2025-12-01@22:30:00 GMT
إجمالي نتائج البحث: 519
«Jam iyyar LP»:
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ya koma jam’iyyar ADC ne saboda ita kaɗai yake gani za ta iya ceto Najeriya daga matsalolin tsaro da na tattalin arziki da take fama da su. Yayin ƙaddamar da ofishin jam’iyyar a Jihar Taraba ranar Asabar, Atiku duk da a baya ya kasance a jam’iyyar...
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nahiyyar Afrika (CAF) ta fitar da jerin alƙalan wasa da masu kula da na’urar VAR a gasar cin kofin Nahiyyar Afrika ta 2025, amma babu ɗan Najeriya ko ɗaya. A sanarwar da hukumar ta fitar, ta ayyana alƙalan wasa 28 da masu kula da VAR 14 daga ƙasashe daban-daban. Ƙasar Japan...
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sauka sheƙa daga jam’iyyar SDP zuwa jami’yyar haɗaka ta ADC. Komawar El-Rufai jam’iyyar ADC a hukumance wani mataki ne da ake ganin zai kawo sabon salo a siyasar adawa wajen ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a Zaɓen 2027. An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane...
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi, a matsayin babban rashi ga al’umma. Gwamnan ya bayyana malamin a matsayin jagoran haɗin kai, zaman lafiya, da fahimtar juna tsakanin Musulmi da mabiya addinai daban-daban. ’Yan sanda sun gano harsasai 210 a kan titin Zariya-Funtuwa Allah Ya yi wa...
Shugaban kungiyar Ansar Allah a Yemen, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya aika da sakon ta’aziyya ga Sakatare Janar na Hezbollah, Sheikh Naim Qassem, kan shahadar babban kwamandan dakarun kungiyar Haitham Ali al-Tabtabai da abokansa. Huthi ya jaddada cewa laifin da aka aikata a kansu, tare da hare-haren da ake kai wa Lebanon da Zirin Gaza, yana...
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya karɓi katin kasancewa ɗan jamʼiyyar ADC a hukumance. Atiku wanda ya yi wa jam’iyyar PDP takarar kujerar shugaban ƙasar Zaɓen 2023, ya karɓi katin ya yi rajistar zama tabbataccen ɗan jam’iyyar ADC a mazaɓarsa ta Jada da ke jihar Adamawa. Jarumin fina-finan Indiya Dharmendra ya rasu Slot na...
Babban magatakardar Majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani ya mika ta’aziyyar shahadar daya daga cikin kwamandojin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Haisam al-Tabtabai wanda ya yi shahada a jiya Lahadi sanadiyyar harin Haramtacciyar Kasar Isra’ila. Dr. Ali Larijani ya wallafa sakon ta’aziyyar a shafina na X cewa; A daren shahadar Sayyidah Fatimah...
A yau Litinin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, zai yankin kati domin shiga Jam’iyyar ADC a hukumance. Manyan hidiman Atiku sun shaida wa Aminiya cewa an kammala dukkan shirye-shirye domin yin rajistar Atiku a mazaɓarsa ta Jada 1 da ke Ƙaramar Hukumar Hada ta Jihar Adamawa. Atiku ya yi nuni da wannan mataki ne...
Shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya ce jam’iyyar APC ba ta da ƙarfin da zai kai ta ga samun nasara a 2027, sai dai idan ta jingina da tasirin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar NNPP ta jihar, Dungurawa ya ce APC a...
A Iraki an sanar da sakamakon karshe na zaben ‘yan majalisar dokoki da aka gudanar a ranar Talata data gabata. Sakamakon ya nuna cewa Jam’iyar Firaminista Mai Barin Gado Mohamed Shia al-Soudani ce ta sami rinjaye mai yawa a majalisar da kujeru 46, inda za ta rike kusan rabin kujerun, idan aka kwatanta da kasa...
Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suna ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon, da a yau Talata su ka kai wani hari a garin Bint-Jubail da ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya da kuma jikkatar wani. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya ambato ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon tana cewa; Birnin na Bint...
An ba wa hamata iska a Hedikwatar Jam’iyyar PDP da ke Abuja a tsakanin bangarorin da ke hamayya da juna. Fadan ya barke ne bayan bangarorin sun halarci ofishin domin gudanar da tarukansu daban-daban a safiyar Talata. Idan ba a manta ba, bangaren Ministan Abuja, Nyesom Wike, wadanda uwar jam’iyyar ta dakatar a yayin babban...
“Lokacin da Wike, Makinde, Ugwuanyi, Ikpeazu da Ortom suka kafa G5, bana are da su. Amma duk da haka, Wike abokina ne sosai. Lokacin da PDP ta samu matsala Wike ne ya yi ƙoƙarin tallafa mata,” in ji Anyanwu. Ya ƙara da cewa Wike bai fice daga PDP ba. Anyanwu ya kira taron gangamin PDP...
Rushewar ramukan hako ma’adinai ta kashe ma’aikata 32 a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Akalla ma’aikatan hakar ma’adinai 32 ne suka mutu a ranar Asabar sakamakon zaftarewar ƙasa a wani ma’adinan cobalt a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, yayin da ake ci gaba da neman waɗanda har yanzu ba a same su ba a yankin. Zaftarewar ƙasa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matsayar doka ta zama babbar abun tattaunawa a Najeriya yayin da jam’iyyar PDP ta gudanar da taron ta na kasa duk da mabanbantan hukunce hukunce daga kotuna biyu. Umarnin kotu guda yana goyon bayan taron, ɗayan kuwa ya haramta shi gaba ɗaya. Wadannan hukunce hukunce ba baiwa...
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce gwamnati ce ke da alhakin samar da tsaro da haɗin kai a Jihar Filato da kuma Najeriya baki ɗaya. Ya ce babu wata ƙasa da za ta shigo don kawo zaman lafiya na dindindin a Najeriya, face ’yan ƙasa sun haɗa kai. ’Yan Bindiga A Kano: Sanusi II...
“A shekaru goma da suka gabata, ayyukan ta`addanci da tashe-tashen hankula daga masu tsattsauran ra`ayi ya haifar da mummunan koma bayan tattalin arziki da na zamantakewar alummomin dake shiyyar, halin da daliban irin wadannan makarantu suke ciki yana bukatar kulawar gaggawa daga kungiyar ta ECOWAS, abin takaici irin wadannan makarantun allo suna daukar dalibai masu...
Gwamna Caleb Muftwang na Jihar Filato, ya ce ba da yawunsa jam’iyyarsu ta PDP ta kori Ministan Abuja, Nyesom Wike ba. Yayin da yake nisanta kansa daga matakin da PDP ta ɗauka na korar Wike daga jam’iyyar, ya yi gargaɗin cewa hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba. Fintiri ya yi watsi da...
An zaɓi tsohon Ministan Ayyuka na Musamman da Harkokin Gwamnati, Kabiru Tanimu Turaki, a matsayin sabon shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa a yayin babban taron jam’iyyar da aka gudanar a birnin Ibadan na Jihar Oyo a ranar Asabar. PDP ta ce Barista Kabiru Tanimu Turaki, ya yi nasarar ce akan Sanata Lado Ɗan Marke da...
Da yake magana da manema labarai, Ahmed ya ce ficewar ba za ta raunana jam’iyyar ba, amma dai, ya yi fatan alheri ga ‘yan jam’iyyar da suka fice. Ahmed ya ƙara da cewa, NNPP tana da ƙwarin gwiwar riƙe Kano da kuma lasheh kujera a Jigawa, Kaduna, da sauran jihohi. Ya kuma yi ikirarin...
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa, ya yi watsi da hukuncin da Jam’iyyar PDP ta yanke na korar Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, daga jam’iyyar. Aminiya ta ruwaito yadda PDP ta kori Wike, Sanata Samuel Anyanwu da tsohon Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, a yayin babban taron PDP da aka gudanar a Ibadan, Jihar...
Tsohuwar Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP, Iyom Josephine Anenih, ta ce jam’iyyar za ta sake yin ƙarfi idan shugabanninta suka cire girman kai suka mayar da hankali kan yi wa jama’a hidima. Ta bayyana haka ne yayin babban taron PDP da aka gudanar a Ibadan a ranar Asabar. PDP ta kori Wike, Fayose, Anyanwu da...
An haife ni a garin Kano, karamar hukumar Nasarawa, Giginyu, Mahaifana ‘yan Sakkwato ne. Na yi aure a Kano ina da yara na guda uku, namiji daya mata guda biyu. Na yi firamare da Sakandare, a garin Kano. Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma harkar fim? A baya ban taba jin zan yi...
Jam’iyyar PDP ta kori Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose da tsohon sakataren jam’iyyar na ƙasa, Samuel Anyanwu. PDP ta yanke wannan hukunci ne a babban taron jam’iyyar da ake gudanarwa a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo. Gwamnati, UNICEF da ’yan jarida sun haɗa don yaƙar cututtukan da aka...
Bayan hukunci, kwamitin gudanarwa karkashin shugabancin Damagum ta dakatar da sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Samuel Anyanwu da mashawarcin shari’a na kasa, Kamaldeen Ajibade da sakataren shirye-shirye na kasa, Umar Bature na tsawon wata guda saboda zargin ayyukan da ke goyon bayan abin da ya saba wa jam’iyya. Bayan awanni 24, Anyanwu da magoya bayansa...
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sake hana jam’iyyar PDP gudanar da babban taronta na ƙasa da ta ke shirin yi. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Peter Odo Lifu, ya yanke hukuncin ne a ranar Juma’a. Mutfwang ya musanta raɗe-raɗin sauya sheƙa zuwa YPP Mutfwang ya musanta raɗe-raɗin sauya sheƙa zuwa YPP Ya ce taron...
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya ƙaryata jita-jitar ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa YPP. Rahotanni na yawo a shafukan sada zumunta cewa ya sauya sheƙa, amma mai magana da yawunsa, Gyang Bere, ya ce labarin ƙarya ne, tare da buƙatar jama’a su yi watsi da shi. Ɗalibar BUK ta samu kyautar motar N35m a gasar...
Tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya buƙaci jam’iyyar PDP da ta ɗage babban taronta da ta shirya gudanarwa tsakanin ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba a birnin Ibadan na Jihar Oyo. Saraki ya ce ci gaba da shirin gudanar da taron duk da irin umarnin dakatarwa da kotuna suka bayar zai ƙara ta’azzara...
Shugaban jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin da shugaban ma’aikatan fadar Shugaban ƙasa, Hon. Femi Gbajabiamila da Dr Abdullahi Umar Ganduje, sun ziyarci zauren Majalisar Wakilai ranar Alhamis domin shaida sauya sheƙar ƴan majalisa biyu daga NNPP zuwa APC. Ƴan majalisar da suka sauya sheƙar sun haɗa da Hon....
Sauran sun haɗa da: Hon. Ibrahim Adamu Sarki a jam’iyyar PDP daga shiyya ta biyu sai , Nazifi Jibrin Muhammad na jam’iyyar PDP daga shiyya ta biyu da Haruna Dogo Mabo na.jamiyya NNPP daga shiyya biyu sai Honorable Isah Dan Maryam na PRP daga shiyya ta biyu da , Honarabul Isaac Auta Zankai na jam’iyyar...
A jiya Talata ne dai MDD ta yi kira da a gudanar da bincke akan kashe-kashen da aka yi sanadiyyar zaben da aka yi a watan karshe. Wannan kiran na MDD ta zo ne a daidai lokacin da mahukuntan kasar ta Tanzania su ka tuhumi wasu daruruwan mutane da cin amanar kasa saboda Zanga-zangar kin...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja November 7, 2025 Siyasa Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha November 4, 2025 Labarai “Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri...
Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Birnin Kano da Kewaye, Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi, ya bayyana ficewarsa a hukumance daga jam’iyyar NNPP. Ƙoƙ8 inda ya danganta hakan da rikicin shugabanci da ke kara tsananta a cikin jam’iyyar. PDP ta sha alwashin gudanar da babban taronta duk da umarnin kotu Abdulmumin Jibrin ya koma APC wata...
Jam’iyyar (APC) a ƙarƙashin kungiyar Wamban Shinkafi ta jihar Zamfara, ta bayyana goyon bayanta ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar shugabancin ƙasa guda ɗaya na jam’iyyar a zaben 2027. Wannan sanarwar ta fito ne daga wanda ya kafa kungiyar kuma jigo a jam’iyyar APC a Zamfara, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi, yayin...
Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana kudurinta na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da babban taronta na kasa da aka tsara a yi a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba. Hakan na zauwa ne duk da sabon umarnin kotun tarayya da ke hana ta ci gaba da shirya taron. Yadda muka daƙile yunƙurin tsige...
Ministan Harkokin Wajen Iran Sayyed Abbas Araghchi, ya ce masana’antar nukiliya yanzu ta zama babban fanni kuma tana kara samun ci gaba cikin sauri a fannoni daban-daban. Sabanin yadda ake ganin cewa wannan masana’antar ta takaita ne ga tace uranium, ya kara da cewa ana gudanar da ayyuka da dama da suka shafi fannoni daban-daban...
Shugabannin jam’iyyar APC a matakin unguwanni 35 da sakatarorinsu a faɗin Jihar Kuros Riba, sun nemi a tsige shugaban jam’iyyar na jihar, Mista Alphonsus Eba, bisa zargin badaƙala da kuɗaɗen jam’iyya da kuma nuna son kai wajen gudanar da harkokin jam’iyyar. Wannan buƙatar ta fito ne a cikin wata sanarwa da shugabanni da sakatarorin jam’iyyar...
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da sabon umarnin dakatar da Babban Taron Jam’iyyar PDP da ake shirin gudanarwa ranar 15 da 16 an watan nan a Ibadan, fadar Jihar Oyo. Umarni na uku masu karo da juna ke nan da kotu ta bayar kan taron babbar jam’iyyar adawar mai cike da ruɗani.
Tawagar lauyoyin Trump ta ce an ɓata masa suna da mutunci, inda ta bayyana cewa BBC ta yi hakan ne don siyasa. Trump ya taɓa shigar da ƙorafe-ƙorafe makamantan wannan a kan wasu manyan kafafen yaɗa labarai na Amurka, ciki har da ABC, CBS, da The New York Times, bisa zargin yaɗa labaran ƙarya a...
Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’il Baghaei yayi tir da Amurka game da rashin kyakkawar nufi ko muhimmantar da tattunawa da ake Magana akai, yace sanarwar da shugaban Amurka trump ya fitar a baya bayan nan na amicewa da hannu Amurka wajen kai mata hari ya nuna cewa ta ma shiga cikin harin soji...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa yanzu babu abin da ya ragewa kasashen yamma banda su amince da Iran a matsayin cibiyar kimiyyar masa’antu ta shirin nukiliya na zaman lafiya. Ministan ta fadi hakan ne a wata ziyara da ya kai hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar, inda ya bayyana...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da aikin gina hanya da kudinta ya kai Naira Biliyan 14 a Karamar Hukumar Malam Madori, wanda ke nuna jajircewar gwamnatinsa wajen bunkasa ababen more rayuwa1 karkashin shirin sabunta kudurori na gwamnatin tarayya wato “Renewed Hope Agenda.” A yayin taron kaddamarwar, an kuma...
Kamfanin dillancin labarun kasar Lebanon ya ambaci cewa, Mutum daya ya kwanta dama, sadaniyyar harin wani jirgin sama maras matuki na HKI akan wata mota a garin al-yasariyyah,dake gundunar Saida, a kudancin kasar. Majiyar tsaro ta fada wa kafafen watsa labaru cewa, jirgin saman maras matuki ya harba makamai masu linzami guda 3 ne akan...
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙiru da Bebeji daga Jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC, wata biyu bayan jam’iyyar NNPP ta dakatar da shi. A safiyar Litinin ɗin nan ɗan majalisar ya sanar da sauya sheƙarsa tare da magoya bayansa daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC tare da goyon bayan neman...
Babban jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, Alhaji Sani Adamu Yarin Fika, ya sauya sheƙa zuwa APC da ke mulki a jihar. Yarin Fika, ya sanar da sauya sheƙarsa a wani biki da aka gudanar a Damaturu, inda ya ce ya yanke shawarar shiga APC ne saboda irin ƙoƙarin da Gwamna Mai Mala Buni...
Babban jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, Alhaji Sani Adamu Yarin Fika, ya sauya sheƙa zuwa APC da ke mulki a jihar. Yarin Fika, ya sanar da sauya sheƙarsa a wani biki da aka gudanar a Damaturu, inda ya ce ya yanke shawarar shiga APC ne saboda irin ƙoƙarin da Gwamna Mai Mala Buni...
Charles Soludo na jam’iyyar All Progressives Grand Alliance wato APGA, ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Anambra wanda aka yi a jiya Asabar, 8 ga watan Nuwamba. Baturen zaɓen jihar, Farfesa Edoma Omoregie ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon zaɓen da ke babban birnin jihar, Awka a safiyar yau Lahadi. Yaran Bello Turji...
Sunana Abdulhamid Ado (Danbayaro): Inna lillahi wa inna ilaihirraju’un. Na ji ba dadi na ji komai sai da ya tsaya min har tsahon lokaci, abun ba zai musaltuba, sai dai kawai mu ce Allah ya ji kan Mal. Nata’ala. Mutum ne mai barkwanci, ga zumunci na gaske, ba a yin gulma da shi, baya...
Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; Da safiyar yau Asabar ne jiragen yakin HKI su ka kai hari a garin Bint Jubail dake kudancin kasar. Harin na jiragen Sahayoniya dai ya kasance ne a kusa da aibitin Salah-Gandur da hakan ya yi sanadin jikkatar wasu mutane biyu. Wasu yankunan da jiragen sama...
