Daga Shamsuddeen Mannir Atiku 

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta karɓi daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya zarce naira miliyan dubu dari tara da tamanin da biyar daga bangaren zartarwa jihar.

Da yake gabatar da kasafin kudin a  zauren majalisar, Gwamna Malam Uba Sani ya bayyana kasafin a matsayin na sauye-sauye da ci-gaba wanda aka tsara domin bunkasa al’umma cikin tsarin da ya haɗa kowa da kowa.

Ya ce gabatar da kasafin kuɗi muhimmin al’amari ne na dimokradiyya da ke bai wa gwamnati damar yin waiwaye, da tantance nasarorin da aka samu, da kuma fayyace hanyoyin ci gaba na shekara mai zuwa.

Gwamnan ya bayyana cewa an ware sama da naira biliyan dari shida da casa’in da tara daidai da kashi kashi 71 ga manyan ayyukan ci gaba, yayin da sama da naira biliyan dubu dari biyu da tamanin da shida daidai da kashi 29 za su tafi ga al’amuran yau da kullum.

Ya ce kaso mafi tsoka na ayyukan ci gaba ya mayar da hankali ne kan gina manyan muhimman ababen more rayuwa masu dorewa.

Rabe-raben kason sune: Ilimi ya samu kashi 25 bisa dari, sai  Ayyukan Gine-gine da Cigaban KarKarkashi ma kashi 25 bisa 100, Lafiya kashi 15 bisa 100; Noma da Samar da Abinci  kashi 11 bisa 100; Tsaro kashi 6 bisa 100; Ci gaban Zamantakewa kashi 5 bisa 100; Muhalli da Matakan Sauyin Yanayi kashi 4 bisa 100; sai Mulki da Gudanarwa kashi 5 bisa 100.

A nashi jawabin, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman, ya ce kasafin kuɗin 2026 ya nuna sahihiyar manufa wadda ta ƙunshi faɗaɗa ababen more rayuwa a yankunan karkara, da habbaka kwazon ma’aikata da tabbatar da ganin dukkan al’ummomi suna cin gajiyar ci gaba mai ɗorewa da ya haɗa kowa.

Rt. Hon. Liman ya jinjina ga Gwamna Uba Sani da tawagarsa a bisa gabatar da kasafin da ya dace da hangen nesan gwamnatin da ke ƙoƙarin gina Jihar Kaduna mai  yalwar arziki.

Ya kuma gode wa gwamnan bisa samar da zaman lafiya, haɗin kai da sabunta kudurori a fadin jihar, tare da yabawa gwamnan bisa rashin yin katsalandan cikin harkokin majalisar wanda hakan alama ce dake nuna cikakken tsarin rabon iko da ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ingantaccen sa ido da daidaito tsakanin bangarorin gwamnati.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jihar Kaduna

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Za ta Kauracewa taron fasalta kasashen da za su halarci  gasar cin kofin duniya na shekara ta 2026

Rahotanni sun bayyana cewa hukumar kwallon kafa ta kasar iran ta sanar cewa  za ta kauracewa taron da za’a yi  a makon gobe a birnin Washington bayan da kasar Amurka ta ki yarda ta bada shedar izinin shiga kasar ga wasu daga cikin wakilanta

Kakakin hukumar kwallon kafa ta kasar iran yace mun riga mun sanarwa da hukumar kwallon kafa ta duniya fifa cewa wannan matakin ba shi da wata alaka da wasanni , kuma wakilan kasar iran din ba za su halarci gasar kofin duniya ba .

Wannan yazo ne bayan da hukumar kwallon kafa ta kasar iran ta sanar cewa Amurka ta hana wasu daga cikin jami’anta visa shiga Amurka ciki har da shugaban hukumar Mahdi Taj,

Ana sa bangaren Mahdi Taj ya bayyana mataki a matsayin na siyasa kuma ya fadawa hukumar fifa cewa wannan matakin na Amurka siyasace zalla don haka yayi kira gareta da ta shiga tsakani don warware takaddamar.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka China Ta Gargadi Amurka Akan Batun Yakar Kasar Venezuela November 28, 2025 Palasdinu: Kwamandoji Biyu Na Rundunar “Sarayal-Quds” Sun Yi Shahada A Yammacin Kogin Jordan November 28, 2025 Kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi Ta Soki Shirin Trump Na Bayyanata A Matsayin Kungiyar Ta’addanci November 28, 2025 Kasashen Qatar Da Jordan Sun Yi Allawadai Da Harin “Isra’ila” A Kasar Syria November 28, 2025 Senegal: Hambararren Shugaban Kasar Guinea Bissau Ya Isa Kasar Senegal November 28, 2025 Limamin Tehran: Hadin Kai Ne Sakamakon Imani Da Ayyukan Kwarai Ne November 28, 2025 Yamen Ta Soki Kasashen Birtaniya Da Amurka Da Tsoma Baki Kan harkokin Kasarta November 28, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 10 A Wani Hari Da Ta Kai A Birinin Damaskas Na Kasar Siriya November 28, 2025 Jagoran : Amurka Ta Sha Kashi A Yakin Kwanaki 12 Duk Da Manyan Makamanta Na Zamani November 28, 2025 Ministocin Tarayyar Turai Sun yi Tir Da Karuwar Hare –Haren Da Yahudawa Ke Kai wa Falasdinawa November 28, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Kano Ta Kara Jaddada Dokar Haramcin Yin Haya da Babur a Jihar
  • Jihar Jigawa Ta Mayar da Rarar Kudi Sama da Naira Miliyan 50 Ga Maniyyatan Aikin Hajjin 2026
  • Cinikin Kasashen Waje na Iran Ya Zarce Dala Biliyan 76.5
  • Likitoci sun gindaya sabon sharaɗi bayan janye yajin aiki
  • Trump Ya Bada Sanarwan Rufe Sararin Samaniyar Kasar Venezuela Gaba Daya
  • Barau ya musanta zargin gwamnatin Kano, ya soki gwamna Abba
  • Iran Za ta Kauracewa taron fasalta kasashen da za su halarci  gasar cin kofin duniya na shekara ta 2026
  • Asibitin Kula Da Masu Lalurar Ƙwaƙwalwa Na Kaduna Na Bunƙasa Ta Fannoni Daban-Daban
  • Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali