HausaTv:
2025-11-18@14:04:49 GMT

Hamas : Shirin da Trump ya gabatar yana “Kusa da Hangen Isra’ila”

Published: 30th, September 2025 GMT

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta ce kawo yanzu bata samu ba ta samu rubutaccen shirin zaman lafiya na shugaban Amurka Donald Trump kan Gaza ba.

Mahmoud Mardawi wani babban jami’in kungiyar ta Hamas ya bayyana cewa har yanzu kungiyar ba ta samu daftarin shirin, wanda kafofin yada labaran Amurka suka wallafa bayanansa.

Amma ya bayyana cewa tabas shirin wanda bai da garanti yana kusa da hangen nesa na Isra’ila.

Dangane da furucin da Trump ya yi na kwance damarar kungiyar, ya fayyace cewa Hamas ba a taba amfani da makamanta ba da nufin kai hari ba, sai dai kawai domin kare ‘yancin cin gashin kan Falasdinu.

Mardawi ya soki shirin na Trump, yana mai imani cewa wani yunkuri ne na dakile ci gaban kasa da kasa da kuma amincewa da kasar Falasdinu.

Ya yi gargadin cewa kungiyar Hamas ba za ta amince da duk wani shiri da ba zai tabbatar wa al’ummar Palasdinu ‘yancin cin gashin kai da kuma kare kai daga kisan kiyashi ba.

A jiya ne Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da kudirin samar da zaman lafiya mai kudurori 20 kan Gaza, yana mai cewa zai kawo karshen yakin da Isra’ila ke yi shekaru biyu a Gaza.

Trump wanda ya gana da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a fadar White House, Ya ce ya gabatar da shirin wanzar da zaman lafiya ga shugabannin Larabawa da na Musulmi a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya.

Shirin ya tanadi sakin daukacin mutanen Isra’ila da ake garkuwa da su a cikin sa’o’i 48, da kwance damara a Gaza, da kuma janye sojojin Isra’ila sannu a hankali daga yankin.

Kwamitin zaman lafiya da shugabannin kasashen Larabawa da Isra’ila da kuma Amurka za su jagoranci gudanar da tsarin.

Sai dai Trump ya nanata adawar Netanyahu a fili kan batun kafa kasar Falasdinu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Isra’ila : Netanyahu na shan suka bayan ya nemi afuwar Qatar September 30, 2025 Araghchi ya gana da sakatare janar na MDD September 30, 2025 Madagascar : Shugaba Rajoelina ya sanar da korar daukacin gwamnatinsa September 30, 2025 Adadin Hada-hadar Kasuwancin Kasashen Waje Ta Iran Takai Dala Biliyan 54 A Cikin Wata 6 September 30, 2025 Janar Safavi: matukan jirgen Isra’ila 16 ne suka a harin makami mai linzami na Iran a lokacin yaki September 30, 2025 Trump: Za mu goyi bayan Netanyahu idan Hamas ba ta amince da kudirinmu ba September 30, 2025 Iran: An zartar da hukuncin kisa a kan wani babban dan leken asirin Isra’ila September 30, 2025 Axios: Netanyahu ya nemi afuwar Qatar kan harin da Isra’ila ta kai a kan Doha September 30, 2025 Larijani: Iran a shirye take don tallafawa Lebanon da gwagwarmaya a kowane mataki September 30, 2025 Takunkumin makamai na Turai ya haifar da mummunar illa ga tattalin arzikin sojojin Isra’ila September 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: zaman lafiya

এছাড়াও পড়ুন:

NELFUND ya raba wa ɗalibai tallafin karatu na Naira Biliyan 116 

Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) ya bayyana cewa ya raba jimillar kuɗi Naira biliyan 116 domin tallafa wa dalibai a faɗin ƙasar nan wajen biyan kuɗin makaranta da kuma kula da rayuwarsu ta yau da kullum.

Shugaban NELFUND, Akintunde Sawyerr ya bayyana a Abuja cewa, daga cikin kuɗin, an tura Naira biliyan 65 aka tura kai tsaye zuwa makarantu 239 na tarayya — jami’o’i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi — domin biyan kuɗin makarantar ɗaliban da aka amince da buƙatar lamuninsu.

Sauran Naira biliyan 51 kuma an tura ne kai tsaye ga ɗaliban a matsayin tallafin kula da rayuwa na wata-wata.

Ya ce: “Mun raba Naira biliyan 65 ga makarantu da kuma Naira biliyan 51 ga ɗaliban domin tallafin rayuwa. Jimillar kuɗin da aka fitar ya kai Naira biliyan 116.”

Sawyer ya ce har zuwa yanzu NELFUND biya dalibai 624,000 da suka riga suka fara karɓar kuɗin makaranta da tallafin rayuwa.

Shugaban NELFUND ya bayyana shirin a matsayin ɗaya daga cikin manyan shirye-shiryen saka jari na zamantakewa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar.

Ya ce manufar shirin ita ce kawar da matsalolin kuɗi da ke hana ɗalibai ci gaba da karatu, tare da tabbatar da cewa babu ɗan Najeriya da zai bar makaranta saboda rashin kuɗi.

Sawyer ya tabbatar da cewa NELFUND za ta ci gaba da gudanar da shirin cikin gaskiya da inganci, musamman ganin yadda yawan ɗaliban da ke amfana yake ƙaruwa a kullum.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hamas Ta yi Watsi Da Amincewa Da Kudurin Amurka Da Kwamitin Tsaro Ya yi Kan Gaza
  • Mahukuntan Gaza Sun Yi Gargadin Bullar Bala’in Jin Kai A Yankin Da Ba A Taba Ganin Irinsa Ba
  • Hamas Da Sauran Bangarorin Falasdinawa Sun yi Watsi Da Shirin Aikewa Da Dakarun Kasashen Waje A Yankin Gaza
  • NELFUND ya raba wa ɗalibai tallafin karatu na Naira Biliyan 116 
  • Kwamitin tsaron MDD zai kada kuri’a kan daftarin kudirin Trump kan Gaza
  • Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon
  • Na kusa komawa APC – Gwamnan Taraba
  • Lebanon za ta shigar da kara a kan Isra’ila a MDD game da gina Katanga a iyakarta
  • AU ta sake nanata cewa “Babu kisan kare dangi a arewacin Najeriya
  • Ma’ariv: Netanyahu Yana Tsoron Hukuncin  Da Kotu  Za Ta Yanke Akansa