HausaTv:
2025-11-18@12:51:33 GMT

Axios: Netanyahu ya nemi afuwar Qatar kan harin da Isra’ila ta kai a kan Doha

Published: 30th, September 2025 GMT

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nemi afuwar firaministan Qatar Mohammed bin Abdulrahman Al Thani a ranar Litinin din nan kan harin da jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka kai kan Qatar a baya-bayan nan wanda ya yi sanadin mutuwar wani jami’in tsaron Qatar, kamar yadda wata majiya mai tushe ta shaida wa Axios.

An bayar da rahoton neman afuwar a yayin ganawar Netanyahu da shugaban Amurka Donald Trump, kuma ana kallon shi a matsayin wani muhimmin sharadi da Doha ta gindaya na sake tattaunawa da Hamas a kan yarjejeniyar da za ta kawo karshen yakin Gaza da kuma sako sauran mutanen da aka yi garkuwa da su.

Bayan ganawar, fadar White House ta tabbatar da cewa Netanyahu ya bayyana matukar bakin ciki da cewa harin makami mai linzami da “Isra’ila” ta kai kan ofishin Hamas a Qatar ya kashe wani ma’aikacin Katar, tare da tabbatar da cewa ba za ta sake kai irin wannan a cikin Qatar a nan gaba ba.

A cewar fadar White House, PM Qatar Mohammed bin Abdulrahman Al Thani ya yi maraba da wadannan tabbacin, yana mai jaddada a shirye Qatar ta ci gaba da bayar da gudummawa mai ma’ana ga tsaron yankin.

Harin na ranar 9 ga watan Satumba mai cike da cece-kuce a birnin Doha ya nufi wasu manyan kusoshin Hamas ne, amma a maimakon haka ya yi sanadin kashe wasu ‘ya’yan kungiyar biyar wadanda basu hada da manyan kusoshin ba.

Harin ya haifar da tofin Allah tsine a duk fadin kasashen Larabawa tare da mayar da “Isra’ila” saniyar ware a fannin diflomasiyya.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Larijani: Iran a shirye take don tallafawa Lebanon da gwagwarmaya a kowane mataki September 30, 2025 Takunkumin makamai na Turai ya haifar da mummunar illa ga tattalin arzikin sojojin Isra’ila September 30, 2025 Kungiyar Yan Gudun Hijira Na Kasar Noway Tace Akwai Babbar Damuwa Game Shiru Kan Gaza September 29, 2025 Shugaban Iran: Yunkurin Durkusar Da Alummar Iran Bashi Da Maraba Da Mafarki. September 29, 2025 Kwamitin Tsaro A Majalisar Dokokin Iran Ta Gama Tsara Ficewar Kasar Daga NPT September 29, 2025 An Kashe Sojan HKI Guda A Harin Maida Martani A Yankin Yamma Da Kogin Jordan September 29, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Cewa Bukatun Amurka Daga Iran Ba Mai Yuwa Ba Ne September 29, 2025 Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Iran Yace SnapBack Baya Bisa Ka’ida September 29, 2025 Jami’an Tsaro A kasar Burtaniya Sun Tsare George Gallowy Da Matarsa Na Wani Lokaci September 29, 2025 Ayarin Jiragen Ruwan Keta Killace Yankin Gaza Sun Kusa Isa Yankin September 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Rushewar Ramukan Hako Ma’adinai Ta Kashe Mutane 32 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango

Rushewar ramukan hako ma’adinai ta kashe ma’aikata 32 a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Akalla ma’aikatan hakar ma’adinai 32 ne suka mutu a ranar Asabar sakamakon zaftarewar ƙasa a wani ma’adinan cobalt a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, yayin da ake ci gaba da neman waɗanda har yanzu ba a same su ba a yankin.

Zaftarewar ƙasa ta faru ne a wurin Kalandu da ke cikin ma’adinan Mulundu kusa da Kolwezi, wani wuri da kamfanin Bajiklem ke gudanar da shi a hukumance.

Ministan harkokin cikin gida na lardin, Rui Kawumba Mayondi, ya ce “masu hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba sun kai hari kan wurin duk da haramcin da aka sanya saboda ruwan sama mai ƙarfi da kuma haɗarin zaftarewar ƙasa,” ya ƙara da cewa “hawa da suka yi cikin gaggawa ya sa gadar da suka gina a kan wani rami da ambaliyar ruwa ta mamaye ta ruguje.”

Jami’in ya bayyana cewa zuwa yanzu ƙungiyoyin ceto sun gano gawawwaki 32 daga cikin tarkacen, kuma ana sa ran adadin waɗanda suka mutu zai ƙaru.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Alummar Kasar Ecodo Sun yi Watsi Da Batun Sake Dawo Da Sansanin Sojin Amurka A Kasar November 17, 2025 Sojojin HKi Sun Kashe Wasu Falasdinawa Guda 2 A Sansanin Yan Gudun Hijira November 17, 2025 Tawagar Wasan Wushu Ta Kasar Iran Ta Samu Lambobin Yabo 4 A Saudiya November 17, 2025 Shugaban Nukiliyar Iran Yace Amurka Da Israila Sun Shiga Sabon Mataki Mai Hadari November 17, 2025 Hamas Da Sauran Bangarorin Falasdinawa Sun yi Watsi Da Shirin Aikewa Da Dakarun Kasashen Waje A Yankin Gaza November 17, 2025 Nukiliya : Iran zata sake duba huldarta da IAEA idan aka dauki wani sabon mataki kanta November 17, 2025 Kwamitin tsaro zai kada kuri’a kan daftarin kudirin Trump kan Gaza November 17, 2025 Ansarullah Ta Yi Allah Wadai Da Sabunta Takunkumin MDD Kan Yemen November 17, 2025 Afirka ta Kudu na Binciken shigar wasu ‘yan gudun hijirar Falasdinu 153 cikin kasar November 17, 2025 Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo na biyu a jere November 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mataimakin Shugaban Iran Na Daya Ya Gana Da Prime Ministan Rasha A Birnin Mosko
  • Ministan tsaron Iran na Ziyara a UAE don karfafa dangantakar tsaro tsakanin kasashen yankin
  • Congo ta tsawaita haramcin fataucin ma’adinai a gabashin kasar
  • Na’ini: Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Da Kansa Ya Jagoranci Yaki Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran
  • Rushewar Ramukan Hako Ma’adinai Ta Kashe Mutane 32 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango
  • Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon
  •  Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran
  • IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran
  • Lebanon za ta shigar da kara a kan Isra’ila a MDD game da gina Katanga a iyakarta
  • Ma’ariv: Netanyahu Yana Tsoron Hukuncin  Da Kotu  Za Ta Yanke Akansa