Isra’ila : Netanyahu na shan suka bayan ya nemi afuwar Qatar
Published: 30th, September 2025 GMT
Jami’an Isra’ila da dama da suka hada da Ministoci masu tsattsauran ra’ayi irin su Itamar Ben-Gvir da Bezalel Smotrich, sun soki Firaminista Benjamin Netanyahu kan neman gafarar Qatar bayan harin da gwamnatin Tel Aviv ta kai kan shugabannin Hamas a kasar a ranar 9 ga watan Satumba.
Netanyahu ya nemi uzurin ne a wata ganawa tsakaninsa da shugaban Amurka, lokacin da Netanyahu ya kira firaministan Qatar, inda ya bayyana cewa Tel Aviv ta yi nadamar harin da aka kai ta sama.
Kiran da Netanyahun ya yi ta wayar tarho ya jawo suka daga jami’an Isra’ila, ciki har da minista mai tsatsauran ra’ayi Itamar Ben-Gvir, wanda ya kira harin “mai muhimmanci.”
A cikin wani sako a shafin X, Ben-Gvir ya sake nanata ayyana kungiyar Hamas a matsayin “kungiyar ta’addanci,” yana mai kiran Qatar a matsayin “kasa mai goyon bayan ta’addanci.”
Shi ma Ministan Kudi Bezalel Smotrich ya yi Allah wadai da uzurin na Netanyahu, yana mai kiransa da “abin kunya.”
A cewar jaridar Jerusalem Post ta Isra’ila, Smotrich ya sanya wa Netanyahu “jajayen layuka” da yawa kafin ganawarsa da Trump.
Tsohon ministan yakin Isra’ila, Avigdor Liberman, shugaban jam’iyyar masu tsattsauran ra’ayi ta Yisrael Beytenu, ya kira uzurin da Netanyahu ya yi a matsayin abin da ba za a taba mantawa da shi ba.
Harin da Isra’ila ta kai a ranar 9 ga watan Satumba ya kashe akalla jami’an Hamas biyar da ke Doha, babban birnin Qatar, da kuma wani jami’in tsaron Qatar.
A yayin kiran, an bayar da rahoton cewa, Netanyahu ya “tabbatar wa da” firaministan Qatar cewa Tel Aviv ba za ta sake kai irin wadannan hare-hare ba kan kasar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araghchi ya gana da sakatare janar na MDD September 30, 2025 Madagascar : Shugaba Rajoelina ya sanar da korar daukacin gwamnatinsa September 30, 2025 Adadin Hada-hadar Kasuwancin Kasashen Waje Ta Iran Takai Dala Biliyan 54 A Cikin Wata 6 September 30, 2025 Janar Safavi: matukan jirgen Isra’ila 16 ne suka a harin makami mai linzami na Iran a lokacin yaki September 30, 2025 Trump: Za mu goyi bayan Netanyahu idan Hamas ba ta amince da kudirinmu ba September 30, 2025 Iran: An zartar da hukuncin kisa a kan wani babban dan leken asirin Isra’ila September 30, 2025 Axios: Netanyahu ya nemi afuwar Qatar kan harin da Isra’ila ta kai a kan Doha September 30, 2025 Larijani: Iran a shirye take don tallafawa Lebanon da gwagwarmaya a kowane mataki September 30, 2025 Takunkumin makamai na Turai ya haifar da mummunar illa ga tattalin arzikin sojojin Isra’ila September 30, 2025 Kungiyar Yan Gudun Hijira Na Kasar Noway Tace Akwai Babbar Damuwa Game Shiru Kan Gaza September 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Netanyahu ya
এছাড়াও পড়ুন:
GGCSS Maga: Halin da iyaye ke ciki bayan sace ’ya’yansu
Iyayen ɗalibai ’yan mata 25 ’yan bindiga sace ɗakunan kwanansu a Jihar Kebbi sun bayyana irin tashin hankali da suka shiga bayan abin da ya faru.
“Ita kaɗai gare ni,” in ji Malam Muhammad Maga, mahaifin Nafisa, wadda ita kadai ya haifa, kuma take cikin ɗaliban da ’yan bindiga suka sace a makarantar.
Malam Muhammad wanda idanunsa ke cike da ƙwalla ya ce, “Roƙona Allah Ya sa a dawo min da ita lafiya, ita kaɗai gare ni. Ina roƙon Gwamna Idris ya taimaka a dawo mana da su. Mun san ƙoƙarin da yake yi a fannin tsaro a tsawon shekara biyu da ya yi a kan mulki.”
Shi ma Malam Aliyu Yakubu, ɗaya daga cikin iyayen ɗaliban da aka sace, ya ce, “’Yata na cikin ɗaliban da aka sace daga ɗakin kwanansu a safiyar Litinin, gaskiya ni da sauran iyaye muna cikin tashin hankali.
Za mu ceto ’Yan Matan GGCSS Maga cikin ƙoshin lafiya — Gwamnan Kebbi Sace Ɗalibai: Gwamnatin Tinubu ba ta shirya kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga ba — Amnesty Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno“Babban abin da nake tsoro shi ne kada abin ya zama irin na Makarantar ’Yan Mata ta Gwamantin Tarayya ta Birnin Yauri, inda yaran da aka sace suka shafe sama da shekara biyu a hannun ’yan bindiga
Muna rokon Gwamnatin Jihar Kebbi da Gwamnatin Tarayya su yi duk mai yiwuwa su ceto mana ’ya’yan mu”
Aminiya ta ruwaito cewar da asubahin ranar Litinin ne ’yan bindiga suka yi ta harbe-harbe a iska sa’annan suka kutsa cikin Makarantar sakandaren ’Yan Matan Gwamnati ta Musamman (GGCSS) da ke garin Maga a Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu a Jihar Kebbi, suka yi abin gaba da ɗalibai 25.
’Yan bindigar sun ci karensu babu babbaka, ba tare da wani ƙalubale ba, in banda Mataimakin Shugaban Makarantar, Malam Hassan Yakubu Makuku, wanda ya yi ƙoƙarin hana su tafiya da ɗaliban, amma suka harba shi har lahira, suka yi abin gaba da yaran.
Makarantar GGCSS Maga ta kasance a rufe na kimanin shekaru biyar saboda tsaron irin garin GGSS Birnin Tauri a zamanin gwamnatin da ta gabata ta Abubakar Atiku Bagusu, sai ’yan shekarun baya aka buɗe ta, inda aka girke jami’an tsaro.
Wani mahaifi da ’yarsa A’isha take cikin ɗaliban da aka sace, ya ce, wani mazaunin garin ne ya fara sanar da shi cewa A’isha tana cikin yaran da aka sace, “Amma ban gaskata ba, sai da na zo makarantar na iske iyaye na ta koke-koke. Roƙona ga gwamnati shi ne ta taimaka ta ceto maka ’ya’yanmu.”
Kawai Altine, wanda shi ma ’yan bindiga sun sace ’yarsam ya ce, “Na miƙa komai ga Allah, kuma na yi imanin cewa Allah Zai dawo mana da ita nan ba da jimawa ba. Roƙona kawo shi ne gwamnati da jami’an tsaro kada su yi ƙasa a gwiwa, wajen bi sawu domin gano yaran namu.”
Wani shugaban al’umma a yankin, Malam Rabi’u Abubakar, ya ce harin ya girgiz al’ummar yankin, musamman iyayen ɗalibai.
Ya ce, “Muna da dalilin yin baƙin ciki, saboda sun tafi mana da ’ya’ya, kuma suka kashe mana Malam Yakubu Makuku, saboda ya nemi kada su ɗauki yaran. Haƙiƙa wannan babban rashi ne.”
Kakakin Gwamnan Jihar Kebbi, Abdullahi Idris Zuru, ya shaida wa Aminiya cewa an turo ƙarin jami’an tsaro daga Abuja zuwa jihar domin su taimaka a aikin da ake yi na nema da kuma ceto ɗaliban.
Tun da farko Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta tabbatar da harin, tare da sanar da cewa tuni jami’an tsaro da mafarauta suka fara aikin ceto ɗaliban.
Aminiya ta ruwaito cewa Gwamna Jihar Kebbi, wanda labarin harin ya sa shi gaggawar yanke ziyarar aiki da ya kai Abuja, ya yi wata ganawa da iyayen ɗaliban, inda ya ba su tabbacin yin duk mai yiwuwa tare da jami’an tsaro domin kuɓutar da yaran.
Karo na biyu ke nan da ’yan bindiga suka kutsa cikin makarantar kwana ta ’yan a Jihar Kebbi suka yi garkuwa da gomman dalibai — na farko shi ne a Makarantar ’Yan Mata ta Gwamantin Tarayya da ke Birnin Yauri.