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali