Leadership News Hausa:
2025-10-13@17:53:38 GMT

Yaushe Mourinho Zai Koyar Da Kwallon Kafa A Kasashen Jamus Da Faransa?

Published: 28th, September 2025 GMT

Yaushe Mourinho Zai Koyar Da Kwallon Kafa A Kasashen Jamus Da Faransa?

An kori Lage daga Benfica duk da wasa daya ya yi rashin nasara a dukkan karawa a kakar nan, kuma Mourinho ya gaji kungiyar da take ta shida a teburin Primeira Liga da tazarar maki biyar tsakani da Porto mai jan ragama.

Ya fara da wasa ranar Asabar, inda suka ziyarci ABS, wadda take ta 17 a kasan teburin a babbar gasar kasar Portugal.

Mourinho, dan kasar Portugal wanda ya bai wa kansa sunan ”the special one’ a 2004 zai ziyarci tsohuwar kungiyarsa wadda ya koyar sau biyu a tarihi wato Chelsea a Champions League da Benfica za ta buga ranar 30 ga watan Satumba.

Jerin kungiyoyin da Mourinho ya koyar Porto (2002-04) Primeira Liga biyu, Champions League, Uefa Cup da

Portuguese Cup Chelsea (2004-07 da 2013-15) Premier League uku, FA Cup da League Cup uku. Inter Milan (2008-10) Serie A biyu, Champions League da Coppa Italia

Real Madrid (2010-13) La Liga, Copa del Rey, Manchester United (2016-18) Europa League da League Cup. Tottenham (2019-21) Bai ɗauki kofi ba. Roma (2021-24) Conference League. Fenerbahce (2024-25) Bai ɗauki kofi ba.

Mourinho ya yi suna a kungiyar FC Porto tsakanin shekara ta 2002 zuwa 2004, bayan lashe kofi guda shida har da Champions League da ya dauka a kakar wasa ta 2003 zuwa 2004.

Tun bayan da ya bar kasarsa ta haihuwa a 2004, Mourinho ya horar da kungiyoyin Chelsea karo biyu da Inter Milan da Real Madrid da Manchester United da Tottenham Hotspur da Roma da kuma Fenerbahce. Bayan ya koma Benfica, Mourinho ya ce “babu daya daga cikin manyan kungiyoyin” da ya yi aiki tun da ya bar Benfica da ya ji a matsayin “girmama, alhaki ko kwazo”. Bayan da aka kori Lage ranar Talata, shugaban kungiyar, Rui Costa ya ce sabon kociyan da zai dauka sai mai tarihin lashe kofuna.

Hakan yana nufin Mourinho ne ya dace, bayan da ya lashe kofi 21 na baya-bayan nan shi ne Conference League a Roma a 2022, da kuma Champions League biyu da gasar rukuni-rukuni guda takwas a kasashe hudu, amma dai kofi na karshe da ya dauka shi ne Europa League.

Benfica za kuma ta je buga wasa a Newcastle United, sannan kuma za ta karbi bakuncin tsohuwar kungiyar da Mourinho ya horar Real Madrid a dai Champions League.

Benfica ta kare a mataki na biyu a teburin babbar gasar Portugal a bara, kuma rabonta da kofin tun 2022 zuwa 2023. Mourinho ya fuskanci takaddama a Turkiya, musammam yadda ya yi ta caccakar alkalan wasa na kasar, lamarin da ya kai ya samu rashin jituwa da su.

A watannin baya cikin watan Nuwamba, Mourinho ya zargi Fenerbahce da kin gaya masa gaskiya kan gogewar alkalan wasan kasar, amma ya ce Atilla Karaoglan shi ne wanda ya fi gwanninta lokacin da ya yi rafli da suka doke Trabzonspor.

Mourinho ya shigar da Galatasaray kara a watan Fabrairu, bayan da suka zarge shi da yin kalaman wariyar launin fata. Lokacin da aka nada Mourinho kociyan Fenerbahce a watan Yunin shekarar 2024, miliyoyin magoya baya sun yi kyakkyawan fata saboda suna ganin an dauki daya daga cikin fitattun masu horarwa a duniya wanda zai kawo karshen kamfar lashe kofi a shekaru da yawa da cewar kungiyar za ta taka rawar gani a gasar zakarun Turai.

Sai dai nan take mafarkin ya kasa zama gaske. Fiye da shekara daya, wannan mafarkin sai ya koma takaici. Mourinho ya kasa yin nasara a wasan hamayya na Istanbul derby kuma ya kasa daukar kofin babbar gasar kasar.

Yanzu dai ya koma kungiyar da ta fitar da Fenerbahce a wasannin cike gurbin shiga gasar Champions League ta bana. Wasu magoya bayan Fenerbahce na jin an yaudare su. Ba kawai Mourinho ya yadda su ba, ya kuma dauke su shashashai. Wasu suna ganin banda kungiyar kwallon kafa ta Benfica da Mourinho ya koma, kasar da ake ganin nan gaba zai iya komawa domin koyar da kwallon kafa ita ce kasar Saudiyya, idan har ya bar kungiyar Benfica, amma kuma har yanzu bai koyar da kungiya ba a kasar Faransa da Jamus. A shekarun baya an taba alakanta Mourinho da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen da Jamus kafin daga baya kungiyar ta dauki Pep Guardiola, sannan a Faransa ma shugabannin kungiyar Paris Saint German zun yi zawarcinsa a lokacin da kungiyar take neman mai koyarwar da zai jagorance ta zuwa lashe gasar cin kofin zakarun turai da suke nema ruwa a jallo.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Mourinho ya

এছাড়াও পড়ুন:

Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya ASUU a ranar Lahadi ta sanar da shiga yajin aiki na makonni biyu, wanda zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, a duka jami’o’in gwamnati na ƙasar.

Shugaban ƙungiyar Farfesa Chris Piwuna ne ya sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja, a ranar Lahadi.

Asuu ta ce yajin aikin na gargaɗi ne bayan cikar wa’adin da suka bai wa gwamnatin Najeriya a watan Satumban da ya gabata.

“Yajin aikin gargadin zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, kamar yadda aka amince a taron NEC na ƙarshe,” kamar yadda Piwuna ya bayyana.

RN

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kungiyar ‘Yan Dako Ta Kasa Ta Nada Sabon Sakatare A Jigawa
  • Yaƙin Gaza: Hamas da Isra’ila sun fara sakin fursunoni
  • Yaushe Lamine Yamal Zai Lashe Kyautar Ballon d’Or?
  • Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
  • Zuwa Kofin Duniya: Za A Yi Ta Ta Kare A Nahiyar Afirka
  • Rashin Amincewa Da Kasashen Yamma Yana Haifar Da Sabon Tunani Kan Huldar Kasa Da Kasa
  • Afirka Ta Kudu Ta Ce Babu Wata Makarkashiya A Mutuwar Jakadanta A Kasar Faransa
  • Ayyukan Da Suka Sauya Fuskar Zamfara A Ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal
  • Ammar Hakim Ya Gargadi Kasashen Yamma Da su Kiyayi Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidan Kasar.
  • Faransa Da Jamus Da Kuma Birtaniya Sun Bayyana Aniyarsu Ta Ganin An Farfado Da Tattauna Da Iran