2025-09-18@13:16:17 GMT
إجمالي نتائج البحث: 437

«Iran da Rasha»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu zai yi magana ne a kan Aya. Shahid Mttahari, shahidi na farko daga cikin malamai jagororin juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran a shekara 1979. A jiya Jumma ce 2 ga watan Mayu na wannan shekara ta 2025 aka yi juyayin shahadar malami na fadrko wanda ya kai ga shahada bayan nasaral juyin juya halin musulunci a nan iran. Aya. Murtadha Muttahari, malami marubuci sannan jagora mai farkar da mutane a Iran da sauran kasashen duniya ta hanyar alkalaminsa da kuma jawabansa na shekaru masu yawa. Kafin juyin juya halin musulunci a nan Iran shekaru 46 da suka gabata, Aya, Muttahari ya zama fitilla ga mutane da dama a nan kasar...
    Bishop Joseph Osifuwa, Bishop na jihar Kwara, ya ce Nijeriya za ta iya magance matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a sassan kasar nan idan har ta dauki matakin magance masu tada kayar baya.   Bishop Osifuwa ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen babban taron cocin karo na 35 a Ilorin.   A cewarsa, magance rashin tsaro bai kamata ya zama matsala ga kasar da ta hada karfi da karfe a ayyukan wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa domin murkushe ‘yan tawaye ba.   Ya kuma shawarci gwamnati da kada ta rinka yi masu tada kayar baya ta hanyar yi musu afuwa, ya kara da cewa kada gwamnati ta tausayawa...
    Layukan dogo na kasar Sin sun gudanar da sufurin kusan fasinjoji miliyan 23.12 a jiya Alhamis, ranar farko ta bikin ranar ‘yan kwadago ta duniya da aka saba yi duk shekara a watan Mayu, kamar yadda kamfanin sufurin layin dogo na kasar Sin ya bayyana.   A cewar alkaluman da kamfanin ya fitar a yau Jumma’a, wannan adadi ya nuna karuwar kashi 11.7 cikin dari na adadin da ake samu a mizanin shekara-shekara. (Abdulrazaq Yahuza Jere)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen gina jihar da ma’aikata za su bunkasa, samar da ayyukan yi masu nagarta, da baiwa kowane bangare damar bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban jihar.   Gwamna AbdulRazaq a cikin sakonsa na bikin ranar ma’aikata ta duniya na shekarar 2025, a Ilorin, ya mika sakon gaisuwa ga maza da mata da jama’a da kungiyoyi masu zaman kansu wadanda kokarinsu ke karfafa tattalin arziki da samar da makomar al’ummarmu.   Ya yaba da gagarumar gudunmawar da ma’aikata ke bayarwa a kowane fanni na sadaukarwa, juriya, da fasaha wanda ya sa su zama ginshiƙan girma da ci gaba.   Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatin na aiwatar da manufofin da...
    Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa, duba mara lafiya guda daya tak da ke dauke da cutar Maleriyar da ba ta yi karfi sosai ba a asibitin gwamnati, na lashe kimanin Naira 17,000, tsakanin ganin likita, yin gwaje-gwaje da kuma magunguna.   Wadannan kudade sun kai kimanin Naira tiriliyan 1.156 da ake kashewa a kan wannan cuta, amma asalin kudaden sun zarta haka, musamman idan Maleriyar ta yi kamari, za a iya kashe ninki uku ko sama da haka na wannan kudi.   Yayin da duniya ke yin wannan biki na ranar Maleriya, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta nanata cewa, cutar na ci gaba da zama barazana, musamman a yankuna masu fama da zafi, duk da cewa; cuta ce da...
    Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya? Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu girma da tsayi. Hakan ya sa hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila suka kafa dokar ta baci tare da neman taimakon kasashen duniya. Yayin da Ministan tsaron cikin gidan Isra’ila Itamar Ben-Gvir yake neman dora wa Falasdinawa, alhakin tashin gobarar. Gobarar ta kunno kai ne a daidai lokacin da yahudawan sahayoniyya suka fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 77 da kafuwar gwamnatinsu ta mamaya a kasar Falasdinawa,...
    Gwamnatin Amurka da kuma kasar Ukraine daga karshe sun rattaba hannu kan yarjeniyar hakar ma’adinai masu karanci na kasar Ukraine, don bawa kasar damar biyan basussukan da Amurka ta ke binta sanadiyyar yakin da take fafatawa da kasar Rasha fiye da shekaru 3 da suka gabata. Jaridar ‘The Nation” ta kasar Amurka ta kara dacewa yawan kudaden da Amurka ta tallafawa Ukraine a yakin dai ya kai dalar Amurka biliyon $175, kuma wannan ita ce hanya tilo wacce Ukraine zata iya biyan wadannan basussuka. Labarin ya kara da cewa a jiya Laraba ce kasashen biyu suka rattaba hannu a kan yarjeniyar. Wannan na faruwa ne al-hali ana ci gaba da yaki tsakanin Rasha da Ukraine. Wannan yarjeniyar dai ta tabbatarwa...
    Gwamnatin Nijeriya ta ayyana gobe Alhamis 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan ƙasar albarkacin bikin murnar Ranar Ma’aikata ta Duniya. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Ministan Harkokin Cikin Gida na ƙasar, Olubunmi Tunji-Ojo, ya fitar a yammacin wannan Larabar. AU ta janye takunkumin da ta ƙaƙaba wa Gabon Tsoffin ma’aikatan NECO na neman a biya su bashin haƙƙoƙinsu Sanarwar ta ambato ministan yana yaba wa ma’aikatan ƙasar kan sadaukarwa da jajircewar da suke yi wajen gudanar da ayyukansu. Ministan ya kuma yaba musu kan gudunmawar da suke bayarwa wajen ciyar da Nijeriya gaba. Ana dai gudanar da bikin Ranar Ma’aikata a ranar 1 ga watan Mayun kowace shekara a sassan duniya.
    Kakakin ma’aikatar sharia a nan JMI ya bada sanarwan cewa,ma’aikatar za ta bayyanawa mutanen sakamakon bincken da suka gudanar kuma suke ci gaba da yi, dangane da fashewa da kuma gobatar da ta tashi a tashar jiragen ruwa ta Shahid Rajaee a cikin yan kwanakin da suka gabata. . Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran, ya bayyana cewa, Asgar Jahangir  kakakin ma’aikatar sharia da kuma Zabihullah Khudayiyan shugaban hukumar bincike ta kasa, sun gudanar da taron hadin guiwa da yan jaridu da kafafen yada labarai na cikin gida da waje a safiyar, dangane da fashewa da kuma gobarar da ta biyo baya a tashar jiragen ruwa na Shahid Rajaee. Banda haka jami’an sun amsa tambayoyin yan jarida bayan jawabansu...
    Kakakin kwamitin tsaron kasa a majalisar shawarar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; ” Ya zuwa yanzu ba za mu iya yin hukunci akan dalilan da su ka haddasa fashewar abubuwa a tashar ruwa ta Shahid Raja’i ba, amma za mu iya cewa babu hannu waje a ciki. Kakakin kwamitin tsaron kasar ta Iran Ibrahim Rizai wanda ya halarci taron da aka yi a Majalisa akan fashewar da aka samu a tashar ruwan ta shahid Raja’i, ya kuma kara da cewa; Fahimtata da abinda na ji daga abokan aikina dangane da abinda ya faru a tashar ruwa ta Shahid Raja’i, da kuma rahotannin da su ka iso mana, shi ne cewa abinda ya farun ba shi da alaka da waje.”...
    Shugaban Putin Na Rasha Ya Bada Sanarwan Tsagaita Wuta Da Ukraine Na Bangaren Guda kuma na sa’o’ii 72 ko kwanaki 3, daga 8-10 na watan Mayu mai zuwa. Jaridar Daily Trust ta Najeriya nakalto jakadan kasar Rasha a Abuja yana fadar haka a wani taro baje kolin hotinan yaki Rasah da Nazi a dai dai lokacinda kasar take cikar shekaru 80 da samun nasara a kan sojojin Nazi a karshen yakin duniya na II a Abuja. Andrey Podelyshev yace idan kasar Ukraine ta zami da tsagaita wuta a cikin wadannan kwanaki ba laifi, amma kuma idan sojojinta sun kai wani hari a kan rasha ta zata rama da hare-hare masu tsanani. Shugaban Volodimir Zelesky dai tuni ya yi watsi da...
    Fadar Kremlin ta kasar Rasha ta ayyana tsagaita wuta na kwana biyu ita kaɗai a yakinta da kasar Ukraine. Shugaba Vladimir Putin ya sanar a ranar Litinin cewa Rasha za ta aiwatar da tsagaita wutar ne daga tsakar dare na 8 ga Mayu zuwa tsakar dare na 10 ga Mayu. A ranakun da za a tsagaita wutar ne Rasha ke bikin karshen da yakinta da kasar Jamus a shekarun 1941 zuwa 1945, wanda aka fi sani da Yakin Duniya na Biyu a yawancin duniya. A Rasha ana kiran yakin na Duniya na biyu da sunan Babban Yaƙin Ceton Kasa. Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi Dukan farar hula saboda sanya kayan sojoji laifi...
    A cewarsa, tuni aka shirya wuraren kwana da abinci ga maniyyatan a kasar Saudiyya.   Abdulkadir ya tabbatar da cewa, ana shirye-shirye, inda za a yi alluran rigakafi a ranar 28 ga Afrilu, za a raba tufafi a 30 ga Afrilu, sannan kuma za a raba jakunkuna a ranar 1 ga Mayu.   Ya kara da cewa maniyyatan da suka biya sama da Naira miliyan 8.4 na kudin aikin Hajji, za a biya su bayan sun dawo daga Saudiyya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
    Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae, a karon farko da yayi magana dangane da fashewar tashar jiragen ruwa na Shahida Rajae ya gabatar da Ta’ziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu ko suka jikata a wannan hatsarin. Ya kuma bukaci a gudanar da bincike mai mai zurfi don gano musabbabin fashewar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jagoran yana bada umurni ga ma’aikatar shari’aa a kasar ta gudanar da cikekken bincike don sanin abinda ya faru saboda daukar matakan da suka dace don hana irin wannan sake faruwa nan gaba, sannan idan akwai wadanda suka yi kuskure a hukunta su. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa gobarar da ta taso...
    Mataimakin ministan harkokin waje mai kula da bangaren siyasa, ya bayyana cewa; Ko kadan ba a bijiro da batun dakatar da tace sanadarin uranium a Iran ba, ko kuma batun makamanta masu linzami. Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya tabbatar da cewa, wadannan abubuwan biyu wato dakatar da ci gaba da tace sanadarin uranium da kuma makamai masu linzami, jan layi ne da jamhuriyar musulunci ta Iran ba za ta bari a ketara su ba ba kuma za ta bari a bude tattaunawa akansu ba. Kwamitin da yake kula da tsaron kasa da kuma siyasar waje a majalisar shawarar musulunci ta Iran a karkashin jagorancin dan majalisar Ibrahim Ridhazi ya yi taro a ranar Lahadin da ta gabata, inda...
    Ministan kiwon lafiya na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Ridha Zafarqandi ya tattauna hanyoyin bunkasa aiki tare a fagen kiwon lafiya da mataimakin ministan kiwon lafiya na tarayyar  kasar Rasha. Ministan na Iran dai ya yi wannan trattaunar ne a jiya Lahadi inda su ka tabo fagage da dama da su ka yi tarayya akansu a cikin harkar kiwon lafiya. Ministan na Iran ya kuma ce, a baya kasashen biyu sun cimma yarjejeniya wacce a wannan lokacin ake son bunkasa ta. Muhammmad Ridha Ya kuma bayyana yadda kasashen biyu suke da kayan aiki masu yawa a fagagen magance cutuka masu yaduwa da wdanda ba su yaduwa haka nan kuma fagen yin magunguna. Shi kuwa mataimakin ministan kiwon lafiyar na tarayyar...
    Ministan harkokin cikin gidan Iran Askandar Mumini wanda ya kai Ziyara zuwa wurin da gobarar ta tashi ya sanar da cewa adadin wadanda su ka jikkata sun kai 750 da kuma wadanda su ka rasa rayukansu zuwa 14. Sai dai kuma daga baya ma’aikatar shari’a ta kasar Iran din ta ta sanar da karuwar wadanda su ka kwanta dama zuwa 21 Mai shigar da kara na gundumar Hurzumgan, Mujtaba Kahraman ya sanar da cewa; Daya daga cikin aikin da suke yi shi ne tantance wadanda su ka su ka rasa rayukansu. Haka nan kuma ya kara da cewa; Ya zuwa yanzu sun tabbatar da mutuwar mutane 21. Har ila yau ya bayyana cewa bayan tantance gawawwakin wadanda su ka rasa...
    Daruruwan mutane ne suka jikkata sakamakon fashewar wani abu mai karfi a tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke kudancin kasar Iran Wata babbar fashewa, wacce ba a taba jin irin ta ba, ta afku da yammacin ranar Asabar a yankin tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke Bandar Abbas, a kudancin kasar Iran, wanda ya yi sanadiyyar jikkata daruruwan mutane a rahotonnin da ake da su a hannu har zuwa yanzu. A cikin wani sabon rahoton da aka samu kan adadin mutanen da suka jikkata sakamakon fashewar tashar jiragen ruwa ta Shahid Raja’e, kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ya ce: Adadin wadanda suka jikkata ya kai 516 ya zuwa yanzu. Fashewar ta yi karfi...
    Daruruwan mutane ne suka jikkata sakamakon fashewar wani abu mai karfi a tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke kudancin kasar Iran Wata babbar fashewa, wacce ba a taba jin irin ta ba, ta afku da yammacin ranar Asabar a yankin tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke Bandar Abbas, a kudancin kasar Iran, wanda ya yi sanadiyyar jikkata daruruwan mutane a rahotonnin da ake da su a hannu har zuwa yanzu. A cikin wani sabon rahoton da aka samu kan adadin mutanen da suka jikkata sakamakon fashewar tashar jiragen ruwa ta Shahid Raja’e, kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ya ce: Adadin wadanda suka jikkata ya kai 516 ya zuwa yanzu. Fashewar ta yi karfi...
    Kasar Rasha ta fara tura iskar gasa zuwa kasar Iran ta kasar Azarbaijan, wanda daga karshe zai shiga kasuwan ga kasar ta rasah. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto gwamnatin kasar ta na fadar haka a yau Asabar. Labarin ya kara da cewa tun taron kwamin hadin guiwa na kasuwanci da tattalin arziki na kasashen biyu ya gudanar da taronsa na hadin guiwa karo na 18 a birnin Mosco, Rasha ta bada sanarwan fara tura iskar gas zuwa kasar ta Iran ta kasar Azirbajan, wanda kuma hakan zai zama kasuwa ga kasar Rasha amma a kasar Iran.. Kasashen biyu dai sun dade suna kokarin karfafa dangantaka a tsakaninsu, musamman bayan da kasashen yamma suka dora masu takunkuman...
    “Rashin samar da daidaito a hada-ahadar kasuwanci, ya kasance abinda ya sanya Hukumar ta NPA ke cazar kudaden gudanar da aiki da yawa,” Inji Dantsoho.   Dantsoho wanda Janar Manaja na sashen hudda da jama’a da gudanar da tsare-tsare na Hukumar NPA Miista Seyi Iyawe Akinyemi ya wakilce shi a wajen taron, ya ce, NPA ta bai wa kamfanini biyar Lasisi a jihar Legas, bisa kokarin da take yi, na bunkasa fitar da kaya zuwa waje ta hanyar amfani da Tashoshin ta.   Sai dai, ya sanar da cewa, Hukumar na duba yuwuwar samar da rangwamen cazar kudaden, musamman domin ta kara inganta ayyukanta.   Ya yi nuni da cewa, Tashoshin Jiragen Ruwa waje ne da ke taimaka wa wajen...
    An sako limamin cocin Katolika, Rabaran Fada Ibrahim Amos wanda ’yan bindiga suka sace a ranar Alhamis da rana a Kurmin Risga da ke Ƙaramar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna. Fada Amos, wanda ke aiki a Cocin St. Gerald Ƙuasi Parish ya dawo gida lafiya lau ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 2 na tsakar dare, kwana ɗaya bayan sace shi. An kama mutum 2 ɗauke da ƙwayar tramadol ta N150m a Kano Mahaifi ya kashe ɗansa mai shekara 6 don yin tsafi a Gombe Bayani kan sakin nasa na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban Cocin Diocese na Kafanchan, Rabaran Fada, Dakta Jacob Shanet ya fitar, inda ya gode wa Allah tare da nuna godiya ga...
    Sashin ma’adinai da ba na karfe ba ta kashe kudin makamashi da kashi 33.7 zuwa naira biliyan 118.49, kuma masana’antar yadi, tufafi da takalmi kudin da ya kashe ya karu sau hudu, wanda ya kai naira biliyan 26.45 a shekarar 2024, idan aka kwatanta da naira biliyan 6.97 a shekarar 2023.   Rahoton ya ce duk da an samu karin wutar lantarki a cikin masana’antu a shekarar 2024, da adadin karin wuta na awa 13.3 a kwace ranar da ya karu daga awa 10.6 a shekarar 2023.   Kazalika karin kudin wuta ya karu da kaso 200 ga wadanda suke amfani da rukunin A, don haka kudaden da masana’antun ke kashewa wajen biyan kudin wuta nan ma ya karu sosai....
    “Saboda ragin farashin litar man fetur da Dangote ya yi ne. Gidan man yana da tsohon mai da ya saya a farashin da ya fi wannan, kuma ba zai sayar da shi a asara ba.   “Wannan dalilin ne ya sanya muka rufe gidajen man tun ranar Talata. Da yiwuwar mu bude nan gaba.”   Kazalika, wani ma’aikacin gidan man, ya tabbatar da cewa suna ‘yan wasu gyare-gyare ne amma za su sake budewa. Ya kuma ce, gidan man zai fara sayar da man fetur ga jama’a a ranar Talata kan kudi naira 910 a kowace lita.   Rahotonni sun tabbatar da cewa sauran abokan huldar matatar man Dangote, kamar su AP, Ardoba, da Optima, sun yi ta sayar wa...
    Gwamnatin kasar Amurka ta gargadi kasar Ukraine a dai dai lokacinda ta gabatar da shirin zaman lafiya da kasar Rasha na karshe. Shirin da shugaban kasar Donal Trump ya bayyana shi ne karshe dai, ya bukaci gwamnatin shugaba Volodimir Zelesky ta amince da yankin Cremea da kuma sauran yankunan hudu wadanda Rasha ta mamaye da karfi shekaru uku da suka gabata su zama mallakin kasar Rasha har’ abada. Sannan ta amince a daukewa kasar Rasha takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata tun bayan fara yakin. Sannan daga karshe ta amince ba zata shiga kungiyar tsaro ta NATO ba. Shawara bata yi maganar wani abu banada wadannan hudu ba, duk da cewa Ukraine tana da wasu bukatu a yarjeniyar tsagaita...
    Raguwar kudin a hannun mutane na iya zama wani bangare na kokarin rage matsin lamba kan hauhawar farashin kayayyaki da samun daidaiton tattalin arziki.   Baya ga raguwar kudade a hannun mutane, ajiyar a bankin CBN ya karu zuwa naira biliyan 28.52 a watan Maris na 2025, daga naira biliyan 27.57 a watan Fabrairun 2025. A watan Janairun 2025, ajiyar ya kai naira biliyan 27.43.   A halin yanzu, ajiyar ko-ta kwana ba ta canza ba a naira miliyan 284.36 a cikin watanni uku.   Ajiyar banki yana nufin kudaden da Babban Bankin da bankunan kasuwanci ke rike da shi don tabbatar da hada-hadar kudade a cikin bangaren banki. Ci gaba da karuwar ajiyar bankuna wata alama ce ta kokarin...
    “Aisha ba wai mawaƙiyar amshi ba ce kawai a wajen Rarara ba. Sun yi matuƙar shaƙuwa da juna, kuma mu da muka san su ba abin mamaki ba ne don an ce za a yi wannan aure,” in ji majiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jinjinawa kasashen Sin da Rasha a matsayin abokan hulda na kut-da-kut da kasar, yayin da ya isa birnin Beijing domin yin shawarwari da manyan jami’an kasar Sin, gabanin yin tattaunawa zagaye ta uku da Amurka kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Abbas Araghchi ya shaida wa kafar yada labaran Iran a babban birnin kasar Sin a ranar Laraba cewa, “Sin da Rasha abokan hulda ne na kut da kut da suka tsaya tare da mu a lokutan wahala, don yana da kyau da ma’ana mu ci gaba da tuntubar juna tare da su a bangarori daban-daban, musamman ma yanzu da ake tattaunawa da Amurka.” “Ya zama dole mu sanar da abokanmu a kasar...
    Matsalar tsaro ta kara tabarbare a jihohin Filato da Benuwai, inda rahotanni ke cewa, wasu da ake zargin makiyaya ne daga kasashen waje ne ke kai hare-haren kashe rayuka da kuma raba al’umma da matsugunansu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Bugu da kari, kasar ta samar da cibiyoyin kula da lafiyar mata da kananan yara 3,081, baya ga likitocin yara da na mata a fadin kasar da yawansu ya kai 373,000. Kana fiye da kashi 90 cikin dari na cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a yanzu sun mallaki kayan aiki da sassan kula da lafiyar yara masu inganci.   Ba a cikin kasarta kawai take kokarin inganta kiwon lafiyar mata da kananan yara ba, har ma da kasashen duniya, domin kwararrun likitocin Sin da aka tura don ba da agaji a kasashen waje sun gudanar da ayyukan kula da lafiyar mata da yara a kasashe da yankuna 44, ciki har da wasu kasashen Afirka. A cikin 2024 kadai, tawagogin...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: China da Rasha abokan hulda ne na tushe ga Iran bisa kyakkyawan tsari Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana kasashen China da Rasha a matsayin abokan huldar na tsari a kan tubalin manyan tsare-tsare ga Iran, kuma ya dace kasashen uku su ci gaba da tuntubar juna a fannoni daban daban. A yayin da ya isa birnin Beijing, yayin da yake amsa tambaya game da makasudin ziyararsa a kasar China a jajibirin shawarwarin da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, Araqchi ya bayyana cewa: Kasashen China da Rasha abokan hulda ne na kut-da-kut da Iran. Sun kasance tare da Iran a lokutan wahala, kuma abu ne mai...
    Majiyar fadar Vatican ta bada sanarwan cewa za’a gudanar da jana’izar paparuma Francis a ranar Asabar mai zuwa 26 ga watan Afrilu a dandalin st. Peter dake birnin Vatican amma za’a ajiye gawarsa don yi mata kallo na karshe a daga gobe Laraba a St. Peter’s Basilica har zuwa ranar Jana’izar. Shafin yanar gizo na labarai “Africa News” ya bayyana cewa paparoma Francis ya mutane a ranar 20 ga watan Afrilu yana dan shekara 88 a duniya, kuma fatansa a cikin jama’a da kuma jawabinda na karshe kwana guda ne kafin rasuwarsa. Labarin ya kara da cewa paparoman ya shahara da son talaka, da kuma wadanda aka zalunta, musamman al-ummar Falasdinu, wadanda yahudawan HKI suke yiwa kissan Gila tun sdhekara...
      Iyalan Alhaji Surajo Ilyasu Malumfashi (RADIO NIGERIA KADUNA) dana Alhaji Idris Ahmed Accama na farin cikin sanar da bikin aure na ‘ya’yansu, Muhammad Auwal Idris da Zainab Surajo Malumfashi. Za’a gudanar da bikin auren ranar Asabar, 3 ga Mayu, 2025, a Masallacin Juma’a na Dan Fodio, Dake Anguwan Sunusi, Jihar Kaduna. Za a daura auren da misalin karfe 11:00 na safe, sannan ana sa ran ci gaba da liyafa kai tsaye bayan kammala daurin auren. Iyalan suna gayyatar dangi, abokan arziki da duk masu fatan alkhairi su halarta tare da murnar wannan babban biki, wanda ke nuna sabon babi a rayuwar amarya da ango. Surajo Ilyasu Malumfashi
    Wasu shugabannin duniya da suka bayyana niyyarsu ta halartar jana’izar sun haɗa da Donald Trump na Amurka, Emmanuel Macron na Faransa, Luiz Inacio Lula da Silva na Brazil, da Volodymyr Zelensky na Ukraine. Ana sa ran jana’izar za ta samu halartar manyan baƙi daga sassan duniya, tare da girmama rayuwar Fafaroma Francis da ayyukansa da ya yi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jamuhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada matsayinta kan batun tace sinadarin yuraniyo. Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatemeh Mohajerani ta bayyana cewa, Iran na kokarin yin shawarwari ne domin samar da amana da samar da gaskiya game da shirinta na nukiliya domin dage takunkumi kanta. A cikin taron manema labarai na mako-mako da ta gudanar a jiya litinin, Mohajerani ta mayar da martani ga wata tambaya game da tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka, inda ta ce, shin bangarorin biyu sun cimma matsaya dangane da kasar da za a aike da hajojin uranium da Iran ta inganta? Shin Iran ta amince ta mika wadannan haja zuwa Rasha? Ta ce: Ina so in bayyana dangane da kashi na...
    A yau Litinin shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya fitar da sanarwa ta nuna aljinin rasuwar Papa Roma Farancis,sannan kuma ya mika sakon ta’aziyya ga Mabiya darikar Roman Katolika na duniya. Shugaban kasar ta Iran ya rubuta cewa; Daga cikin matsaya da ta kasance fitacciya wacce Papa Roman ya dauka a lokacin rayuwarsa ita ce ta kalubalantar yadda ake take hakkin bil’adama a duniya, musamman mai dai yadda ya yi Allawadai da kisan kiyashin da ‘yan sahayoniya suke yi wa Falasdinawa a Gaza. Haka nan kuma yadda ya rika yin kira da HKI ta kawo karshen kisan kiyashin da take yi, da kashe mata da kananan yara. Fizishkiyan ya kuma kara da cewa; Wadannan matakan da Papa Roman ya dauka...
    Fadar Vatican ta sanar da mutuwar shugaban majami’ar katolika na duniya, Fafaroma Francis yana da shekaru 88 a duniya. A shekarar 2023 ne cocin ya zaɓi Fafaroman, wanda asalin sunansa shi ne Cardinal Jorge Mario Bergoglio a matsayin wanda zai jagorance ta, bayan saukar Fafaroma Benedict XVI daga kan muƙamin. Da safiyar Litinin ne ɗaya daga cikin jagororin cocin ya sanar cikin jimami game da rasuwar ta Fafaroma Fraincis, inda ya ce: “Ya ku ƴan’uwana, cikin alhini, ina sanar da ku game da rasuwar Babanmu a addini, Francis. Da misalin ƙarfe 7:35 na wannan safiya (Agogon Vatican), Bishop ɗin Roma, Francis ya koma ga mahalicci. Ya sadaukar da rayuwarsa baki ɗaya wajen bauta wa ubangiji da kuma coci.” “Ya koya...
    Ana zargin wani ɗan kasar Indiya mai shekara 20 da tserewa da surukarsa mai shekara 40, kwanaki tara kacal kafin aurensa da ’yarta. Ma’auratan Rahul da Shibani, matasa ne ’yan Aligarh, a Jihar Uttar Pradesh ta Indiya, wadanda suka shirya yin aure a ranar 16 ga Afrilu na watan da muke ciki. Zaɓen 2027: Babu ɗan takarar da zai yi nasara ba tare da goyon bayan Arewa ba — Hakeem NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye cikin littafai ana shirin kaiwa Saudiyya An aika wa dangi katin gayyata domin halartar taron bikin, amma kwanaki tara kafin ranar bikin, sai wani iftila’i ya afku. Angon dan shekara 20 ya lallaba ya bace, amma bai tafi shi kadai ba; ya...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi watsi da barazanar HKI na kaiwa cibiyoyin makamashin nukliyar kasar don hana kasar abinda take kira makaman Nukliya. Ministan ya kara da cewa kasar Iran zata iya kare kanta ko da Amurka ce ta takaleta, kuma Amurka ta san hakan. Sannan ya ce HKI bata taba kaiwa Iran hari a bay aba kuma ba zata taba kai mata hari ba. Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya buga wannan labarin a jiya Asabar ya kuma nakalto ministan yana cewa kasashen Rasha da Iran basu taba karfafa dangantakar tsakaninsu fiye da yanzu ba. Aragchi ya kara da cewa kasashen Iran Rasha da kuma China suna aiki tare don tabbatar da zaman...
    Gwamnatin Rasha ta sanar da amincewarta da tsagaita bude wuta da Ukraine a wannan karo Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar da tsagaita bude wuta na kwanaki uku na Ista, inda ya yi kira ga sojojin kasarsa da su kasance cikin shirin ko ta kwana idan Ukraine ta karya yarjejeniyar. Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ba da sanarwar tsagaita wuta na kwanaki uku na Ista, yana mai kira ga sojojin kasarsa da su “ci gaba da kasancewa cikin shiri don yiwuwar keta yarjejeniyar tsagaita wutan daga bangaren Ukraine, a sanarwar da fadar Kremlin na fitar. Putin ya fada a ranar Asabar cewa: “Tsarin tsagaita bude wuta zai nuna a fili gwamnatin Ukraine tana da ikon warware matsalar cikin lumana.”...
    Shugaba Vladimir Putin a yau Asabar ya umarci sojojin Rasha da su tsagaita buɗe wuta a Ukraine a wanan ranar ta Ista da kuma gobe Lahadi. Putin ya kuma yi kira ga Kyiv da ta yi hakan, yayin da ake ganin tattaunawar tsagaita buɗe wuta ta ci tura. Kada Kanawa su bari rigingimun siyasa su hana su zaman lafiya — Shettima Shin Mataimakin Gwamnan Bauchi ya ‘mari’ Ministan Tinubu? Haka kuma, Rasha da Ukraine sun yi musayar fursunonin yaƙi na sama da mutum 500 — kuma mafi girma tun bayan fara yaƙi a tsakanin kasashen biyu. Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskiy, ya ce ƙasarsa ta karɓi sojoji fursunonin yaƙi akalla 277 waɗanda ke tsare a gidajen yarin Rasha, kamar yadda ya...
    An fara gudanar da bukukuwan ranar soji a Iran a ranar 18 ga watan Afrilu ta hanyar gudanar da faretin soja a gaban shugaban kasar Mas’ud Pezeshkian An fara faretin soji na sojojin kasar Iran a kusa da hubbaren Imam Khumaini (r.a) da ke kudancin birnin Tehran fadar mulkin kasar a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan ranar sojoji ta 18 ga watan Afrilu. A jiya Juma’a 18 ga watan Afrilu ne sojojin kasar Iran suka fara faretin soji na murnar zagayowar ranarsu da kuma irin bajintar jarumtakar sojojin kasar, a kusa da hubbaren Imam Khumaini (r.a) da ke kudancin  babban birnin kasar Tehran. A cewar kamfanin dillancin labaran IRNA na Iran, faretin ya samu halartar shugaban kasar Mas’ud...
    Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bukaci Kiristoci da su yi tunani a kan darussa, muhimmaci, da kuma kyawawan dabi’u na makon Easter.   Gwamna AbdulRazaq a wani sako da ya aike a Ilorin, ya taya mabiya addinin kirista a jihar da ma fadin Najeriya murnar bikin Easter.   Gwamnan ya ce nasarar da Yesu Kiristi ya samu a fuskantar wahala, wanda bikin Ista ke alamta, ya kamata ya fitar da imani ga Allah da kuma yuwuwar da ba su da iyaka da ke zuwa tare da samun bangaskiya mara girgiza cikin ikonsa.   Ya yi addu’ar Allah ya sa lokacin Easter ya kawo farin ciki da jin daɗi mara iyaka ga kowane gida a jihar da kuma bayansa  ...
    Kasar Chaina ta musanta zargin shugaban kasar Ukraine ga kasar, dangane da tallafawa kasar Rasha da makamai. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar wajen kasar China Lin Jian yana fadar haka a safiyar yau Jumma’a ya kuma kara da cewa, kasar China bata taba daukar bangaren a yakin na Ukraine ba, kuma ra’ayinta shi ne shiga tsakanin don kawo karshen yakin. Kafin haka dai shugaban kasar Ukraine Volodimir Zelesky ya zargi gwamnatin kasar China da tallafawa kasar Rasha da makamai a yakin da kasarsa take fafatawa da ita. Zelesky ya ce a wannan karon kasar China ta aikawa Rasha makaman Atilari da kuma PorwerGun. A can baya ma gwamnatin kasar ta Ukraine ta zargi kasar...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya mika rubutacciyar wasikar jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ga shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. Araghchi, wanda ya je birnin Moscow a matsayin shugaban tawagar diflomasiyya don ganawa da wasu manyan jami’an Rasha, ya gana da Putin a yammacin ranar Alhamis. Ministan ya gabatar da sakon Jagoran ga shugaban kasar Rasha tare da bayyana ra’ayoyi da matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da batutuwan da suka shafi ajandar huldar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma ci gaban yanki da sauran batutuwa na kasa da kasa. Araghchi ya tabo yarjejjeniyar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare da shugaba Putin da takwaransa na Iran, Masoud Pezeshkian suka rattabawa hannu a birnin Moscow a...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Sakon jagora ga shugaban kasar Rasha yana da alaka da ci gaban kasa da kasa da na yanki Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana hakan ne a yau Alhamis a birnin Moscow na kasar Rasha cewa: Abu ne da ya dace a rubuta sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aikewa shugaban kasar Rasha dangane da ci gaban kasa da kasa da na yanki da kuma batutuwan da suka shafi kasashen biyu. Araqchi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya isa filin tashi da saukar jiragen sama na Vnukovo da ke birnin Moscow a yau, yayin da yake amsa tambayar da wakilin IRNA ya yi masa kan...
    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Hind Rajab ta yi kira ga Birtaniya da ta kama ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Hind Rajab ta gabatar da bukatar fitar da sammacin kame ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar da yake ziyara a Birtaniya. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa: Cibiyar Hind Rajab Foundation da ta mayar da hankali kan neman gurfanar da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da ake zargi da aikata laifukan yaki, ta mika bukatar kama Gideon Sa’ar a birnin Landan na Birtaniya. Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun jiyo ofishin ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila na cewa babu wata niyyar takaita ziyarar Sa’ar...
    Ministan Harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya je kasar Rasha a safiyar yau Alhamis don isar da sakon jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaei zuwa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan sakon na zuwa ne rana guda da amincewar majalisar dojojin kasar Rasha ta dangantaka ta musamman tsakanin kasashen biyu, mai tsawon shekaru 20. Har’ila yau da kuma kwanaki biyu kafin a gudanar da tattaunawa na biyu tsakanin Iran da Amurka dangane da shirin ta na makamashin Nukliya a birnin Roma na kasar Italiya. Masana dai sun bayyana cewa kasashen Rasha da Iran suna kara dankon zumunci a tsakaninsu ne a dai-dai lokacinda al-amura da dama...
    Majalisar kasa ta kasar Rasha ta amince da yarjeniyar dangantaka ta musamman tsakanin kasar da JMI a ranar 8 ga watan Afrilun da muke ciki sannan ana saran shugaban kasa Vladimir Putin zai sanyawa yarjeniyar hannu a nan gaba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa yarjeniyar ta musamman mai kuma dogon zango na shekaru 20 zai bawa kasashen biyu damar tallafawa juna da kuma aiki tare da bangarori daban-daban wadanda suka hada da tsaro makamashi kimiyya da fasaha da sauransu. Labarin ya kara da cewa idan yarjeniyar ya fara aiki kasashen biyu suna da damar kyautata dangantaka a tsakaninsu, wanda zai rage dogaro da suke yi da kasashen yamma a bangarori da dama. Dangantakar Tehran da...
    Hukumar UNICEF ta MDD mai kula da yara ta bada sanarwan cewa kimani yara 3,500 suka rasa rayukansu a kokarin ketara tekun Medeteranina a cikin shekaru 10 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran Spunic na kasar Rasha ya nakalto hukumar tana fadar haka a wani rahoton da ta fitar dangane da hakan. Labarin ya kara da cewa, wannan ya nuna cewa akalla yaro guda ne ya ransa ransa a ko wace rana. Kuma kashi 7/10 daga cikinsu sun halaka ko sun bace ne su kai ba ba tare da rakiyar iyayensu ba. Har’ila yau rahoton ya kara da cewa akalla mutane 20,803 suka halaka a tsakiyar tekun na Mediterranean a kokarinsu na tsallakawa zuwa kasashen na turai. Daga karshe hukumar...
    Rasha ta ce tana ta na sa ido sosai game da tattaunawa karo na biyu tsakanin Amurka da Iran kuma a shirye take ta taimaka wajen warware shirin nukiliyar Iran ta hanyar siyasa da diflomasiyya. Makomar shirin nukiliyar Iran da kuma zaman lafiyar yankin na iya danganta ne kan ko Washington da Tehran za su koma kan teburin shawarwari. Yayin da tattaunawar tsakanin Amurka da Iran ta tsaya cik a baya, manyan kasashen duniya musamman Rasha da China sun yi yunkurin ganin neman farfado da tattaunawar ta diflomasiyya. Tunda farko a makon da ya gabata Majalisar Tarayyar Rasha ta amince da yarjejeniyar hadin gwiwa ta tsawon shekaru 20 a hukumance da Iran, wanda ke karfafa kawancen dogon lokaci tsakanin kasashen...
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Neja ta kaddamar da rabon sutura da jakunkunan hannu masu nauyin kilo 8 ga maniyyatan bana, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen aikin Hajji na shekarar 2025. A lokacin da yake jawabi yayin kaddamar da rabon, Shugaban Hukumar, Sheikh Muhammad Awwal Aliyu, ya bayyana cewa rabon kayayyakin na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da sauƙin tafiya da kuma aikin Hajji ba tare da wata tangarda ba ga maniyyatan jihar. Shugaban wanda Daraktan Gudanarwa, Babani Aliyu Yahaya, ya wakilta a yayin bayar da kayan ga Jami’in Alhazai na Ƙaramar Hukumar Chanchaga, ya ce kayayyakin na maniyyatan  da suka kammala biyan kuɗin kujerunsu ne. Daraktan Gudanarwar ya kuma yi kira ga waɗanda har yanzu ba su...
    Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da yin luguden wuta kan zaman taron shugabannin sojojin Ukraine a birnin Sumy da ke arewa maso gabashin Ukraine Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa, ta kai hari kan wani ofishin rundunar sojojin Ukraine da ke dauke da makamai masu linzami na Iskander a yayin wani zaman taron manyan sojojin kasar a birnin Sumy, inda aka kashe jami’ai sama da 60. Ma’aikatar tsaron Rasha ta kara da cewa sojojin na Ukraine na ci gaba da amfani da fararen hula a matsayin garkuwa gare su, tare da kafa cibiyoyin soji da kuma shirya tarurruka tare da halartar sojoji a tsakiyar birni mai yawan jama’a, tare da yin nuni da cewa; Rasha ta kai harin...
    Al’ummar Babura sun shirya gagarumin taron girmamawa domin karrama Dr. Salisu Mu’azu, bayan nada shi a matsayin Daraktan kuma babban likitan asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ke jihar Jigawa, da kuma samun matsayin mamba na Cibiyar Kasa (mni). Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kwamitin Shirye-shirye, Rabiu Umar, ya bayyana cewa an gudanar da taron ne domin nuna godiya ga Allah da kuma murnar manyan nasarorin da Dr. Mu’azu ya samu. Ya yaba da kokarin Daraktan wajen gudanar da aikinsa da kwarewa, da kuma ci gaba da tallafa wa al’umma. A sakon da aka gabatar a madadin Mai Martaba Sarkin Ringim, Alhaji Dr. Sayyadi Abubakar Mahmoud, wanda Mai Girma Alhaji Usman Sayyadi, Babban Hakimin Masarautar, ya wakilta,...
    Majiyar Falasdinawa a Gaza sun bada labarin kissan wasu sojojin HKI  a unguwar Shuja’iyya kusa da Gaza a jiya Litini,  inda wasu kuma suka ji rauni. Kafafen yada labarai da yahudawan da kuma larabawa sun bayyana cewa kungiyar Jihadul Islami a Gaza ta ce nayakanta masu farautar yahudawa daga nesa sun bayyana cewa suk halaka wasu yahudawa wadanda suka boye a wani gida a garin Rafah kudancin Gaza, inda suke halakasu. Sannan a sauran wuraren kuma sojojin yahudawan da dama ne  suka ji rauni. Kuma sun ga jiragen yakin masu sauran ungulu na yahudawan sun zo sun tafi da wadanda abin ya shafa. Wannan dai kadan Kenan daga hare-haren maida martanin da dakarun falasdinawan suke mayarwa ga sojojin yahudawan, tun...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana alhininsa akan rasuwar Dr. Akbar I’itimadi wanda shi ne na farko da ya kafa hukumar makamashin Nukiliya ta Iran. Wasikar ta’aziyyar da shugaban kasa ta kunsa ta ambaci cewa:  Shakka babu hidima mai kima da wannan masanin ya yi, ya share fagen gina da ci gaban fasahar makamashin Nukiliya a Iran da kuma mayar da kasar mai cin gashin kanta a wannan fage. Har ila yau, shugaban kasar ta Iran ya mika sakon ta’aziyyarsa ga masana na Iran, da kuma iyalansa. Ya kuma yi addu’a da rokon Allah madaukin sarki da ya lullube shi da rahamarsa da kuma gafararsa, sannan ya bai wa iyalansa na hakuri.
    Labaran da suke fitowa daga kasar Ukraine sun bayyana cewa, gwamnatin kasar tana son karban iko da bututun iskar gas na kasar Rasha wanda yake yammacin kasar da Turai, wanda kuma yake kai iskar gasa zuwa kasashen Turai. An gina bututun tun zamanin tarayyar Soviet kuma kasashen biyu suna samun kudade masu yawa daga wannan bututun. Gwamnatin kasar Amurka dai tana son ta dawo da kudaden da ta kashewa kasar Ukraine na makamai wacce ta karba a likacin shugaban Biden. Daga cikin dai Amurka ta bukaci Ukraine ta bada ma’adinanta na kimani dalar Amurka biliyon $500. Wasu rahotanni sun bayyana cewa jami’an gwanatocin kasashen Amurka da Ukraine sun tattauna wannan batun a ranar jumma’an da ta gabata, don tattauna batun...
    Isra’ila ta ce ta karbe iko da wata muhimmiyar hanya a zirin Gaza a wani mataki da ya yanke gaba daya yankin kudancin Rafah mai yawan jama’a daga sauran yankunan Falasdinawa da aka yiwa kawanya. A cikin wata sanarwa da Isra’ila ta fitar yau Asabar ta ce dakarunta sun yi wa Rafah kawanya gaba daya tare da samar da “yankin tsaro” a can. Sanarwar da ministan harkokin soji na gwamnatin Isra’ila Katz ya fitar ta ce sojojin sun karbe ikon “Morag axis, wanda ke ratsa Gaza tsakanin Rafah da Khan Yunis.” Katz ya kuma yi kira ga Falasdinawa da su fara kaura zuwa yamma, yana mai gargadin cewa nan ba da jimawa ba za a kara kaimi da fadada ayyukan...
    Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da dokar albashi na naira 70,000 a ranar 29 ga watan Yuli na 2024, bayan shafe watanni ana muhawara da kungiyoyin kwadago. Sabon mafi karancin albashin na wata-wata ya karu da kaso 133 daga naira 30,000 zuwa naira 70,000, sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar nan. Da yake ba da bayani kan halin da ake ciki, shugaban kungiyar NULGE ya ce, “A zahirin gaskiya muna fuskantar matsaloli da jihohi da dama, kusan jihohi 20 ba su fara aiwatar da mafi karancin albashi ba. “Muna da Jihohi irinsu Sakkwato, Yobe, Gombe, Zamfara, Kaduna, Imo, Ebonyi, Borno, Kurus Ribas, Abuja, da dai sauransu, wasu sun fara biyan ma’aikatan jiharsu albashi sun...
    Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya nuna kaɗuwar sa bisa rashin da aka yi na ɗan Majalisar Dokokin jihar, Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji, ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Ƙauran Namoda ta Kudu. Iyalai sun bayyana cewa Hon. Aminu Kasuwar Daji ya rasu ne a cikin barcin sa da asubahin ranar Larabar nan a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa gwamnan ya miƙa ta’aziyyar sa ga Majalisar Dokokin jihar da Iyalan mamacin. Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta aika da tawaga ta musamman, ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Mallam Mani Mummuni a yayin jana’izar ta marigayi Aminu K/Daji in...
    Majalissar Dokokin Rasha ta amince da yerjejeniyar huldar ta shakaru 20 tsakanin kasar da Iran. Wannan na nuna muhimmin mataki na zurfafa dangantakar siyasa, soja da tattalin arziki tsakanin Moscow da Tehran. Yarjejeniyar ta tsawon shekaru 20, wakilan majalisar sun amince da ita ne a kuri’ar da aka kada a ranar Talata ta yadda kasashen biyu za su iya yin hadin gwiwa cikin tsari da inganci. Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na kasar Iran Massoud Pezeshkian ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a cikin watan Janairu, da nufin karfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban da suka hada da tsaro, makamashi, kudi, sufuri, masana’antu, noma, al’adu, da kimiyya da fasaha. Yarjejeniyar ta kuma bada damar zuba jari a...
    Amurka za ta iya janye sojoji 10,000 daga Gabashin Turai, kamar yadda rahoton NBC News ya bayyana. A shekarar 2022, tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya tura karin sojoji 20,000 zuwa yankin bayan Rasha ta kai hari Ukraine. A ranar Talata, NBC ta ruwaito cewa jami’ai shida daga Amurka da Turai sun tabbatar da tattaunawa kan rage yawan sojojin da aka tura, inda aka fi mayar da hankali kan rage adadin a Romania da Poland. Shugaba Donald Trump yana kokarin kawo karshen yakin Ukraine da aka shafe fiye da shekaru uku anayi tun bayan hawansa mulki, amma har yanzu bai cimma nasarar warware matsalar ba. Ya sha sukar NATO, yana mai jaddada cewa ya kamata Turai ta dauki karin nauyi...
    Duk da wannan zullumi da ake ciki, a kwanakin baya, kasar Sin ta tattauna da wasu kamfanonin Amurka sama da 20 cikinsu har da Tesla, inda ta kara ba su tabbacin cewa, za ta ci gaba da bude kofarta ga kamfanonin kasashen waje da aiwatar da gyare-gyare a gida. Wannan shi ake nufi da babbar kasa mai sanin ya kamata, mai kuma la’akari da moriyar sauran kasashe maimakon moriyarta ita kadai.   Idan Amurka na ganin matakanta za su danne ci gaban wasu kasashe, su kuma bata fifiko a duniya, to ta yi kuskure, domin yanzu ta budewa duniya ido, kuma kasashe da ma kamfanoninsu, za su koma ne ga inda suka tabbatar da cewa za su samu moriya, kuma...
    Ya ce karin wa’adin na baya-bayan nan ya biyo bayan cikar wa’adin farko na ranar 1 ga Afrilu, 2025, wanda aka sanya tun da farko a ranar 24 ga watan Janairu.   Umar ya kara da cewa, duk da wannan karin wa’adin, amma an ci gaba da samun karancin fitowar masu filaye domin sabunta takardunsu.   Domin tabbatar da bin ka’ida, kwamishinan ya yi gargadin cewa, nan ba da jimawa ba, za a buga sunayen wadanda ba su bi ka’ida ba a jaridun kasar nan da kuma nuna su a allunan sanarwa a muhimman wuraren gwamnati da suka hada da dakin karatu na jihar Kano, Sakatariyar Audu Bako, Gidan Murtala, da kuma babbar kotun jihar. Daga kanmu, magana ta...
     Kasashen Uku Suna Yin Taron ne dai a matsayin kwararru domin tattauna batutuwa da dama daga cikinsu da akwai na shirin Nukiliya na Iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’ila Baka’i ne ya sanar da cewa za a yi wannan taron ne a birnin Moscow wanda kuma ya kuma kunshi wakilai daga kasashen Iran, China da kuma mai masaukin baki Rasha. Buku da kari Baka’i, ya kuma bayyana cewa za a yi wata tattaunawar a tsakanin Iran da tarayyar turai a matakin masana shari’a. A can kasar Rasha mai Magana da yawun harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ta fada wa kafafen watsa labarun kasar ta Rasha cewa, a gobe Talata ne za a yi tattaunawar a tsakanin kwararru daga kasashen...
    A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, a yayin bikin ranar yara kanana ta duniya a Falasdinu, cibiyoyi masu fafutuka kan harkokin fursunoni sun sanar da cewa: Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila tana ci gaba da tsare kananan yara Palastinawa sama da 350 a gidajen yari da wuraren da ake tsare da fursunoni. Sanarwar hadin gwiwa da hukumar kula da harkokin tsare-tsare, da “Kungiyar Fursunonin palasdinu”, da kuma “Cibiyar Kare Hakkokin Bil Adama ta Al-Dameer” suka fitar, ta bayyana cewa, yaran na fuskantar matsaloli Ciki har da azabtarwa, yunwa da gangan, da rashin kulawar likita. Wadannan cibiyoyi sun jaddada cewa yaran Palasdinawa su ma suna fuskantar tauye hakkinsu, wanda irin wannan hali ne ya yi sanadin shahadar wani yaro a cikin makon...
    Yayin gabatar da rahoton an raba lambar yabo ga Hakiman da aka fi samun gudunmawar Zakkar daga gundumominsu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran ta yi kira ga kasashe mambobi kungiyar hadin guiwa ta Shanghai da ta yi Allah wadai da barazanar Trump ta baya baya nan kan kasar. A taron ministocin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da aka gudanar a birnin Moscow a ranar Alhamis, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht Ravanchi, ya yi kira ga mambobin kungiyar SCO da su yi Allah wadai da kalaman da shugaban na Amurka Donald Trump ya yi a baya-bayan nan kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, lamarin da ya ce yana da hadari. Majid Takht Ravanchi ya yi kakkausar suka ga barazanar harin bam da Trump ya yi a wata hira da tashar NBC News, inda ya ce, hakan ya keta...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta yi na kakaba “harajin ramuwar gayya,” kana ta magance sabanin dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashen duniya dangane da tattalin arziki da cinikayya, ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito, da mutunta juna ta yadda bangarorin za su ci moriyar juna. Guo ya bayyana hakan ne a taron manema labarai na yau, a matsayin martani ga wata tambaya game da sanarwar da Washington ya yi na kakaba “harajin ramuwar gayya” kan manyan abokan cinikiayya. Yana mai cewa, a karkashin manufar “ramuwar gayya”, Amurka ta sanya karin harajin fito kan kayayyakin da ake fitarwa daga kasar...
    Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya gargadi Amurka da cewa. duk wani harin soji a kan cibiyoyin nukiliyar Iran zai haifar da “mummunan sakamako” ga daukacin yankin. Sergei Ryabkov ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da wata mujallar harkokin kasa da kasa, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai wa Iran hari idan har ta kasa cimma matsaya da Washington kan shirinta na nukiliya. Ryabkov ya ce, “Hakika ana jin barazanar, ana kuma jin bayanai kan abubuwan da suka dace,” in ji Ryabkov, yana mai cewa “Sakamakon hakan, musamman idan harin ya kasance kan kayayyakin nukiliya, na iya zama bala’i ga daukacin yankin.” Ya ce sabbin kalaman na Trump za su kara...
    Akalla mutane 2 ne suka rasa rayukansu a sabbin hare-haren da jiragen Amurka suka kai kan kasar Yemen a jiya Laraba da yamma, saboda hanata tallafin da take bawa falasdinawa a Gaza wadanda sojojin HKI sukewa kissan kare dangi a gaza. Tare da hana abinci shigowa yankin kimani watanni 2 da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin Amurka sun kai wadannan hare-hare ne a garin Rasul Isa da lardin Salif a yammacin birnin Hudaida na kasar ta Yemen. Sannan tashar talabijin ta Almasirah ta bayyana cewa akalla mutum guda ne ya rasa ransa a wannan harin sannan wani guda ya ji rauni. Har’ila yau jiragen yakin Amurkan sun kai hare-hare kan yankin...
    Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya sanar da shirin kai ziyara birnin Tehran nan da makwanni masu zuwa a yayin da ake ci gaba da tattaunawa don tsaida takamaimen lokacin. Ziyarar ta zo ne a wani bangare na ci gaba da huldar diflomasiyya tsakanin Iran da hukumar IAEA, da nufin tinkarar batutuwan da suka shafi Nukiliya, da samar da hadin gwiwar fasaha cikin tsarin alkawurran da Iran ta dauka a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Ziyarar ta kuma jaddada irin hadin gwiwar da Tehran ke ci gaba da yi da hukumar ta IAEA, duk da matsin lamba daga waje da kuma zargin siyasa daga kasashen yammacin Turai. Da yake amsa...
    Yakin cinikayya ba zai taba durkusar da kasar Sin ba, sai dai kaikayi ya koma kan mashekiya. Yayin da wasu kasashen ke aiwatar da kariyar cinikayya da kokarin rufe kofarsu ga sauran sassan duniya, kasar Sin ta kara bude kofarta, tana kuma maraba da ’yan kasuwa daga kasa da kasa. Maimakon kawo cikas, kasar Sin za ta lalubo hanyoyin samun karin ci gaba ga kanta da sauran sassan duniya, kuma kariyyar cinikayya da ake yi, zai rikide ya zamo alheri a gare ta.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
    Kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Kebbi, NUJ, ta taya gwamnatin jihar da al’ummar musulmin jihar murnar zagayowar ranar Sallah.   Majalisar a cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na jiha, Kwamared Bello Sarki Abubakar da Sakatare, Ismail Adebayo, ta yi murna da al’ummar musulmin jihar kan kammala azumin kwanaki 29 na watan Ramadan da kuma bikin Eid-Fitr.   Ta yi kira da a zauna lafiya da juna a tsakanin al’ummar jihar bisa koyarwar addinin Musulunci da manzon Allah mai tsira da amincin Allah tare da la’akari da muhimmancin watan Ramadan da Idi-El-Fitr.   Majalisar ta yabawa gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Nasir Idris kan kayayyakin abinci da aka rabawa musulmi a...
    Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Dakta Abdul’aziz Yari, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu na alheri fiye da watan Ramadan.   Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa Talatan Mafara, a wani bangare na sakonsa na Sallah, Yari ya jaddada muhimmancin ci gaba da al’adun bayar da Zakka, Sadaka, da sauran nau’o’in tallafi ga marasa galihu a duk shekara.   Ya yabawa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa bullo da shirye-shiryen jin dadin jama’a da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya.   Dokta Yari ya yi kira ga ‘yan kasar da su ba da cikakken goyon baya ga kokarin shugaban...
    Majalisar Karamar Hukumar Jahun dake Jihar Jigawa ta kaddamar da rabon tallafin kayan noman rani ga manoma 300.   A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a Garin Darai, shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Jamilu Muhammad Danmalam yace hakan na daga cikin manufofin Gwamna Umar Namadi na bunkasa noman rani da na damina domin kawar da yunwa da kuma samar da abinci ga al’umma. A cewar sa, karamar Hukumar ta ware wasu yankunan Sahara domin fara noman rani a karo na farko dan fadada harkar noma a kan Tudu.   Alhaji Jamilu Danmalam yace an zabi kauyen Tunubu dake mazabar Kanwa domin fara noman Rani. Ya kara da cewar, wadanda suka anfana da tallafin za su ci moriyar kaso...
    Kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC Rear Admiral Ali-Reza Tangsiri ya tunatar da gwamnatin Amurka kan cewa idan ta aikata wawta ta kaiwa cibiyoyin Nukliyar kasar zata gamu da maida martani mai tsanani. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Tansiri yana fadar haka a kan jirgin ruwa mai daukar jiragen saman yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa a cikin tekun farisa wanda aka sanyawa suna Shahid Baghiri mai kuma  tsawon mita 180. Sannan   Labarin ya kara da cewa gwamnatin shugaba Donal Trump na kasar Amurka ta bawa Iran razarar watanni biyu ta amince da zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ta yi shirin yaki da kasar ta Amurka. Dakarun...
    Wanda ya jagoranci sallar juma’a a nan Tehran a jiya Juma’a ya bayyana cewa; Jerin gwanon ranar Kudus tana da matukar muhimmanci a addinin musulunci, yana mai kara da cewa: Muna godewa Allah madaukakin sarki cewa, ranar kudus ta wannan shekarar ta bunkasa fiye da shekarun baya.” Haka nan kuma ya kara da cewa; Imam Khumaini ( r.a) da ya ayyana ranar Kudus a duniya a 1979, wacce ita ce juma’ar karshe ta watan Ramadan, a wancan lokacin manyan kasashen duniya masu takama da karfi suna kokarin ganin an mance da batun Falasdinu da kuma kasakantar da shi da cewa batu ne na Larabawa kadai. Limamin na Tehran ya kuma kara da cewa, abinda Imam Khumain ( r.a) ya yi...
    A wannan Juma’a ce 28 ga watan Maris na shekarar 2025, aka gudanar da taruka da jerin wano na ranar Qudus ta duniya wadda ta zo daidai da ranar Juma’ar karshe ta watan Ramadan mai alfarma. An gudanar da wadannan taruka da jerin gwano ne a kasashe daban-daban da suka hada da wasu kasashen musulmi da na larabawa, har da wasu da wasu daga cikin kasashn ymmacin duniya da kuma na Afirka, ta hanyar shirya gagarumin gangamin da ke jaddada aniyarsu ta tabbatar da al’ummar Palastinu ta samu hakkokinta da Haramtacciyar kasar Isra’ila ta haramta musu, tare da nuna cikakken goyon baya ga gwagwarmayarsu ta neman samun wadannan hakkoki nasu. A safiyar Juma’ar ne aka fara gudanar da jerin gwano...
    Aikin na tura danyen Man, ya kai akalla tsawon kilo mita 180 wanda a tura shi, daga wajen hako shi da ke a yankin Neja Delta. danyen Man da Nijeriya ke hakowa, ya kai kasa da yawan wanda Hukumar OPEC ta iyakan ce, a watan Fabirairun  2025, wanda ya kai yawan Ganga  1,465,006 da ake hakowa a  kullum. A yanzu dai, ana ci gaba da gudanar da bincike, domin a  gano musababbin abinda ya janyo fashewar man Bututun dan Man da irin asarar da aka tabka da kuma yawan adadin wadanda suka samu raunuka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
    Ana ci gaba da gudanar da jerin gwamnon ranar Kudus ta duniya a birane daban-daban na kasashen duniya. Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, yanzu haka ana ci gaba da gudanar da jerin gwamnon ranar Kudus ta duniya a birane daban-daban na kasashen duniya. Marigayi Imam Khomeni ne ya ayyana ranar karshe ta kowane Radan a matsayin ranar Kudus ta duniya tun fiye da shekaru 40 da suka gabata, kuma ana ci gaba da gudanar tarukan wannan rana a kowace shekara a Iran da sauran sassa na duniya.
    A safiyar yau ne aka fara gudanar da jerin gwano na ranar Qudus ta duniya a duk fadin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda aka samu halartar jama’a da dama karkashin taken “Muna ci gaba da cika alkawarin da muka dauka.” Mahalarta taron za su yi tattaki ne daga masallatai da manyan filaye a birane da kauyukan kasar zuwa wuraren da ake gudanar da Sallar Juma’a. A birnin Mashhad da ke gabashin Iran, tun da sanyin safiya ne aka fara gudanar da jerin gwano a wani bangare na bikin na shekara-shekara. A halin da ake ciki dai jama’a a birnin Tehran sun fara taruwa daga wurare daban-daban a kan titin juyin juya hali domin tunawa da wannan rana. A cewar wakilin...
    Imam sayyid Aliyul Khamina’ie Jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran yayi kira ga mutanen kasar su fito kwansu da kwarkwatansu don halattar zanga-zangar ranar Kududs ta duniya a yau Jumma’a. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Alhahamis da yamma. Ya kuma kara da cewa fitowar zanga-zangar ranar Kudus ta duniya alama ce ta hadin kan mutanen kasar Iran, sannan cika alkawali ne ga al-ummar kasar Falasdinu kan cewa mutanen kasar Iran ba zasu taba barinsu su, su kadai ba. Ranar Qudus ta duniya dai, rana ce wacce Imam Khomaini (q) wanda ya kafa JMI ya ware a ko wace ranar Jumma’a ta karshe...
    Jiragen ruwan yaki na dakarun juyin juya halin musulunci  IRGC a nan Iran, kanana da manya-manya, har’ila yau da na masu sa kai sun gudanar da faretin jiragen ruwan yaki don raya ranar Kudus ta duniya kwana guda kafin ranar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto dubban  jiragen yaki da na masu sa kai a tekun Farisa da ke kudancin kasar da kuma tekun Caspian da ke arewacin kasar suna jerin gwano a cikin ruwayen yankunansu don raya wannan ranar. Dakarun IRGC sun gudanar da wannan atisai ne a jiya Alhamis, don nuna goyon bayansu ga Falasdinwa musamman a Gaza, wadanda a halin yanzu, sojojin HKI sun yi masau kawayya, sun hana shigowar abinda da abinsha  cikin...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kira hadin kan kasashen duniya domin nuna goyon baya ga Falasdinu gabanin ranar Kudus ta Duniya. Kungiyar ta yi kira da a samar da hadin kai a kasashen duniya a ranar Juma’a da Asabar da Lahadi masu zuwa domin nuna goyon baya ga Gaza da Kudus, yayin da Isra’ila tare da goyon bayan Amurka ke ci gaba da yakin kisan kare dangi da suke yi wa Falasdinawa. A cikin sanarwar da ta fitar, Hamas ta yi kira da a gudanar da gagarumin jerin gwano na hadin gwiwa a dukkan birane da manyan birane na duniya. “Muna kira ga daukacin al’ummar Falasdinu, kasashen Larabawa da na Musulunci, da dukkan al’ummarmu masu son ‘yanci na...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kira ga al’ummar kasar da su nuna hadin kai a yayin bukukuwan ranar Kudus ta duniya wato ranar JUma’ar kashe ta watan Ramadana da ke gabatowa, yana mai jaddada cewa hakan zai nuna matukar goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga al’ummar Falastinu. Pezeshkian, ya bayyana hakan ne a yayin taron majalisar ministocin kasar na farko sabuwar shekarar kalandar farisa, inda yake cewa “Ina fatan tare da halartar al’ummar kasar, za a gudanar da ranar Kudus mai daraja, kuma a wannan rana al’umma za su nuna hadin kai ga duniya.” Ranar Kudus ta duniya dai marigayi Imam Khumaini ne ya ayyana ta kuma ana gudanar da ita a kowace shekara a ranar Juma’ar...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300 a Yobe Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, tare da yin kira a gare su da su ci gaba da halaye nagari da suka koya a watan. Haka kuma ya jaddada muhimmancin soyayya, yafiya, da haɗin kai wajen gina al’umma. Tunji-Ojo, ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan...
    Mai Magana da yawun gwamnatin Iran malam Fatima Muhajirani ta yi ga al’ummar Iran da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin halartar jerin gwanon ranar Kudus ta duniya, wacce take fatan ganin ta taka rawa wajen taimakawa al’ummar Falasdinu. Muhajirani wacce ta yi bayanin haka a wata hira ta tashar talbijin ta kuma kara da cewa; Gwargwadon yadda al’umma za su fito wajen yin jerin gwanon saboda hadakar da ake da ita a tsakanin al’ummar Iran da Falasdinawa ta fuskokin addini da al’adu, da kuma tarayya akan manufofin juyi, tasirin haka zai fi fitowa. Malama Fatima Muhajirani ya kuma ambato maganar Imam Khumaini         ( r.a) akan fatansa na ganin an sami fitowa mai yawa domin karfafa al’ummar Falasdinu. A na...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhummanci a makon da ya gabata, dangane da siyasa tattalin arziki zamantake tsaro da sauran, sannan mu yi masu karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////.. Madallah, masu sauraro shirinmu na yau zai yi dubi dangane da “ranar Qudus ta Duniya’ wacce aka rayata a jiya Jumma’a ce 27 ga watan Ramdan shekara ta 1446 wanda yayi dai-dai da 28 ga watan Maris shekara ta 2025 miladiyya ne aka gudanra da ranar Qudus ta duniya, a nan kasar Iran da kuma...
    Kwamitin tallafawa marayu da masu karamin karfi na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Ikamatis Sunnah dake karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa ya tallafawa gidajen marayu da masu karamin karfi da kayan abinci na kusan naira miliyan 9. Shugaban kungiyar Sheikh Hassan Sabo Musa ya bayyana hakan yayin rabon kayan da aka gudanar a karamar hukumar Babura.   Yace, an sami gudunmawar  kudade da kayan abinci daga al’umma da kungiyoyi. Sheihk Hassan Musa ya kara jadadda bukatar cewar, ya zama wajibi a rika jibintar al’amuran marayu domin samun falala daga Allah.   A jawabinsa, shugaban kwamitin tallafawa marayu,  Malam Nura Sale ya ce wannan shine karo na goma Sha biyu na shirin. Ya godewa wadanda suka bayar...
    Fadar Gidan Gwamnatin Amurka (WhiteHouse), ta ce Rasha da Ukraine sun amincewa Jiragen jigilar kayayyakin kasuwanci gudanar da zirga-zirga cikin aminci a tekun Black Sea ba tare da kai musu hare-haren soji ba. Amurka ta fitar da wannan sanarwar ne bayan jami’an Amurka sun gana da wakilan kasashen biyu a Saudiyya a ranar Talata. Dole Ne A Tauna Tsakuwa Don Aya Ta Ji Tsoro Sin Na Ci Gaba Da Kasancewa Cibiyar Rarraba Hajojin Da Masana’antu Ke Sarrafawa Sai dai Rasha ta ce, dole ne a dage wasu takunkuman da aka sanya wa bankuna, kamfanonin inshora, da masu fitar da abinci, kafin yarjejeniyar tsagaita bude wutar ta fara aiki. Sai dai, Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya zargi Rasha da “kwarara...
    Kasar Rasha ta bayyana a wannan Talata cewa tana nazarin sakamakon tattaunawar da ta yi da Amurka kan Ukraine a Saudiyya, Rasha ta ce ba wani bayyani da za’a fitar game da tattaunawar, kuma ba wani lokaci da aka a sanya na ranar da za a sake ganawa da Amurkawa ba. “An ba da sakamakon tattaunawar da aka yi a manyan biranen, Kuma “Ana nazarin su,” in ji mai magana da yawun shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov yayin jawabinsa na yau da kullun. Rahotanni sun ce ana tattaunawa tsakanin Amurka da Ukraine har zuwa yau Talata. Bayan shafe sa’o’i 12 na tattaunawar sirri da aka yi a Saudiyya, jami’an Amurka da na Rasha sun kammala tattaunawa kan rikicin Ukraine a...
    Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kebbi ta raba kayan abinci da kudi ga iyalan mambobinta da suka rasu a lokacin da suke kan aikin jarida, a matsayin kyautar azumin Ramadan. Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kungiyar na Jiha, Kwamared Bello Sarki Abubakar, ya ce suna gudanar da wannan shiri a duk shekara, tun bayan kaddamar da shi da tsohon shugaban kungiyar na jiha Alhaji Aliyu Jajirma ya yi, domin faranta ran iyalan abokan aikinsu da suka rasu. Kwamared Sarki Abubakar ya bayyana cewa dukkan shugabannin kungiyar da suka gabata sun tabbatar da ci gaba da gudanar da wannan shiri a duk lokacin azumin Ramadan domin rage wa iyalan mamatan radadin wahalhalun rayu. Ya sanar...
    Bayan shafe sa’o’i 12 na tattaunawar sirri da aka yi a Saudiyya, jami’an Amurka da na Rasha sun kammala tattaunawa kan rikicin Ukraine a ranar Litinin. Hukumomin Rasha sun ruwaito cewa fadar White House da Kremlin za su fitar da sanarwar hadin gwiwa yau Talata kan tattaunawar da suka yi, wanda Moscow ta bayyana tun da farko a matsayin “mai wuyar gaske.” Tattaunawar yanzu tana mai da hankali kan yiwuwar tsagaita wuta a tekun Black Sea, domin ba da damar komawa kan yarjejeniyar da ta bai wa Ukraine damar fitar da hatsin da yake da muhimmanci ga samar da abinci a duniya. Ministan tsaron Ukraine Rustem Umerov ya bayyana ganawar da suka yi da Amurkawa a ranar Lahadi a matsayin...
    Ebrahim Rasool, jakadan Afirka ta Kudu da gwamnatin Trump ta kora, ya samu tarba a wannan Lahadin daga daruruwan magoya bayansa da suke rera wakoki  domin karrama shi a filin jirgin sama na Cape Town. Jama’a sun kewaye Rasool da matarsa ​​Rosieda bayan isowarsu, yayin da ‘yan sanda suka yi musu rakiya har zuwa tashar jirgin kasa. Da yake yiwa magoya bayansa jawabi, Rasool ya ce, Abin da ya faru yana a matsayin wulakanta ku ne ku al’ummar Afirka ta kudu, amma kuma idan kuka tsaya tsayin daka kan manufofinku na ‘yancin kai to za ku ci gaba da rayuwa a cikin mutunci da daukaka. Ya ce ba laifi muka yi ba, ammam kuma mun dawo gida ba tare da...
    Ƴansandan sun gayyaci Sanata Sunday Karimi domin bayani kan zarginsa na cewa ƙungiyar leƙen asirin ƙasar Rasha ta KGB ta samu shiga cikin Majalisar Dokoki, wanda ke barazana ga tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya. Zargin ya samo asali ne daga rahoton da Sanata Karimi ya raba akan ƙungiyar ta WhatsApp a Majalisar Dattijai a ranar 23 ga Fabrairu, 2025. Rahoton, wanda aka wallafa ta gidan jaridar The Reporters, ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin Majalisar, inda Sanata Natasha H. Akpoti-Uduaghan, wacce aka dakatar, ta shigar da buƙatar yin bincike ga Shugaban ‘Yansanda. Fiye Da Dalibai 4,200 Suka Amfana Da Tallafin Ilimi Na Sanata Solomon Adeola Kotu Ta Dakatar Da INEC Karɓar Buƙatar Yin Kiranye Ga Senata Natasha A cikin ƙarar da ta...
    Ya sanar cewa karamar hukumar ta kuduri aniyar daukar tsauraran matakai don dakile wannan barazana ta hanyar tura jami’an GOSTEC da Operation Hattara don inganta tsaro.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnonin Arewa sun aike wa Gwamna Dikko Umar Radda na Jihar Katsina, saƙon ta’aziyya game da rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru Baribari, wadda ta rasu tana da shekaru 93. Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana Hajiya Safara’u a matsayin uwa mai tausayi da riƙon gaskiya, wadda ta rayu bisa turbar Allah da hidima wa al’umma. ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a Zamfara Mahaifiyar Gwamnan Katsina ta rasu A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, Gwamna Yahaya, ya iyalanta da shugabanni za su yi kewarta. Ya kuma buƙaci Gwamna Radda da iyalansa da su ci gaba da girmama tarihinta ta...
    Kasar Rasha ta bayyana cewa dole Moscow da Beijing su shiga shawarwarin tattaunawar nukiliya da Iran. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyana cewa, Moscow a shirye take ta samar da ingantacciyar hadin gwiwa da dukkan bangarorin kan batun yarjejeniyar nukiliyar Iran. “ Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa ya aike da wasika zuwa Tehran domin fara tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran; yayin da shi da kansa ya fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran a wa’adinsa na farko. A halin da ake ciki dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump a cikin kwanaki masu zuwa...
    Allah Ya yi wa mahaifiyar Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda rasuwa. Wakilinmu ya ruwaito cewa, mahaifiyar Gwamnan, Hajia Safara’u Umar Radda, ta rasu ne a wani asibiti da ke birnin Katsina. Cikin wani saƙo da tsohon mai magana da yawun gwamnan, Isah Miqdad ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Hajiya Safara’u ta riga mu gidan gaskiya bayan ta yi fama da doguwar jinya. Mabiya dandalan sada zumunta na ci gaba da bayyana alhini dangane da rasuwar Hajiya Safara’u.