Gwamna Yusuf Ya Bada Hutu A Ranar Litinin Domin Addu’o’i Ga ‘Yan Wasan Kano 22 Da Suka Rasu
Published: 1st, June 2025 GMT
Gwamna Yusuf wanda a halin yanzu yake kasar Saudiyya don gudanar da aikin hajjin 2025, ya bayar da umarnin ware ranar Litinin 2 ga watan Yunin 2025 a matsayin ranar hutu domin bai wa al’ummar damar yin jimami tare da yi wa wadanda suka rasu addu’a.
Ya kuma yi kira ga limamai da daukacin al’umma a fadin jihar, da su yi addu’o’i na musamman ga wadanda abin ya shafa da kuma karfafa wa iyalansu da suka rasu.
Gwamna Yusuf ya tabbatar da cewa, gwamnati na daukar matakan tallafawa wadanda suka jikkata da kuma iyalan wadanda abin ya shafa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Al’ummar Fegin Mahe Sun Yi Zanga-zanga Kan Kisan Jama’a Da ‘Yan Bindiga Ke Yi
Daruruwan mazauna kauyen Fegin Mahe da ke yankin Ruwan Bore a karamar hukumar Gusau ta Jihar Zamfara, sun gudanar da zanga-zanga a gaban Gidan Gwamnati da ke Gusau, inda suka bukaci gwamnatin jihar ta dauki matakin gaggawa kan kisan gilla da ‘yan bindiga ke yi a yankinsu.
Masu zanga-zangar sun rike takardu masu dauke da rubuce-rubuce kamar su: “Muna bukatar zaman lafiya a yankunanmu” da “Gwamnati ta cika alkawarin da ta dauka”.
A cewar mazauna kauyen, harin ya faru ne da safiyar ranar Laraba, lokacin da wasu ‘yan bindiga dauke da manyan makamai suka afka wa kauyen, inda suka rika harbin mai-kan-uwa-da-wabi.
Al’ummar yankin sun bayyana harin a matsayin daya daga cikin mafi muni da suka taba fuskanta a ‘yan shekarun nan, wanda ya bar su cikin tsoro da fargaba.
Masu zanga-zangar sun ce manufarsu ita ce jawo hankalin gwamnati kan tabarbarewar tsaro a yankin da kuma bukatar daukar matakin gaggawa don dakile kisan fararen hula da ake ta yi ba kakkautawa.
Sun kuma koka da cewa har yanzu akwai gawarwakin wasu daga cikin mutanen da aka kashe a dajin, amma babu wanda ke iya dauko su saboda tsoron sake fuskantar hari daga hannun ‘yan bindigar.
Har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, ba a samu wata sanarwa ko martani daga gwamnatin jihar ba dangane da harin ko kuma zanga-zangar da aka gudanar.
Daga Aminu Dalhatu