2027: APC Da ADC Na Gwagwarmayar Neman Samun Goyon Bayan Mutanen Arewa
Published: 2nd, August 2025 GMT
A yanzu haka dai ratotannin sun tabbatar da cewa APC da ADC suna gogayya wajen neman samun goyon bayan mutanen arewa kafin babban zaɓen 2027 ya ƙariso.
A ranar 1 ga Yuli, manyan ƴan adawa da suka hada da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi da dan takarar shugaban ƙasa a APC a 2023, Rotimi Amaechi, da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun gabatar da ADC a matsayin hadakar jam’iyyar adawa domin ƙalubalantar Tinubu a 2027.
Shugabannin ADC sun ci gaba da yin ƙoƙari don samun goyon bayan mutanen arewacin Nijeriya da sauran yankuna tun bayan buɗe jam’iyyar.
A taron, Mark ya buƙaci shugabannin arewacin Nijeriya da su daina dabi’ar zargi da kuma amincewa na suna da alhakkin ƙalubalen da yankin ke fuskanta.
Ya ce, “Wannan wata dama ce da kuma girmamawa kasancewa a gabanku yau don magana kan batun halin da muke ciki a yanzu da kuma sauya makomarmu. Ina kira a gare ku mu yi gaggawar samun haɗin kai da ƙarfafa dangantaka a matsayin hanyar magance ƙalubalen da yankinmu ke fuskanta.
“Arewacin da muka sani ya kasance wata ƙasa ce mai ɗimbin tarihi da albarkatun ma’adinai da ƙasa noma da al’adu masu yawa da kuma ƙarfin tasiri.
“ɗuk da wadannan albarkatu, muna fuskantar ƙalubale masu yawa da suka hada da rashin tsaro da talauci da rikice-rikicen ƙabilanci da addinai da rarrabuwar kai a siyasa da matsalolin zamantakewar da na tattalin arziki. Wadannan ƙalubale ba su faru a dare daya ba kuma ba za su kau ba har sai mun hada kai wajen daukar matakin da ya dace.
“ɗole ne mu yarda da cewa mu ne masu gina matsalolinmu, dole ne mu daina zargin kawunanmu idan muna son samun mafita ɗorewar yankinmu.”
Tsohon shugaban majalisar dattawa ya ƙara bayyana cewa rarrabuwar kawuna ta hana wa arewacin ƙasar nan ci gaba, yayin da halin ko-in-kula da rashin daukan mataki ya ƙara zurfafa rarrabuwar da ta riga ta wanzu.
“ƙalubalen da ke fuskantar arewacin Nijeriya suna da alaƙa da juna. Rashin tsaro yana janyo ficewar masu zuba jari, wanda hakan ke ƙara tsananta talauci. Talauci yana jawo aikata muyagun laifuka. ƙabilanci na rage ƙarfin haɗin kanmu wajen neman kyakkyawan shugabanci. Rugujewar harkokin siyasa na tabbatar da cewa ba za a samu ingantaccen ci gaba a yankinmu. Wannan ba arewar da muka gada ba ne,” in ji ADC.
ɗon dawo da martaban yanki, Mark ya jaddada cewa akwai buƙatar matanen arewa su sake tunani da yin Nazari wajen daukan matakan da suka dace.
Ya kira ga dukkan mutanen arewa su dauki wannan a matsayin babban nauyi na haɓaka haɗin kai wajen inganta yankin maimakon zama a rarrabe.
A nasa ɓangaren, Lawal ya bayyana cewa gamayyyar ƙungiyar tuntuɓa kan harkokin siyasa ta arewa ta amince da ADC a matsayin jam’iyyar da ta iya tunkarar APC a zaɓen 2027.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya ya ce wakilai daga dukkanin jihohin arewa 19 sun cimma yarjejeniya cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ba ta wani yuƙuri wajen magance matsalolin yankin.
Ya ce masu ruwa da tsaki daga arewacin ƙasar nan sun amince su tashi tsaye su yada saƙonsu wajen samn haɗin kan mutane da cimma matsaya kan zaɓe mai zuwa.
A martaninsa, daraktan yada labarai na APC ya ce jam’iyyar mai mulki ba ta damu da abin da ake kira da suna hadakar jam’iyya ba.
Ibrahim ya bayyana cewa Shugaba Tinubu na jagorantar gwamnati mai cike da samun goyon bayan dukkan mutanen Nijeriya.
Ya ce, “Jam’iyarmu ta APC, tana samun goyon bayan mutanen arewacin Nijeriya da kuma dukkan sauyan yankunan Nijeriya gaba daya, sai dai wadanda ba su gamsu ba da suka kafa jam’iyyar ADC a yanzu.”
Ya bayyana cewa APC ta jajirce wajen sabunta fata ga ƴan Nijeriya kuma yana nuna tabbacin cewa jam’iyyar za ta ƙara samun nasara a 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Arewa samun goyon bayan mutanen arewa arewacin Nijeriya bayyana cewa
এছাড়াও পড়ুন:
Matsalar Tsaro: Ko Sabbin Shugabannin Rundunar Soji Za Su Kawo Sauyi?
Shugabannin Rundunar tsaro da Tinubu ya sallama sun hada da shugaban rundunar tsaro ta kasa Janar Christopher Musa da shugaban sojojin ruwa, Emmanuel Ikechukwu Ogalla da shugaban sojojin sama Hassan Abubakar.
Wadanda suka maye gurbin su da idanu ya koma kan hobbasar kwazon da za su nuna su ne shugaban rundunar tsaro Olufemi Oluyede, shugaban sojojin kasa Waidi Shaibu, shugaban sojojin ruwa Idi Abbas da shugaban sojojin sama S.K Aneke sai kuma shugaban rundunar leken asiri, EAP Undiendeye wanda ya ci-gaba da rike kujerar sa.
Yan Nijeriya sun jima suna kukan duk da kwarewa da gogewar jami’an sojojin Nijeriya da irin makuddan kudaden da gwamnati ke kashewa a sha’anin tsaro a kowace shekara amma matsalar kullum gaba- gaba take kara yi.
Yankuna da dama a Nijeriya musamman a Arewa- Maso- Yamma, Arewa- Maso- Gabas da Arewa ta tsakiya sun zama lahira kusa a bisa ga yadda barayin daji ke garkuwa da mutane, kone garuruwa da yi wa jama’a kisan kare dangi.
Gagarumar matsalar wadda tuni ta zama tamkar ruwan dare a tsayin shekaru ta ci dimbin rayuka da dukiyoyin al’umma ba adadi ba tare da samun gagarumar nasarar dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma ba.
Masana tsaro sun bayyana ra’ayoyi mabambanta kan sauye- sauyen. Wasu na ganin cewa sabbin jini za su iya kawo canji, yayin da wasu suka yi gargadin cewa sauya shugabanni kadai ba zai wadatar ba idan ba a yi gyaran tsari ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA