Daga Aliyu Muraki

Hukumar Ilimi Matakin Farko ta Jihar Nasarawa (NSUBEB) ta yi barazanar kamawa tare da gurfanar da iyayen da  ‘ya’yansu ba sa zuwa makaranta a jihar.

Shugaban Hukumar, Dr. Kasim Mohammed Kasim ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a matsayin wani bangare na ayyukan babban  taron inganta ilimi da hukumar ta shirya.

Dr. Kasim Mohammed Kasim ya ce, ilimin boko matakin farko haƙƙin kowanne yaro ne, ba gata ba, kuma ya sha alwashin tabbatar da cewa ba a bar wani yaro a baya ba.

Shugaban Hukumar ya bayyana cewa hukumar ta yanke shawarar gudanar da gagarumin wayar da kan jama’a ta hanyar tarurrukan jin ra’ayoyin jama’a, da kafofin watsa labarai domin jaddada muhimmancin ilimin boko na a matakin farko ga kowane yaro a jihar.

Dr. Kasim Mohammed Kasim ya ce sun sayi motocin bas guda bakwai da za a gudanar da wayar da kan jama’a a dukkan sassan kananan hukumomi 13 na jihar, domin fadakar da iyaye  muhimmancin kai ‘ya’yansu makaranta.

Game da babban taron, Dr. Kasim Mohammed Kasim ya ce wannan taro zai hada manyan masu ruwa da tsaki ciki har da masana ilimi, jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, masu tsara manufofi, iyaye, malamai da sauransu.

Ya ce, mahalarta taron za su tattauna hanyoyin magance matsalolin ilimi, musayar kwarewa da sabbin dabaru domin kara inganta koyarwa da koyo a jihar.

Ya lissafo wasu daga cikin matsalolin da suka hada da ginin makarantu marasa inganci, karancin kujeru, karancin malamai, yawan rashin zuwa aiki daga ma’aikata, da rashin daidaitaccen tsarin tura malamai, da sauransu.

Ya ce hukumar ta maida malamai 1,900 wadanda a da ke aiki a ofis-ofis zuwa azuzuwa domin koyarwa, kuma nan ba da jimawa ba za a dauki sabbin malamai 1,000 domin cike gibi a makarantun jihar.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Gurfanar da Iyaye nasarawa

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun kashe tsohuwa, sun sace mutum 3 a Kano

’Yan bindiga sun harbe wata tsohuwa har lahira a wani sabon hari da suka kai ƙauyen Yankamaye da ke Ƙaramar Hukumar Tsanyawa a Jihar Kano.

Sun kai harin ne a daren ranar Asabar, a lokacin da mutanen ƙauyen ke kwance.

Likitoci sun gindaya sabon sharaɗi bayan janye yajin aiki Tinubu ya sake aike wa majalisa ƙarin sunayen jakadu 32

Yayin kai harin, ’yan bindigar sun kuma sace aƙalla mutum uku.

Yankamaye, wani ƙaramin ƙauyen manoma ne, ’yan bindiga da ke tserewa daga maƙwabtan jihohin Kano ne suka fara kai musu hare-hare.

Kakakin rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an tura jami’ai domin bin diddigin maharan.

Mazauna ƙauyen sun ce ’yan bindigar sun isa ne a kan babura inda suka ajiye su daga nesa, sannan suka shiga ƙauyen a ƙafa.

A yayin taron majalisar zartarwa da aka gudanar kwanan nan, Gwamna Abba Yusuf, ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na magance matsalar tsaro.

Ya kuma ce hare-haren ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da ɓarayi shanu a wasu yankunan Arewacin jihar, babban abin damuwa ne.

Gwamnan, ya ce suna aiki tare da hukumomin tsaro don magance barazanar da kuma tabbatar da zaman lafiya.

Ya bayyana ƙananan hukumomin da abin ya shafa; Kunchi, Tsanyawa, Gwarzo, Kabo, Sumaila, Shanono, Tudun Wada, Doguwa, da Rogo.

Amma ya ce hukumomi na ci gaba da ayyuka domin toshe hanyoyin shigowar ’yan bindiga da kuma kare al’ummomin ƙauyuka.

“Duk da wasu ƙalubale da ake fuskanta a nan da can, jama’a su kwantar da hankalinsu, gwamnati tana aiki domin magance duk wata barazana ga zaman lafiya,” in ji Yusuf.

Gwamnan, ya kuma goyi bayan matakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na ayyana dokar ta-ɓaci a harkar tsaro a faɗin ƙasar nan.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu ya naɗa Janar Christopher Musa sabon Ministan Tsaron Nijeriya
  • ’Yan ta’adda sun kashe ɗan sanda a gidan DPO a Jigawa
  • Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Gabatar Da Kasafin Kudin 2026 Na Kimanin Triliyan Daya
  • MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar
  • ’Yan sanda sun gano zinaren N23m bayan shekara 12 da ɓacewarsu a Borno
  • Gwamnatin Kano Ta Kara Jaddada Dokar Haramcin Yin Haya da Babur a Jihar
  • Jihar Jigawa Ta Mayar da Rarar Kudi Sama da Naira Miliyan 50 Ga Maniyyatan Aikin Hajjin 2026
  • Mutum 6 sun jikkata a rikici manoma da makiyaya a Jigawa
  • ’Yan bindiga sun kashe tsohuwa, sun sace mutum 3 a Kano