Ambaliyar Ruwa Ya Yi Barna A Sassan Sudan Tare Da Kara Janyo Matsalolin Jin Kai A Kasar
Published: 30th, September 2025 GMT
Ambaliyar ruwa a Sudan na barazana ga rayuwar dubban mutane tare da kara munana matsalolin jin kai
Kogin Nilu ya mamaye yankuna da dama a Sudan, lamarin da ke barazana ga rayuwar dubban mutane. Ambaliyar ruwa ta lalata gonaki da kadarori a jihar Al-Jazirah da kewaye, lamarin da ya shafi dubban iyalai tare da barin su cikin bukatar tallafin gaggawa da matsuguni da abinci da magunguna.
Haka zalika ruwan sama kamar da bakin kwarya ya dakatar da zirga-zirgar wasu jama’a a wasu yankuna, yayin hukumomin cikin gida suke kokarin rage barnar da ake amma lamarin ya foi karfinsu sakamakon karancin kayan aiki.
Ambaliyar ruwan ta kara ta’azzara matsalar jin kai a birnin El Fasher da sauran garuruwa, inda mazauna garin ke fama da matsanancin karancin abinci, ruwan sha, da kuma ababen more rayuwa. Ambaliyar ta kawo cikas ga zirga-zirgar kungiyoyin agaji da iyalai da suka rasa matsugunansu da gidajensu ke kan gabar kogin Nilu. Hukumomi sun bukaci al’ummar Sudan da su yi taka-tsan-tsan, tare da gargadin cewa ci gaba da karuwar ruwan na iya yin barazana kai tsaye ga gidaje da ababen more rayuwa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas : Shirin da Trump ya gabatar yana “Kusa da Hangen Isra’ila” September 30, 2025 Isra’ila : Netanyahu na shan suka bayan ya nemi afuwar Qatar September 30, 2025 Araghchi ya gana da sakatare janar na MDD September 30, 2025 Madagascar : Shugaba Rajoelina ya sanar da korar daukacin gwamnatinsa September 30, 2025 Adadin Hada-hadar Kasuwancin Kasashen Waje Ta Iran Takai Dala Biliyan 54 A Cikin Wata 6 September 30, 2025 Janar Safavi: matukan jirgen Isra’ila 16 ne suka a harin makami mai linzami na Iran a lokacin yaki September 30, 2025 Trump: Za mu goyi bayan Netanyahu idan Hamas ba ta amince da kudirinmu ba September 30, 2025 Iran: An zartar da hukuncin kisa a kan wani babban dan leken asirin Isra’ila September 30, 2025 Axios: Netanyahu ya nemi afuwar Qatar kan harin da Isra’ila ta kai a kan Doha September 30, 2025 Larijani: Iran a shirye take don tallafawa Lebanon da gwagwarmaya a kowane mataki September 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Congo ta tsawaita haramcin fataucin ma’adinai a gabashin kasar
Ma’aikatar ma’adinai a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta sanar da tsawaita dokar hana fataucin ma’adinai na tsawon watanni shida daga wuraren hakar ma’adinai da dama a lardunan Kivu ta arewa da ta kudu da ke fama da rikici.
Sabunta haramcin zai kara kawo tsaiko da cikas wajen samar da wasu ma’adanai a duniya, musamman ma’adaanai irin su tin, tantalum, da tungsten, mahimman abubuwan da ake amfani da su wajen kera kayan lantarki, motoci, da wasu ayyuka na sararin samaniya.
Haramcin, wanda aka fara aiki da shi a watan Fabrairu, ya ci gaba da aiki na tsawon wannan lokaci, inda shaidun ke nuna cewa kayayyakin da ake amfani da su ba bisa ka’ida ba daga ma’adinan suna tallafawa kungiyoyin masu dauke da makamai a gabashin Congo, a cewar wani bayani mai kwanan wata 3 ga watan Nuwamba mai dauke da sa hannun ministan ma’adinai na kasar, Louis Watom Kampaba.
Bayanin ya kunshi shafuka 38 da ke nuni da cewa haramcin ya shafi abubuwa da dama daga ciki har da coltan, cassiterite, da wolframite, tin, tantalum, da tungsten.
Har ila yau kungiyar ‘yan tawayen M23 da sauran kungiyoyi masu dauke da makamai sun kwace filaye da dama a gabashin Kongo mai arzikin ma’adinai a cewar Ministan.
Matakin da ma’aikatar ma’adinai ta dauka ya haramta fitar da kayayyaki daga wuraren hakar ma’adinan da ake magana a kai, kuma ta ce za su iya fuskantar bincike mai zaman kansa daga ma’aikatar ko hukumomin kasa da kasa, ciki har da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar hadin kan tattalin arziki da raya kasashen yankin gabashin nahiyar Afirka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Rasha: An dakile wani yunkurin kisan gilla kan Sakataren Majalisar Tsaron kasa November 18, 2025 Aref: Iran Tana Da Kyakkyawar Alaka Da Mambobin Kungiyar Hadin Gwiwa Ta Shanghai {SCO} November 17, 2025 Na’ini: Jagora Ne Da Kansa Ya Jagoranci Lamurra A Lokacin Yakin Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran November 17, 2025 Mahukuntan Gaza Sun Yi Gargadin Bullar Bala’in Jin Kai A Yankin Da Ba A Taba Ganin Irinsa Ba November 17, 2025 Sheikh Na’im: Gwamnatin Lebanon Zata Yi Babban Kuskure Matukar Tabi Hanyar Sassauci November 17, 2025 Rushewar Ramukan Hako Ma’adinai Ta Kashe Mutane 32 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango November 17, 2025 Alummar Kasar Ecodo Sun yi Watsi Da Batun Sake Dawo Da Sansanin Sojin Amurka A Kasar November 17, 2025 Sojojin HKi Sun Kashe Wasu Falasdinawa Guda 2 A Sansanin Yan Gudun Hijira November 17, 2025 Tawagar Wasan Wushu Ta Kasar Iran Ta Samu Lambobin Yabo 4 A Saudiya November 17, 2025 Shugaban Nukiliyar Iran Yace Amurka Da Israila Sun Shiga Sabon Mataki Mai Hadari November 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci