Firayim Ministan Senegal Ya Bayyana Sabon Shirin Farfado Da Tattalin Arzikin Kasar
Published: 2nd, August 2025 GMT
Firayim Ministan Senegal Ousmane Sonko ya sanar da wani sabon shirin farfado da tattalin arzikin kasar, inda ya yi alkawarin samar da kudi “90% na aiwatar da wanann shirin ta hanyar albarkatun cikin gida da kuma kauce wa karbar bashi.
Sonko ya bayyana haka ne a lokacin da ake gabatar da wannan shiri a Dakar babban birnin kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
Ya kara da cewa “dole ne a yi amfani da kuma tattara albarkatun cikin gida don samar da mafi yawan kudaden da kasa take bukata.”
Shirin wanda ke da nufin daidaita harkokin kudi na kasar da ke yammacin Afirka, wadda ta fara hako mai da iskar gas a bara, ya zo ne a daidai lokacin da Senegal ke fuskantar kalubalen kudi da kuma tarin basusuka.
Kasar Senegal dai na fama da boyayyen bashi na biliyoyin daloli daga gwamnatin da ta shude, lamarin da ya sanya hukumar lamuni ta duniya IMF ta dakatar da shirinta na lamuni ga Senegal.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza: Witfkoff ya yi rangadi a wuraren da Amurka ta kafa domin tallafi August 2, 2025 ‘Yan Sudan dama na komawa gida bayan gudun hijira na tsawon shekaru a Masar August 2, 2025 Iran Ta Ce Batun Neman Dakatar Da Tace Uranium Zai Rusa Duk Wata Jarjejeniya Da Ake Son Cimmawa August 1, 2025 Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Watsi Da Duk Wani Zarge-Zargen Neman Bata Mata Suna August 1, 2025 Limamin Sallar Juma’a Ya Ce; Iran Zata Mayar Da Isra’ila Kufai Idan Ta Sake Kai Hari Kan Kasarta August 1, 2025 Kasar Slovenia Da Haramta Tura Makamai Zuwa Haramtacciyar Kasar Isra’ila August 1, 2025 Kasar Spain Ta Bayyana Abin Da Ke Faruwa A Gaza A Matsayin Abin Kunya Ga Bil’Adama August 1, 2025 Iran ta yi watsi da zargin gwamnatocin turai na yunkurin kashe wasu mutane a kasashensu August 1, 2025 Mali da Rasha sun tattauna kan hadin gwiwar makamashi August 1, 2025 Afirka ta Kudu na shirin daukar matakan kauce wa tasirin harajin Amurka August 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mali da Rasha sun tattauna kan hadin gwiwar makamashi
Wakilan kasashen Mali da Rasha sun gudanar da taron farko na kwamitin hadin gwiwa na gwamnatocin kasashen biyu, karkashin jagorancin ministan tattalin arziki da kudi na kasar Mali Husseini Sanou, da ministan makamashi na kasar Rasha Sergey Tsivlev, inda suka tattauna kan “hadin gwiwa a fannin makamashi, musamman wajen yin amfani da makamashin nukiliya domin ayyukn farar hula.
Taron ya samu halartar wakilan “manyan kamfanonin makamashi na Rasha da ma’aikatun gwamnatin tarayya,” kamar yadda ya zo a cikin wata sanarwa da ma’aikatar makamashi ta Rasha ta fitar a shafinta na intanet, a cewar kafar yada labarai ta African Readings.
Bangarorin biyu sun tattauna kan fagagen da suka yi alkawarin yin aikin hadin gwiwa a fannin hakar albarkatun kasa, binciken sararin samaniya, tsaro ta yanar gizo, da kuma aikin gona,” baya ga hanyoyin da za a bi wajen samar da kayayyakin masarufi a kasar Mali da kasashen Sahel, wanda ke da muhimmanci wajen tabbatar da dorewar tsarin ayyukan hadin gwiwa,” a cewar sanarwar ma’aikatar makamashi ta kasar Rasha.
A ziyarar da ya kai birnin Moscow a watan Yunin da ya gabata, shugaban majalisar rikon kwarya a kasar Mali, Janar Assimi Goita, ya amince tare da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin kan kafa kwamitin hadin gwiwa na gwamnatocin Mali da Rasha.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Afirka ta Kudu na shirin daukar matakan kauce wa tasirin harajin Amurka August 1, 2025 Haaretz: Sojojin Isra’ila 7 ne suka kashe kansu a watan Yuli August 1, 2025 Gaza: Mutane Da Dama Sun Yi Shahada A Yau Wasu Kuma Sun Jikkata August 1, 2025 Kungiyar AU Ta Yi Watsi Da Kafa Gwamnatin Adawa Da Kungiyar RSF Ta Yi A Sudan August 1, 2025 Shugaban Kasar Iran Zai Ziyarci Pakistan A Gobe Asabar August 1, 2025 Habasha Ta Kaddamar Da Shirin Shuka Bishiyoyi Miliyan 700 A Rana Daya August 1, 2025 Sayyid Abdulmalik Husi: Taimakon Da Ake Jefawa Gaza Ta Sama Yaudara Ce August 1, 2025 Amurka Ta Kakabawa Jami’an Gwamnatin Falasdinawa Takunkuman Hana Shiga Amurka July 31, 2025 Ministan Harkokin Wajen Siriya Yana Rasha Don Bude Sabon Shafi Tsakaninsu July 31, 2025 Kananan Yan Wasan Dabben Gargajiya Na Iran Sun Zama Zakara A Gasar Wannan Shekara July 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci