Trump: Za mu goyi bayan Netanyahu idan Hamas ba ta amince da kudirinmu ba
Published: 30th, September 2025 GMT
Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a fadar White House jiya litinin cewa, yana fatan samun zaman lafiya mai dorewa a yankin gabas ta tsakiya.
Trump ya sanar da kaddamar da abin da ya kira “Ka’idojin Zaman Lafiya” a hukumance, tare da yin la’akari da abin da ya kira amincewar shugabannin kasashen Larabawa da na musulmi tare da tabbatar da goyon bayansu ga shirinsa na samar da mafita a zirin Gaza, in ji shi.
A cikin cikakkun bayanai kan shirin da Trump ya gabatar, za a saki dukkan fursunonin Isra’ila a zirin Gaza cikin sa’o’i 72 idan Hamas ta amince da shawarar. Shugaban na Amurka ya kuma bayyana cewa, shugabannin sun daura damara kan kawar da Hamas da kuma sauran kungiyoyi daga tafiyar lamarin Gaza bisa shirin da ya tsara.
Trump ya ce sojojin Isra’ila za su janye daga zirin a matakai, yana mai cewa “bangarorin za su amince da jadawalin ficewar Isra’ila.”
Trump ya yi barazanar cewa Isra’ila za ta samu cikakkiar dama domin ruguza Hamas idan kasashen Larabawa da na Musulunci suka gaza magance wannan batu. Ya kuma yi gargadin cewa Netanyahu zai samu cikakken goyon baya don yin duk abin da ya ga dama idan Hamas ba ta amince da shawararsa ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran: An zartar da hukuncin kisa a kan wani babba dan leken asirin Isra’ila September 30, 2025 Axios: Netanyahu ya nemi afuwar Qatar kan harin da Isra’ila ta kai a kan Doha September 30, 2025 Larijani: Iran a shirye take don tallafawa Lebanon da gwagwarmaya a kowane mataki September 30, 2025 Takunkumin makamai na Turai ya haifar da mummunar illa ga tattalin arzikin sojojin Isra’ila September 30, 2025 Kungiyar Yan Gudun Hijira Na Kasar Noway Tace Akwai Babbar Damuwa Game Shiru Kan Gaza September 29, 2025 Shugaban Iran: Yunkurin Durkusar Da Alummar Iran Bashi Da Maraba Da Mafarki. September 29, 2025 Kwamitin Tsaro A Majalisar Dokokin Iran Ta Gama Tsara Ficewar Kasar Daga NPT September 29, 2025 An Kashe Sojan HKI Guda A Harin Maida Martani A Yankin Yamma Da Kogin Jordan September 29, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Cewa Bukatun Amurka Daga Iran Ba Mai Yuwa Ba Ne September 29, 2025 Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Iran Yace SnapBack Baya Bisa Ka’ida September 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran
Dakarun kare juyin juya halin Musulinci na Iran, sun sanar da kwace wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran.
A cikin wata sanarwa da ta fitar IRGC ta ce rundunarta ta gaggawa ta fara bin diddigin jirgin ruwan dake dauke da tutar Tsibirin Marshall a ranar Juma’a da safe, bayan umarnin kotu na kwace kayan da yake dauke da.
A cewar sanarwar, jirgin yana dauke da tan 30,000 na sinadarai dangin mai dake kan hanyarsa ta zuwa Singapore.
“Tankor ya saba wa ka’idoji na daukar kaya ba tare da izini ba,” in ji sanarwar IRGC.
An gudanar da wannan aikin ne bisa doka da nufin kare muradun kasa da albarkatun Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
A ranar Juma’a, jami’an Amurka sun sanar da cewa dakarun kare Juyin Juya Halin Musulunci sun kama wani jirgin ruwa na Talara, da ke kan hanyarsa daga yankin Ajman na Hadaddiyar Daular Larabawa, zuwa Singapore.
Cibiyar Kula da Harkokin Ciniki ta Ruwa ta Burtaniya ta ba da rahoton kwace jirgin, inda ta amince cewa akwai yiwuwar “aikin gwamnati” ya tilasta wa jirgin Talara shiga cikin ruwan Iran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran : kasantuwar sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ce ga zaman lafiyar duniya November 16, 2025 Lebanon za ta shigar da kara a kan Isra’ila a MDD game da gina Katanga a iyakarta November 16, 2025 AU ta sake nanata cewa “Babu kisan kare dangi a arewacin Najeriya November 16, 2025 Falasdinu ta yi wasan sada zumunci a Spain November 16, 2025 Amurka Ta Yi Gwajin Makaman Nukiliya A Watan Ogusta November 15, 2025 Adadin Ma’adanin “Colbat” Da DRC Ta Bai Wa Duniya Ya Kai Ton 1,000 November 15, 2025 Ma’ariv: Netanyahu Yana Tsoron Hukuncin Da Kotu Za Ta Yanke Akansa November 15, 2025 An Bayyana Sunayen Kasashen Da Su Ka Fi Sayar Wa “Isra’ila” Man Fetur A Lokacin Yakin Gaza November 15, 2025 MDD: Mutane 100,000 Ne Su Ka Fice Daga Birnin Al-Fasher Na Kasar Sudan November 15, 2025 Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Yace Iran Ba za Ta Taba Mika Wuya Ga Duk Wata Barazana Ba November 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci