Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Babban Taro Kan Shawarar Samar Da Ci Gaban Duniya
Published: 24th, September 2025 GMT
Jiya Talata 23 ga wata ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya halarci babban taro kan shawarar samar da ci gaba ga duniya baki daya, tare da gabatar da jawabi a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York na kasar Amurka.
A gun taron da kasar Sin ta dauki nauyin shiryawa, firaminista Li ya ce, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar raya duniya baki daya a wajen babban taron MDD a shekara ta 2021, shawarar da ta mayar da hankali kan muradun daukacin bil’adama.
Mahalarta taron daban-daban, sun goyi bayan manyan shawarwarin duniya guda hudu da shugaba Xi ya gabatar, gami da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, tare da nuna babban yabo ga dimbin nasarorin da aka samu don inganta hadin-gwiwa a fannin aiwatar da shawarar samar da ci gaban duniya, da maraba da sabbin matakan hadin-gwiwar sassan kasa da kasa da suka shafi fasahar kirkirarriyar basira ta AI da kasar Sin ta gabatar. Har wa yau, bangarori daban-daban sun nuna cewa, ra’ayi da matakan kasar Sin sun dace da manufofin kundin tsarin mulkin MDD, kuma ya kamata a aiwatar da ra’ayin cudanyar sassa daban-daban, da kyautata tsarin shugabancin duniya, da taimakawa samar da ci gaba dake nuna juriya ga bangarori daban-daban, da kiyaye muradun kasashe daban daban, musamman kasashe masu tasowa. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: samar da ci gaba
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi
Bugu da kari, Amurka ta bayyana a fili cewa batun sauyin yanayi shi ne mafi girman yaudara da aka yi a tarihin dan Adam, kuma ta fice daga “Yarjejeniyar Paris” sau biyu, wanda hakan ya yi mummunar illa ga kokarin al’ummun duniya na kyautata yanayin duniya, kana ta zama babban cikas ga hadin gwiwar duniya a fannin magance sauyin yanayi.
Geng Shuang ya kuma bayyana cewa, a kan batun magance sauyin yanayi, abun da al’ummar duniya ke bukata shi ne dunkulewa da hadin gwiwa, ba zargi da dora laifi kan wasu ba. (Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA