2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a jika baya – Atiku
Published: 2nd, October 2025 GMT
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya ce idan bukatar hakan ta taso, zai iya janye burinsa na takarar shugaban kasa a 2027 don mara wa matashi baya.
Atiku, wanda jigo ne a haɗakar jam’iyyun adawa ta ADC, ya bayyana hakan ne a wata hirarsa da BBC Hausa a ranar Laraba.
NAPTIP ta kama mahaifin da ke ƙoƙarin safarar ’yarsa zuwa Iraƙi ci-rani Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya su daina yi wa ƙasar mummunan fataDa aka tambaye shi ko zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027, sai ya ce lokacin tattauna hakan bai yi ba.
Ya ce, “Lokacin hakan bai yi ba tukuna. Idan lokaci ya yi, zan yanke shawara. Abin da muke yi yana da amfani ga kasa.
“In har matashi ya kayar da ni, zan amince da sakamakon kuma in mara masa baya da dukkan zuciyata, in kuma ba shi shawarwari. Jam’iyyarmu tana samun karbuwa,” in ji Atiku.
Ya ƙara da cewa babban abin da ya fi mayar da hankali a kai yanzu shi ne karfafa kawancen haɗakar ADC.
“Jam’iyyarmu tana ba matasa da mata muhimmanci. Wannan shi ne babban burinmu,” in ji shi.
Atiku ya bukaci matasa da su shiga harkar siyasa da kuma neman mukaman siyasa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Takara
এছাড়াও পড়ুন:
Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku
Babban jirgin ruwan yaki mai dakon sojojin kasa da sauran kayan yaki da ake amfani da su a kan-tudu samfurin 076 irinsa na farko a kasar Sin mai suna Sichuan, ya koma tashar jiragen ruwa da ke birnin Shanghai da misalin karfe 5 na yamma a yau Lahadi, bayan kammala gwajinsa na farko a teku.
Gwajin jirgin na kwanaki uku ya kunshi gwada ayyukan na’urar da ke sarrafa tafiyar jirgin da na’urorin lantarkinsa da sauran kayayyakin aiki, inda aka samu sakamakon da ake sa ran samu.
Kasancewarsa sabon jirgin ruwan yaki na zamani na rundunar sojojin ruwa ta ‘yantar da jama’ar kasar Sin, jirgin ya kunshi sabbin fasahohin majaujawar mayen karfe mai aiki da lantarki, da fasahohin rike jiragen sama bayan saukarsu, wadanda ke ba shi damar daukar jirage masu tsayin fukafuki, da jirage masu saukar ungulu da sauran kayan yaki masu aiki a cikin ruwa da kuma doron kasa. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA