Fira Ministan Faransa ya yi murabus kwana guda bayan kafa gwamnati
Published: 6th, October 2025 GMT
Firaministan ƙasar Faransa, Sebastien Lecornu, ya yi murabus daga muƙaminsa kwana guda bayan ya kafa gwamnatinsa.
Fira Minista Sebastien Lecournu ya sanar da ajiye mukaminsa ne a safiyar Litinin ɗin nan bayan ya yi wata da Shugaba Emmanuel Macron.
Ya yi murabus ne washegarin da ya kafa majalisar ministocinsa domin tafiyar da gwamnati, kuma ƙasa da wata guda bayan Shugaba Macron ya naɗa shi a kujerar.
A jiya Lahadi ne ya sanar da sunayen mambobin sabuwar majalisar ministocinsa inda ya naɗa sabbin muƙamai, amma ya bar wasu da dama a kan kujerunsu, lamarin da bai yi wa ’yan adawa daɗi ba.
Zargin takardun bogi: Jami’ar Nsukka ba ta taɓa ba ni takardar digiri ba — Minista ’Yan bindiga sun kashe wani mutum sun sace hakimi a Kwara NAJERIYA A YAU: ‘Halin Kunci Ya Sa Muke Zama A Baca A Abuja’Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa (AFP) ya ruwaito cewa, sanarwar ajiye aikin ta zo e a yayin da ake sa ran a yau Litinin Lecornu, wanda tsohon ministan tsaron Faransa ne, zai jagoranci zaman majalisar ministocinsa ta farko.
Kawo yanzu ahi ne minista na biyar da Macron ke naɗawa cikin shekaru biyu a yayin da Faransa ke fuskantar gagarumar dambarwar siyasa.
Fadar shugaban ƙasar Faransa ta sanar a safiyar yau Litinin cewa Shugaba Macron ya amince da murabus ɗin babban na hannun daman nasa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Faransa Fira Minista Murabus
এছাড়াও পড়ুন:
ASUU ta tsunduma yajin aikin mako 2
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya.
Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja.
Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaroYa ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025.
ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025.
A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da yajin aikin, don haka dukkanin malamai za su daina aiki a lokacin yajin aiki.
Wannan yajin aikin na zuwa ne duk da cewa har yanzu gwamnati da ASUU na ci gaba da tattaunawa don warware matsalolin da suka daɗe suna fama da su.
Wasu daga cikin matsalolinsu sun shafi batun albashi, kuɗaɗen alawus-alawus, da kuma yarjejeniyar da aka cimma tun shekarar 2009 tsakanin ɓangarorin biyu.
Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya bayyana a ranar Laraba cewa gwamnati na matakin ƙarshe na tattaunawa da ASUU da sauran ƙungiyoyi don warware matsalolinsu.
Ya kuma ce gwamnati ta riga ta fitar da Naira biliyan 50 don biyan haƙƙoƙin malaman da suka cancanta, yayin da aka sake sakin wasu Naira biliyan 150 a kasafin kudin 2025 domin biyan buƙatun jami’o’i.