Leadership News Hausa:
2025-11-18@09:04:14 GMT

Fim Na Nezha 2 Na Kasar Sin Ya Kara Samun Lambar Yabo

Published: 4th, October 2025 GMT

Fim Na Nezha 2 Na Kasar Sin Ya Kara Samun Lambar Yabo

Fim na Nezha 2 na kasar Sin ya kara samun lambar yabo. A gun bikin nune-nunen littattafan zanen hotuna na kasa da kasa na kasar Sin karo na 18 da aka kaddamar a jiya 2 ga wannan wata, fina-finai guda 10 ciki har da fim na Nezha 2, da The Legend of Hei 2, da Curious Tales of a Temple sun samu lambobin yabo na Golden Dragon na kasar Sin karo na 22.

Ya zuwa yanzu, fim na Nezha 2 ya samu kudin tikitin kallo Yuan biliyan 15.44 a duniya gaba daya, yawan kudin tikitin fim din da aka samu a kasashen waje ya kai Yuan miliyan 400. Fim din ya hau matsayi na farko na fim na kagaggun hotuna da ya fi sayar da tikitin kallo a duniya, kana ya shiga jerin sunayen fina-finai na duniya guda 8 dake kan gaba wajen sayar da tikitin kallo. (Zainab Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan

Kalaman tayar da husuma na firaministar Japan Sanae Takaichi, dangane da batun yankin Taiwan na kasar Sin, na ci gaba da shan suka da Allah wadai daga sassan kasa da kasa. Wani sakamakon kuri’un jin ra’ayin al’umma da kafar CGTN ta gabatar ya nuna yadda akasarin masu bayyana mahanga suka amince da cewa, matakin na Takaichi tsoma baki ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma akwai bukatar gaggauta sanya ido kan karuwar burikan wasu jagororin Japan masu tsattsauran ra’ayi, na ruguza odar kasa da kasa ta bayan yakin duniya na biyu.

Kaso 91.1 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin na ganin kamata ya yi Japan ta gyara tarihin ta’asar da ta aikata ta hanyar aiwatar da matakai na hakika, ta kuma martaba dukkanin ikon mulkin kai da kare kimar yankunan kasar Sin. Kazalika, kaso 88.5 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin sun soki lamirin yadda Japan ta yi karan-tsaye ga odar kasa da kasa ta bayan yakin duniya na biyu.

Bugu da kari, kaso 86.1 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin sun soki kalaman Takaichi, ganin yadda suka yi matukar keta tanade-tanade na hakika, dangane da batun yankin na Taiwan, da keta hurumin takardun siyasa hudu wadanda Sin da Japan suka daddade, wanda hakan ya yi matukar illata tushen alakar Sin da Japan.

ADVERTISEMENT

Har wa yau, kaso 88.9 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin sun yi Allah wadai da kalaman Japan, na yunkurin tsoma baki cikin batun Taiwan, da yi wa kasar Sin barazanar soji, suna masu cewa irin wadannan kalamai za su yi matukar barazana ga zaman lafiya da daidaito a shiyyar. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA  November 15, 2025 Daga Birnin Sin Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci November 15, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo November 15, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Alummar Kasar Ecodo Sun yi Watsi Da Batun Sake Dawo Da Sansanin Sojin Amurka A Kasar
  • Tawagar Wasan Wushu Ta Kasar Iran Ta Samu Lambobin Yabo 4 A Saudiya
  • Shugaban Nukiliyar Iran Yace Amurka Da Israila Sun Shiga Sabon Mataki Mai Hadari
  • Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30
  • Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya
  •  Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran
  • Lebanon za ta shigar da kara a kan Isra’ila a MDD game da gina Katanga a iyakarta
  • Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan
  • Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca
  • Jakadan Sin A Japan Ya Bayyana Matukar Adawa Da Kalaman Firaminista Takaichi Dangane Da Kasar Sin