PDP ta mutu murus a Kano — Shugaban NNPP
Published: 2nd, August 2025 GMT
Shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya ce farin jinin jam’iyyar adawa ta PDP ya dusashe a jihar.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martanin da wasu jam’iyyun adawa suka yi, wajen zargin gwamnatin jihar da rashin bayyana yadda ta ke kashe kuɗaɗen da aka ware wa ilimi, lafiya, da gine-gine.
Dungurawa, ya ce waɗannan zarge-zargen siyasa ce kawai, ba su da tushe ko makama.
Ya ce waɗanda ke sukar gwamnati su ne suka gaza lokacin da suka yi mulki a Kano.
“Da farko, muna gode musu da suka amince muna aiki. Amma muna tunatar da su cewa sun yi shekara takwas suna mulki amma ba su bar wani abin a-zo-a-gani ba,” in ji Dungurawa.
Ya zargi gwamnatocin baya da yin ayyukan da ba su da tasiri, ba tare da duba buƙatun al’umma ba.
“Misali duba gadar ƙasa da suka yi a Dangi. Ba ta da wani amfani. Babu cunkoso a wajen da zai sa a gina irin wannan. Kawai sun zuba kankare ne ba tare da wata manufa ba,” in ji shi.
Dungurawa, ya ce a ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, gwamnatin NNPP ta mayar da hankali kan muhimman ayyuka kamar gyaran tituna da gina gadoji don sauƙaƙa zirga-zirga a jihar.
“Yanzu haka, ramuka ƙadan za ka ga ni a titunan Kano. Titunanmu sabbi ne, alamomin titi a bayyane suke, fitilun titi suna aiki.
“Wannan yana nuna cewa masu kishin jihar sun karɓi ragamar mulki,” in ji shi.
Ya kuma kare yadda gwamnati ke biyan fansho, inda ya bayyana cewa an riga an biya Naira biliyan 27 daga cikin Naira biliyan 48 da gwamnatin jihar ta gada a matsayin bashi.
“A cikin shekara biyu kacal, mun biya Naira biliyan 27 sannan an biya biliyan 22, kuma za a biya wata biliyan biyar a watan Disamba.
“Wannan ya nuna irin yadda muke tafiyar da gwamnati da gaskiya,” in ji shi.
Game da maganar da wasu ‘yan adawa ke yi cewa jam’iyyunsu na ƙara ƙarfi, Dungurawa ya yi watsi da hakan.
“Wasu daga cikinsu ko a gidajensu ba za a goyi bayansu ba. PDP ba ta da wani ƙarfi. A zahirin gaskiya, mutuwa ta ke ƙara yi. Shugabanninta ba su da haɗin kai kuma son kansa yake yi,” in ji Dungurawa.
Bayan taɓo batun haɗakar ADC, Dungurawa ya ce hakan na nuna rikicin da ke cikin PDP.
“Idan har ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP yana shirin komawa wata jam’iyya, me hakan ke nunawa?
“Yana nuna cewa jam’iyyar ba ta da tsari ko jagoranci. ‘Yan siyasa masu kishin ƙasa sun riga sun bar jam’iyyar tuntuni,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa za ta ci gaba da shirin gudanar da babban taronta wanda za a yi a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba a Ibadan da ke Jihar Oyo.
Tun da farko, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta hana jam’iyyar gudanar da taron, inda ta ce PDP ta karya dokokinta na cikin gida.
’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi Kotu ta dakatar da gudanar da babban taron PDPMai shari’a James Omotosho, wanda ya jagoranci shari’ar, ya umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), da kada ta karɓi ko ta wallafa sakamakon taron har sai PDP ta cika dukkanin sharuɗan da doka ta tanada.
Sai dai a cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar da yammacin ranar Juma’a, kakakinta na ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce jam’iyyar ba za ta dakatar da shirin gudanar da taron ba.
Ya bayyana hukuncin kotun a matsayin tauye haƙƙin dimokuraɗiyya a Najeriya.
Ologunagba, ya ce hukuncin ba zai hana PDP ci gaba da shirye-shiryenta na zaɓen sabbin shugabanni da za su jagoranci jam’iyyar na tsawon shekaru huɗu masu zuwa ba.
Ya yi nuni da cewa Kotun Ƙoli ta tabbatar da cewa jam’iyyu na da ’yancin tafiyar da harkokinsu na cikin gida.
“PDP na kira ga mambobinta da shugabanni a faɗin ƙasar nan da su kuma ci gaba da shirye-shiryen babban taron jam’iyyar,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa jam’iyyar mai bin doka ce, kuma ta umarci lauyoyinta da su ɗaukaka ƙara game da hukuncin kotun.