Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Dimokuraɗiyyar Nijeriya Daga Rugujewa
Published: 2nd, August 2025 GMT
Bayan shekar 22 da kuɓutar da Nijeriya daga mulkin soja, dimokuraɗiyya na ci gaba da fama da rauni mai tsanani. Alamun cutar sun bayyana ne a cinikin baragurbin wakilai (delegates), amfani da kuɗin ƙasa da aka wawure ta hanyar haram wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe, maƙudan kuɗin da ake ware wa Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC), ƙarancin yawan masu kada ƙuri’a, sayen ƙuri’u a bainar jama’a, tashin hankali yayin zaɓe, da kuma yaɗuwar fargaba, musamman a tsakanin matasa, cin amana na ƴan siyasa, canja sheƙa da zaɓaɓɓu ke yi, da dai sauran makamantansu.
Asalin matsalar ita ce, rashin shiga cikin gudanar da gwamnati a siyasance (eɗclusion) na masu gaskiya da riƙon amana, matasa, mata, masu fama da naƙasa, ƴan gudun hijira da jam’iyyun da ke da ƙaramin ƙarfi, duk sun kasance a wajen filin.
Wannan ba kawai rashin adalci ba ne, har ma ya saɓa wa kundin tsarin mulki, kuma barazana ce ga zaman lafiya da ci gaban ƙasa. Idan ka duba, za ka fahimci cewa; dimokuraɗiyyarmu na hannun wasu tsirarun mutane da shugabannin jam’iyyu masu ƙarfi, wadanda suka killace matasa da sauran ƴan Nijeriya daga samun damar shiga siyasa ko a saurare su ko la’akari da tasu gudunmawar. ɗimokuraɗiyyar cikin gida a jam’iyyu, abin dariya ne kawai, domin an mayar da zaɓe na cikin gida zuwa ciniki, wato ba ni kuɗi ga ƙuri’a. Inda a wani ɓangaren kuma, INEC na fuskantar ƙalubalen rashin ƴanci da rashin ƙwarin guiwar aiwatar da dokokinta.
Har ila yau, ƴan gudun hijira da sauran al’umma masu rinjaye ana ci gaba da ware su daga zaɓe. Haka nan, hukumar zaɓen jihohi, musamman yadda aka gani a zaɓen ƙananan hukumomi a Kaduna da Bauchi, sun zama wani kwafi da ya ci mutuncin dimokuraɗiyya. Wannan ya saɓa wa sassa da dama na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (Sashe 14(2)(a), 15(1), 40, 153(1)(f), 221, 318(1), da Jadawali na Bakwai), da ɗokokin ƙungiyar Tarayyar Afirka da kuma Majalisar ɗinkin ɗuniya.
Yadda Wannan Tsari Na Matasa Zai Taimaka Wajen Ceto Siyasarmu:
1-Yarjejeniya Ta ƙasa ɗon Siyasa Mai Inganci (National Charter for Inclusion): A samar da wata Yarjejeniya ta haɗin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Matasa ta ƙasa, ƙungiyar Gamayyan Jamíyyun Siyasa (IPAC), Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC), ƙungiyoyin Fararen Hula da Majalisar Matasa ta Nijeriya. Wannan yarjejeniya za ta kafa ƙa’idoji da dokokin da za su tilasta dimokuraɗiyya a cikin jam’iyyu, tabbatar da adalci wajen zaɓuɓɓuka da kuma bai wa dukkannin jam’iyyun da suka shiga zaɓe damar ba da gudunmuwa wajen shugabanci a kowane mataki da kuma bai wa matasa, mata, ƴan gudun hijira da kowa da kowa damar ƴancin tsayawa takara cikin adalci.
2- Sauyi Mai Zurfi Ga Jam’iyyu da Tsarin Zaɓe:
Ya zama wajibi jam’iyyu su buɗe ƙofa. A kafa dokar da za ta tilasta duk mai son tsayawa takara gabatar da “Tsarin Ayyuka” (Project Plans) kafin hawa kujera, sannan ya fitar da “Rahoton ƙarshe” (End-of-Term Reports), bayan barin gado ko da kuwa zai koma kuwa. A daƙile kuɗin da ake nema marasa tushe daga masu neman takara, musamman na hukumomin zaɓen jihohi, (Misalin KAɗ-SIECOM). A tabbatar da cikakken amfani da Sashe na 7 na Kundin Tsarin Mulki da ɗokar Zaɓe ta 2022.
3- Runguman ɗimokuraɗiyyar ɗijital Hannu Biyu (ɗigital ɗemocracy):
A kafa “Cibiyar ɗimokuraɗiyyar ɗijital ta ƙasa (NɗɗH)” da za ta sa ido, bayar da rahoto kai tsaye, sa ido kan kuɗin yaƙin neman zaɓe da tantance tsarin jam’iyyu. Za ta kuma ba da damar samun ilimin siyasa ta hanyar wasanni da fasahar zamani domin ƙara fahimta, rage rashin sha’awa daga matasa, da bunƙasa ilimi da riƙon amana.
4- Ƙarfafa IPAC Youth da Shirye-shiryen Fadakarwa:
A ƙarfafa ɓangaren Matasa na IPAC (IPAC Youth ɗirectorate) daga matakin ƙasa har zuwa jihohi, ta hanyar samar da doka, kasafin kuɗi da kuma tsarin aiki. Sannan, a ɗora musu alhakin wayar da kan jama’a a faɗin ƙasar nan, musamman a tsakanin wadanda aka ware daga siyasa.
Me Za Mu Samu Idan An Bi Wannan Hanya? Za mu samu dimokuraɗiyya mai inganci da kuma tsabta, inda matasa, mata, masu fama da nakasa (PWɗs) da ƴan gudun hijira (IɗPs) za su samu bakin fada kuma a ji a cikin siyasa da shugabanci. Za a samu ƙarancin tashin hankali a lokacin zaɓe, raguwar sayen ƙuri’a da ingantaccen ilimi da wayewa a tsakanin jama’a. Za kuma a samu jam’iyyu masu gaskiya da amana da kuma shugabanci na ƙwarai da ci gaban ƙasarmu Nijeriya.
Matakan Aiwanar da Wannan Tsari:
Mataki na 1:
Rubuta NSPPC tare da dukkan masu ruwa da tsaki.
Mataki na 2: Kafa tsarin dubawa tsakanin INEC, IPAC da CSO.
Mataki na 3: ƙaddamar da NɗɗH da kayan aikin ilmantarwa.
Mataki na 4: Gyaran ɗokar Zaɓe, domin shigar da wadanan al‘amura da muka gabatar a sama da sauran buƙatu.
Kafin Mu Kammala: Makomar dimokuraɗiyyar Nijeriya na cikin hadari. Ba za mu iya ci gaba da kallon halin da ake ciki ba na rashin adalci, cin amana, zangon ƙasa ga ƙasa da al’úmarta.
Yazama wajibi mu yi amfani da ƙarfin matasa, domin ceto Nijeriya daga bakin kuraye. ƙirƙire-ƙirƙire da buƙatar riƙon amana, su ne maganin cutar da dimokuraɗiyyarmu ke fama da ita.
Wannan tsari nawa na zuwa ne daga gwanancewa da aiki da IPAC, shirye-shiyen fitar da saƙwanni ta ‘Bakondare Speaks’, wallafa rubuce-rubuce a manyan jaridu kamar su Premium Times, daily Trust, Guardian, Punch, Vanguard, Thisday , Leadership (A hausance da turanci)) da kuma shiga ayyukan siyasa masu tsafta da kuma alaƙa da ƙungiyoyi masu muhimmanci na siyasa.
Yanzu ne lokacin sauyi! Muryar matasa ya kamata ta koma tsakiya wajen tsara manufofi da aiwatar da su. Yakamata dimokuraɗiyyar Nijeriya ta amfani kowa da kowa ba wasu ba kawai!
Kafin rahoton ƙarshe na wannan taro ya isa ofishin Shugaban ƙasa ranar 12 ga Agusta, 2025 (Ranar Matasa ta ɗuniya), ina kira da babbar murya da fatan alheri ga duk dan Nijeriya da kuma dukkan wakilai da su rungumi wannan tsari. Ina kuma kira ga ƴan majalisa da masu zartarwa da su aiwatar da shi, domin ci gaban Nijeriya da kuma amfanin masu zuwa nan gaba. Yanzu ne lokacin daukar mataki na haƙiƙa da Jarumta! Allah ya yi mana albarka, ameen.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: ƴan gudun hijira Nijeriya daga Nijeriya da
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da fasinjoji a cikin wasu motocin bas Toyota guda biyu a titin Itobe zuwa Ajegwu-Anyigba a Ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi.
An samu rahoton cewa, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 5 na asubahi a tsakanin ƙauyukan Ojiwo’-Ajengo da Mamereboh da ke kan babbar hanyar.
Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasaAn ce masu garkuwa da mutanen sun yi amfani da wata tirela da aka kama wajen tare hanyar bayan shingen binciken jami’an tsaro, da ke kusa da wurin da lamarin ya faru.
Shedun gani da ido sun ce ɗaya daga cikin motocin bas ɗin mai lamba KG: KPA 622LG na kan hanyarta zuwa Abuja, tare da fasinjoji daga wata tashar mota a unguwar Ankpa da ke yankin Kogi ta Gabas.
Har yanzu ba a iya gano adadin fasinjojin da aka yi garkuwa da su ba zuwa yanzu, sai dai mun iya tabbatar da cewa ɗaya daga cikin motocin na ɗauke da fasinjoji ne daga yankin Ankpa, kamar yadda aka gano wasu takardu da wasu kayayyaki a wurin da lamarin ya faru suka bayyana.
“Motocin bas ɗin guda biyu suna kan hanyar Abuja ne a lokacin da suka ci karo da shingayen ’yan bindiga a safiyar ranar Alhamis. Dukkanin fasinjojin, ciki har da direban motocin bas ɗin biyu an yi awon gaba da su cikin daji,” in ji Unubi Ademu, wani mazaunin Achigili, a ƙauyen da ke maƙwabta.
Al’ummar yankin sun ƙara da cewa, jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji da mafarauta da kuma ’yan banga suna ƙoƙarin magance lamarin.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Kogi (PPRO), CSP William Aya bai amsa kira da saƙo ba lokacin da aka tuntuɓe shi har zuwa lokacin tattatara wannan rahoto.