Iran ta yi gargadi game da makirce-makircen Isra’ila na kawo cikas ga tsaron yankin
Published: 2nd, August 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na da burin kawo cikas ga harkokin tsaro a yankin, yana mai kira ga daukacin kasashen yankin da su yi taka tsantsan wajen tunkarar irin wannan makirci.
Araghchi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da mataimakin firaministan Hadaddiyar Daular Larabawa kuma ministan harkokin wajen kasar Sheikh Abdullah bin Zayed Al Nahyan a ranar Juma’a.
Ministan na Iran ya ce gwamnatin Isra’ila ta saba da dabi’a ta son kai da rashin bin doka da oda.
Manyan jami’an diflomasiyyar Iran da na Hadaddiyar Daular Larabawa sun tattauna kan sabbin abubuwan da ke faruwa a yankin musamman halin da Falasdinu ke ciki.
Har ila yau Araghchi da Nahyan sun yi musayar ra’ayi game da hanyoyin inganta dangantakar kasashnsu a fannonin siyasa, tattalin arziki da kasuwanci daban-daban.
Sun jaddada bukatar yin amfani da damar da kasashen biyu suke da ita wajen fadada alaka a cikin batutuwan da suka shafi moriyar kasashen biyu.
A watan Yulin da ya gabata ne dai sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Akbar Ahmadian da kuma mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa Tahnoun bin Zayed Al Nahyan suka bukaci hadin kan kasashen yankin don tabbatar da tsaro a yankin baki daya, bayan shafe kwanaki 12 na hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila da Amurka suka kai wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Firayim Ministan Senegal Ya Bayyana Sabon Shirin Farfado Da Tattalin Arzikin Kasar August 2, 2025 Gaza: Witfkoff ya yi rangadi a wuraren da Amurka ta kafa domin tallafi August 2, 2025 ‘Yan Sudan dama na komawa gida bayan gudun hijira na tsawon shekaru a Masar August 2, 2025 Iran Ta Ce Batun Neman Dakatar Da Tace Uranium Zai Rusa Duk Wata Jarjejeniya Da Ake Son Cimmawa August 1, 2025 Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Watsi Da Duk Wani Zarge-Zargen Neman Bata Mata Suna August 1, 2025 Limamin Sallar Juma’a Ya Ce; Iran Zata Mayar Da Isra’ila Kufai Idan Ta Sake Kai Hari Kan Kasarta August 1, 2025 Kasar Slovenia Da Haramta Tura Makamai Zuwa Haramtacciyar Kasar Isra’ila August 1, 2025 Kasar Spain Ta Bayyana Abin Da Ke Faruwa A Gaza A Matsayin Abin Kunya Ga Bil’Adama August 1, 2025 Iran ta yi watsi da zargin gwamnatocin turai na yunkurin kashe wasu mutane a kasashensu August 1, 2025 Mali da Rasha sun tattauna kan hadin gwiwar makamashi August 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta yi watsi da zargin gwamnatocin turai na yunkurin kashe wasu mutane a kasashensu
Iran ta yi watsi da zarge-zargen marasa tushe balantana makama da kasashen yammacin duniya ke yi a kanta, kan cewa tana yunkurin kashe wasu mutane a cikin kasashensu.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya yi Allah wadai da ikirarin da ya kira na kin jinin Iran da Amurka da Canada da wasu kasashen Turai goma sha biyu suka yi a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a wannan Alhamis.
Ya ce wannan batu a fili wani yunkuri ne na karkatar da hankulan jama’a daga batun da ya fi daukar hankali a wannan lokaci, wato kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Palastinu da ta mamaye.
Ya kara da cewa, “Amurka, Faransa, da sauran kasashen da suka sanya hannu kan wannan sanarwa ta kin jinin Iran, tilas ne su kansu su dauki alhakin ayyukan da suka saba wa dokokin kasa da kasa, yayin da suke goyon baya da daukar nauyin ‘yan ta’adda da kungiyoyi masu tayar da hankali, domin yin amfani da hakan ajen cimma manufofinsu na siyasa.
Baghaei ya tabo batun hare-haren wuce gona da iri da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran a watan Yuni da kuma kisan kiyashin da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza, da kuma yin shiru da kasashen yammacin duniya 14 da suka rattaba hannu kan sanarwar suke yi a kan manyan laifukan yaki da Isra’ila take aikatawa a kan idanun dukkanin al’ummomin duniya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Mali da Rasha sun tattauna kan hadin gwiwar makamashi August 1, 2025 Afirka ta Kudu na shirin daukar matakan kauce wa tasirin harajin Amurka August 1, 2025 Haaretz: Sojojin Isra’ila 7 ne suka kashe kansu a watan Yuli August 1, 2025 Gaza: Mutane Da Dama Sun Yi Shahada A Yau Wasu Kuma Sun Jikkata August 1, 2025 Kungiyar AU Ta Yi Watsi Da Kafa Gwamnatin Adawa Da Kungiyar RSF Ta Yi A Sudan August 1, 2025 Shugaban Kasar Iran Zai Ziyarci Pakistan A Gobe Asabar August 1, 2025 Habasha Ta Kaddamar Da Shirin Shuka Bishiyoyi Miliyan 700 A Rana Daya August 1, 2025 Sayyid Abdulmalik Husi: Taimakon Da Ake Jefawa Gaza Ta Sama Yaudara Ce August 1, 2025 Amurka Ta Kakabawa Jami’an Gwamnatin Falasdinawa Takunkuman Hana Shiga Amurka July 31, 2025 Ministan Harkokin Wajen Siriya Yana Rasha Don Bude Sabon Shafi Tsakaninsu July 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci