HausaTv:
2025-08-13@20:53:22 GMT

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 124

Published: 13th, August 2025 GMT

124-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahhari, ko kuma cikin littafin mathnawa na maulana Jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sarir Imam Al-Hassan Almujtaba (a) diyar Fatima (s) kuma jikan manzon All..(s) na farko da muke kawo maku, idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun bayyana yadda.

Yadda aka yi karamin yakin Jamal, wanda ya faru bayan da Rundunar Aisha matar manzon All…(s) da talha da zubai suka kwace birnin Basra, suka saba alkawarin da suka kulla da gwamnan garin Uthman bin Hunaifa al-ansari. Suka kamashi suka azabtar da shi, harma suna son kashe, sai wata mataha ta roki Aisha ta barshi. Sai ta amince amma ta jefashi a gidan yari. Sannan ta kashe dukkan masu gadin baitul Mali sabran, basu da makami a hannunsu. Alokacin Hakim dan Jabala ya ji labarin haka, sai ya fito da mayaka kimani 300 wasu sunce 700 ya fada masu, mayakan aisha sun kashe su gaba daya.

Ance a lokacin yakin, wani daga cikin mayakan Aisha sun yanke kafar Hakim guda,sai ya kama mutumin ya kashe da kafarsa da ya yanke, sannan yaci gaba da yaki har sai da aka kada shi tare da wasu yanuwansa ukku. Duk sun yi shahada wajen kare amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a).   Ana kiran wannan yakin Jamal Karami saboda Jamal babban shi ne yakar Amirumumina (a) ta yi daga baya. Sannan a madina kuma Imam Ali (a) yana shirin yakar muawiya dan Abisufyan, walin kufa wanda yayi tawaye, ya ce ba zai yi bai’a wa Imam Ali (a) sai ya kashe wadanda suka kashe Khalifa Uthman. A cikin wannan halin labari ya zo masa kan abinda Aisha da Talha da Zubair suka shirya.

Daga nan sai yaga cewa yakar Aisha da Talha da Zubair da farko yafi, saboda su suka fi hatsari a lokacin. Daga sai ya fita tare da wadanda suke tare da shi a Madina na manyan-manyan sahabban manzon All…(s). wasu laman tarihi sun bayyana cewa akwai akalla sahabban manzon All..(s) tare da Aliyu (a) wadanda suka kai 70. Wasunsu sun halarci sulhun Hudaibiyya. Sannan a lokacinda ya isa Rabza, sai yayi zango a can nay an kwanaki don ya kara da shi. Har’ila yau yana nan Rabzata ne labarin ya zo masa kan cewa Aisha da Talha da Zubair sun sun kwace barsara sun kuma fara yada fasadi a bayan kasa.

Don haka yayi sauran ya aiki mutane biyu zuwa Kufa kan suyi shirin fitowa don yakar masu tada fitina a Basra. Ya aiki Muhammadn Abubakar, da kuma Muhammad an Jaafar Attayyar .

Ance shi wanda aka fara sanyawa suna Muhammad bayan bayyanar musulunci kuma shi ne ya auri Ummu Kulthum diyar Fatimah (s) diyar manzon All..(s). Yayansa Abdullahi dan Jaafar ne ya auri Zainab (a) jarumar Karbala. Yana da dan uwa da ake kira Aun.

Ya rubuta wasika ya basum su kaiwa walin Kufa a lokacin Abu musa Alashari. Wasikar tana haka. [Ni na zabeku ne kan sauran birane, na kuma koma gareku ne saboda abinda ya faru, ku kasance masu taimakawa addinin All..masu kuma kai masa dauki, ku taimaka mana ku kuma yi yunkuri don taimakommu, Mu dai kyara muke so, don al-umma ta zama yanuwan juna duk wanda yake son wannan, ya kuma zabeshi, hakika ya so gaskiya, wanda kuma ya ki hakan ya ki gaskiya, ya yi watsi da ita.]

Da haka kuma yan aike guda biyu wato Muhammad dan Abubakar da kuma Muhammad dan Jaafaru. Sun kama hanya har suka isa Kufa, suka mikawa Abu Musa Al-shari wasika don karfafasu kan abinda ya zo da su na kirin mutane zuwa ya ki da Aisha da talha da zubair.

Amma sakon Imam (a) bai samu karbuwa daga wajen Abumusa ba, saboda ya bayyana halayen da ba’a saba saninsa da su ba. Ya hana mutane sauraron yan sakon Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a). daga nan sai suka fara mu’amala da Abumusa Alashari da kaushi suna masa tsawo saboda ya yana mutane taimaka amirulmuminina (a) dan abitalib (a).

A lokacinda suka matsa masa, sai ya ce masu, ‘Wallahi, lalle bai’ar Uthman ta na kan wuyata, da kuma wuyar mutuminku, (ya na nufin Amirul muminina(a) idan har ya zama wajibi sai an yi yaki, to da farko sai an warware batun wadanda suka kashe Uthman).

Daga nan sai suka aikawa Imam Aliyu(a) dalla-dallan abinda ya faruwa a kufa da kuma mummunan matsayin da Abu Musa Al-Ashari ya dauka na yin masa tawaye. Da kuma hana mutane sauraron abinda suke fata.

Dagan a sai Imam (a) ya rubuta wata wasika ya bawa Hashim Al-Mirqal ya kaiwa Abumusa Al-Ashari, kuma ga binda ya zo cikin wasikar

{Lallai ni aiki Hashimu don ya kira mutane wadanda suke tare da kai su su shirya yaki su fito zuwa gareni, ka fadawa mutane, kuma lallai ne ban sanya gwamna ba sai don ka kasance cikin wadanda zasu taimaka mani a kan gaskiya.}. Sai Hashim ya kama hanya har ya isa Kufa, ya mikawa Abumusa Al-Ashari wasikar Imam (a). ya karantata amma kuma y adage a kan tawayensa, da kuma toshe hanya wa mutane su fahinci gaskiya.

A lokacinda suka matsa masa, sai Abu musa Al-ashari ya kira, Sa’ib dan Malikul As’ari(s) don ya bashi shawara kan al-amarinsa. Sai Malih al-ash’ari ya bashi shawara kan ya kasance tare da Imam (a) kada ya saba masa.

A lokacinda Hashim ya ga haka, sai ya aikawa Imam (a) wasika, inda ya bayyana masu ci gaba da nuna taurine kai da abu musa al-ashari yake yi. Don haka ya kasa shawo kansa.

A nan ne sai Imam (a) ya aiki dansa Imam Alhasan Al-mujtaba da kuma Ammar dan yasir da wasu. Ya aiki Imam Hassan (a) da wasika na tube Abumusa Al-ashari daga gwamnan Kufa, ya kuma maye gurbinsa da Qurdah dan Kaab ba-ansare.

Wannan shi ne Nissan takardan da Imam(a) ya rubuta (( Bayan haka, hakika ina ganin ka kaucewa wannan al-amarin, wanda nake ganin All.. bai sanya maka rabo a cikin sa ba, saboda ka ki aiwatar da umurnina. Hakika na aiki Hassan dan Aliyu da na, da Ammar dan Yasir su kira mutane su yi shirin yaki tare da ni. Kuma na aiki Qurdah dan Kaabu a matsayin sabon walin birnin Kufa, ka sauka daga aikimmu kana kaskantacce abin zargi, idan ka ki sauka na umurce shi ya tilasta maka yin hakan)).

Imam Hassan (a) ya Isa kufa mutanen kufa sun kewayeshi, suna girmamashi, da dama daga cikin musulmi a Kufa basu taba ganin Jikan manzon All..(s) ba, don haka sun fito don ganinsa da kuma girmama shi.

A dai-dai wannan lokacin ne sai Imam Hassan ya bayyana masu kan cewa an tube Abumusa Al-ashari wanda yake bayyana tawaye da rashin biyayya ga Amirul Muminina (a). da kuma gabatar da Qurdata a matsayinsa.

Sai dai duk da haka Abu musa ya ci gaba bayyana matsayinsa na rashin biyayya ga Amirulmuminin (a). da ya ji sanarwan Imam Hassan (a), na tube shi da kuma maye gurnsa da Qurdatah dan Kaabu. Amma Abu musa ya ci gaba da taurine kansa. Sai Imam Hassan (a) ya na masa maga da taushi, inda y ace masa: ya kai Abu Musa Wallah ba abinda muke bukata sai Alkhairi. Ba kuma kamar Amirulmuminina ne za’a ji tsoron wani abu daga wajensa ba : Sai Abu musa yace: Gaskiya ka fada, iyayena fansarka. Amma wanda ake neman shawararsa amintacce ne. sai Imam yace :ee.

Sai yace ya ji manzon All..(s) yana cewa: Lalle akwai fitina kasance, wanda ya zauna yafi wanda ya tashi, wanda yake zaune yafi wanda yake tafiya, wanda kuma yake tafiya ya fi mahayi. …..

Sai Ammar dan Yasir ya ce masa. Ka ji wannan daga manzon All..(s). Ya ce: ee, sai Ammar ya juya ta mutane yace masu, lalle manzon All..(s) yana nufin Amu musa ne, ya na zaune ya fi masa da ya tsaya.

Sai duk wannan bai hana Abu Musa gano abinda yakamata ya yi ba. Sai Imam Hassan (a) ya fuskanci mutane yana masu magana kan nsu shirya fita yaki. Yana cewa

 [Ya  ku mutane! Lalle Amirulmuminina yana da abinda ya isheku kome, Mun zo wajenku ne don kiraku zuwa yaki, don ku ne na gaba-gaba a yaki a cikin birane,kuma kune shugabannin larabawa. Kuma kunji yadda Talha da Zubair yadda suka kwace bai’arsu da kuma yadda suka fido da Aisha. Kamar kuka ji. Kun san raunin mata, da kuma yadda ra’ayinsu yake kaiwa da asara. Don haka ne All..ya sanyan mata masu kula da mata.

Na rantse da All..idan ba wanda ya taimaka masa, banda wadanda suke tare da shin a Muhajiruna da Ansar da sun wadatar da shi. Da wadanda All…ya aiko masa na daga cikin zababbu ya wadatar da shi, don haka ku taimakawa All..ya taimaka maku. ]. 

Sai ammar dan yasir ya tashi ya yi wa mutane jawabi dangane da yaki da kuma dangane da Uthman yace: Ya ku mutanen Kufa: duk da cewa labarimmu ya boye daga gareku amma al-amarinku ya riskeku. …

Zamu karasa wannan maganar a shirimmu nan gaba.

A nan kuma zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All,,, ya kaimu, wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barkatuhu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 125 August 13, 2025 Iran: Babu Mika Kai Ga Takurawar kasashen Yamma har sai An Kawo Karshen Barazana August 13, 2025 Hukuma Mai Kula Da Sauka Da Tashin Jiragen Sama A Paris Ya Dakatar Da Wani Ma’aikacinta August 13, 2025 Iraki Tace: Ita Yentacciyar Kasashe Ce Bayan da Amurka Ta Yi Korafi Kan Yarjeniyar tsaro da Iran August 13, 2025 Ministan Harkokin Wajen Masar Ya sake Ganawa da Aragchi Da Kuma Gorossy August 13, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Alhininsa Kan Kashen Masanan Kasar Iran Da ‘Yan Sahayoniyya Suka Yi August 13, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Lokaci Ya Yi Da Za A Daina Kakaka Takunkumi Da Ba Dace Ba Kan Kasashe August 13, 2025 Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran Ya Jaddada Kasancewar Iran Tare Da Kasar Lebanon Koda Yaushe August 13, 2025 Kasar Iraki Ta Ce: Yarjejeniyar Da Ta Kulla Da Iran Zai Amfani Dukkan Kasashen Yankin August 13, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’Ila Har Sau Shida  August 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Abumusa Al ashari musa Al ashari musa al ashari wadanda suka

এছাড়াও পড়ুন:

Bankin Duniya zai kashe $300m domin inganta rayuwar ’yan gudun hijira a Arewacin Nijeriya

Bankin Duniya ya amince da bayar da dala miliyan 300 domin aiwatar da wani sabon shiri da zai inganta rayuwar ’yan gudun hijira da kuma al’ummomin da suka ba su matsugunni a Arewacin Nijeriya. 

Bankin ya bayyana cewa a ƙarƙashin shirin mai suna Solutions for the Internally Displaced and Host Communities Project wato SOLID, wanda aka amince da shi a ranar 7 ga Agusta, za a lalubo hanyoyin da za a bi wajen taimakon ’yan gudun hijira, da ma garuruwan da suke rayuwa a ciki.

Dasuki: Kotu ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kammala shari’ar kuɗin makamai Nijeriya ta sake ƙulla alaƙar tsaro da Isra’ila

Ya bayyana cewa shirin SOLID zai ruɓanya ƙoƙarin da gwamnati ke yi da ma wanda sauran abokan hulɗa suka riga suka gudanar, ciki har da Shirin Farfado da Yankunan Da Rikici Ya Shafa (MCRP).

Haka kuma, bankin ya jaddada cewa rikice-rikicen tsaro da rashin kwanciyar hankali da ke gudana a yankin sun raba mutane fiye da miliyan 3.5 da muhallansu, lamarin da ya shafi ababen more rayuwa, wanda a cewar bankin hakan ya sa ababen more rayuwan suka yi ƙaranci a garuruwan da suke zama.

Daraktan Bankin Duniya a Nijeriya, Mathew Verghis, ya ce: “Muna farin cikin ƙaddamar da wannan shiri mai matuƙar tasiri da zai taimaka wa Nijeriya magance ƙalubalen da take fuskanta wadanda suka shafi ’yan gudun hijira”

“Daga cikin ɓangarorin da za mu mayar da hankali akwai rage illolin sauyin yanayi, samar da haɗin kai ta hanyar sasanci, tallafa wa iyalai da inganta ababen more rayuwa.

“Muhimman fannoni sun haɗa da gina ababen more rayuwa masu jure wa sauyin yanayi, ƙarfafa zaman lafiya, tallafa wa hanyoyin samun abin yi, da kuma ƙarfafa cibiyoyi domin su iya magance matsalolin da tsugunar da ’yan gudun hijirar ya haifar.”

Bayanai sun ce shirin SOLID na iya amfanar da mutane kusan miliyan 7.4, wadanda daga cikinsu miliyan 1.3 ’yan gudun hijira ne.

Za a aiwatar da shirin ne ta hanyar tsari na haɗin gwiwar al’umma, tare da shigar dukkan bangarorin gwamnati da kuma haɗin kai da ƙwararrun abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 130
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 129
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 128
  • Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 127
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 126
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 125
  • Bankin Duniya zai kashe $300m domin inganta rayuwar ’yan gudun hijira a Arewacin Nijeriya
  • Mahukuntan Iraki Sun Bayyana Cewa: Akwai Yiwuwar Masu Ziyarar Arba’een Na Imam Husaini {a.s} Zasu Zarce Miliyan 4
  • Ya ba wa alaramma kyautar motarsa saboda daɗin karatun Alkur’ani