An Tashi Dutse Hannun Riga Tsakanin PANGASsSAN da Matar Mai Ta Dangote
Published: 30th, September 2025 GMT
Ƙungiyar manyan ma’aikatan kamfanonin iskar gas da fetur PENGASSAN ta ce tana nan kan bakarta na ci gaba da yajin aiki bayan kasa samun maslaha tsakaninta da matatar Dangote.
Bangarorin biyu sun tashi baran-baran a tattaunawar da suka yi karkashin jagorancin ministan kwadago na Najeriya Mohammed Dingyadi a ranar Litinin.
A ranar Litinin ne ƙungiyar PENGASSAN ta shiga yajin aiki na sai baba ta gani saboda matakin matatar Dangote na korar wasu ma’aikatanta kimanin 800.
Babu dai wata sanarwa daga ɓangaren Matatar Dangote bayan tattaunawa da kungiyar PENGASSAN, amma a sanarwar da ta fitar ranar Lahadi ta ce ta sallamar ma’aikatan ne a wani mataki na ƙoƙarin daidaita tsarin aikin matatar.
Matatar Dangote ta kuma bayyana matakin yajin aikin PENGASSAN a matsayin rashin aiki da doka da kokarin zagon kasa ga Najeriya da al’ummarta.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno
Mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun kashe wani babban kwamandan rundunar sojin Najeriya bayan wani harin kwantan ɓauna da aka kai wa tawagarsa a hanyar Damboa–Biu da ke Jihar Borno.
Lamarin ya faru ne bayan da tawagar sojojin tare da dakarun haɗin gwiwa na Civilian Joint Task Force (CJTF) suka kai wani samame a yankin, inda suka gamu da harin ba-zata na ’yan ta’adda.
’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a Gombe Hauhawar farashi ya ƙara raguwa a Nijeriya — NBSKwamandan, wanda daga baya aka bayyana sunansa a matsayin Brigade Commander M. Uba, shi ne ya jagoranci rundunar da ta kai ɗauki ga wasu sojoji da suka yi ɓatan hanya kafin su faɗa tarkon mayaƙan ISWAP.
PRNigeria ta ruwaito cewa, kafin rasuwarsa, kwamandan ya aike da wani bidiyo ga manyansa yana bayyana irin nasarar da tawagarsa ta samu a wani farmaki da suka kai.
Sai dai bayan haka ne ISWAP ta bibiyi wurin da yake ta katse sadarwa, sannan ta kama shi.
Rahotanni sun ce mayaƙan sun kama shi ne da ransa, inda bayan sun yi masa tambayoyi, daga bisani kuma su kashe shi.
Da farko dai rundunar sojin Najeriya ta ce kwamandan yana cikin ƙoshin lafiya bisa hujjar bidiyon da ya aika yana tabbatar da irin nasarar da suke samu.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin ƙasa, Laftanar Kanar Appolonia Anele, ta bayyana batun cafke kwamandan nata a matsayin “ƙazon kurege”, tana mai cewa duk da “harbe-harbe masu tsanani” da suka fuskanta daga mayaƙan yayin dawowarsu daga sintiri a gefen Sambisa, an yi nasarar tsira da kwamandan.
Sanarwar ta tabbatar da mutuwar sojoji biyu da jami’an sa-kai biyu a harin, amma ta ce kwamandan ba ya cikin waɗanda aka kama.
Sai dai daga bisani, wasu rahotanni na PRNigeria da jaridar PREMIUM TIMES sun tabbatar da cewa mayaƙan ISWAP sun kama kwamanda ne bayan ya yi ɓata hanya yayin guje wa harin farko.
ISWAP ta yi iƙirarin kashe kwamandanA wata sanarwa cikin harshen Larabci da ISWAP ta wallafa ranar Litinin a jaridarta mai suna Amaq, ta nuna hoton kwamandan a lokacin da ya ke hannunta, yana fama rauni har jini na zuba a kafarsa.
Ƙungiyar ta ce: “Mun kama kwamandan rundunar Najeriya bayan ya tsere daga harin Wajiroko, daga nan muka yi masa tambayoyi sannan muka kashe shi.”
Ƙungiyar ta kuma yi wa rundunar sojin Najeriya gugar zana, tana mai bayyana bayanan farko da ta fitar a matsayin “ƙarya tsagwaronta da ke tabbatar da gazawarta.”
Kawo yanzu dai Rundunar Sojin Najeriya ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba, amma majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa ana gudanar da bincike kan yadda aka bar kwamandan cikin haɗari bayan tserewa daga harin farko.