Aminiya:
2025-11-18@12:50:32 GMT

Jiya na yi barci mai daɗi bayan na soke faretin samun ’yancin kai

Published: 2nd, October 2025 GMT

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce soke faretin zagayowar ranar ’yancin kai karo na 65 da sojoji ke yi ya ba shi damar yin lafiyayyen barci da kuma yin kyakkyawan kari a ranar Laraba.

Aminiya ta rawaito cewa Gwamnatin Tarayya ta soke bikin da aka shirya domin murnar cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai a ranar Laraba, daya ga watan Oktoba.

Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya su daina yi wa ƙasar mummunan fata Rashin Tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewacin Najeriya

Sanarwar ta fito ne daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya a ranar Litinin.

“Gwamnatin Tarayya na sanar da soke bikin zagayowar ranar ‘yancin kai da aka shirya domin murnar cikar ƙasar shekara 65 a ranar Laraba, 1 ga Oktoba. Sokewar ba ta rage muhimmancin wannan rana ba,” in ji sanarwar da Daraktan Labarai da Hulɗa da Jama’a, Segun Imohiosen, ya sa wa hannu.

Da yake jawabi a ranar Laraba yayin ƙaddamar da cibiyar Wole Soyinka da aka gyara, wadda a da ake kira National Arts Theatre a Legas, Tinubu ya ce ya yi barci lafiya bayan soke bikin.

Shugaban ya ce ya yi yamma mai daɗi a wajen ƙaddamar da cibiyar da Babban Bankin Najeriya (CBN) tare da haɗin gwiwar Bankers’ Committee suka ɗauki nauyin gyaranta.

Ya ce taron ya sauya abin da ya kira da salo ɗaya na faretin sojoji da ake yi a ranar ‘yancin kai.

“Barka da zagayowar ranar ‘yancin kai karo na 65. Wannan ya sauya salon maimaita faretin sojoji da duk abin da ke tattare da shi. Da aka soke wannan shiri, na samu yin lafiyayyen barci, na yi kyakkyawan kari, sannan na jira wannan yamma. Kuma yammar ta yi kyau,” in ji shi ga mahalarta taron.

Tinubu ya isa wajen taron da misalin ƙarfe 6:24 na yamma domin bikin buɗe wurin tarihin da aka gyara.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yancin kai a ranar Laraba

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo

 

 

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka November 15, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Yi Taka-tsantsan Da Batun Yankin Taiwan  November 15, 2025 Daga Birnin Sin Jakadan Sin A Japan Ya Bayyana Matukar Adawa Da Kalaman Firaminista Takaichi Dangane Da Kasar Sin November 15, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Najeriya ta Fara tattaunawa da Amurka kan zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi
  • Sace Ɗalibai: Gwamnatin Tinubu ba ta shirya kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga ba — Amnesty
  • Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai 
  • Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo na biyu a jere
  • NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar
  • Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95
  • Ɗan Najeriya ya kashe mahaifinsa, ya yanki ƙannensa da wuƙa a Amurka
  • AU ta sake nanata cewa “Babu kisan kare dangi a arewacin Najeriya
  • Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo
  • Mahara sun kashe matan aure sun ƙona gidansu a Kano