Jikamshi Zai Jagoranci Tsofaffin Ma’aikatan FRCN Zuwa PTAD Don Neman Biyan Haƙƙoƙi
Published: 20th, April 2025 GMT
Shugaban Ƙungiyar Tsofaffin Ma’aikatan FRCN, Alhaji Ibrahim Ahmad Jikamshi, zai jagoranci wata tawaga ta musamman domin ganawa da Babban Sakataren Hukumar PTAD kan muhimman batutuwa fansho da ta shafi tsofaffin ma’aikatan.
Alhaji Ibrahim Jikamshi dayake bayani a Kaduna, yace za a gudanar da wannan ganawa a cikin wannan mako domin tattaunawa kan wasu matsaloli da aka gano wajen biyan bashin da ake bin tsofaffin ma’aikatan shekaru da dama.
Ya tabbatar da cewa ƙungiyar tana ƙoƙari wajen shawo kan irin waɗannan matsaloli da suka dade ana fama da su, tare da fatan cewa hukumar PTAD za ta nuna gaskiya, rikon amana da kuma jajircewa wajen biyan hakkokin da suka rage.
Alhaji Ibrahim Jikamshi, wanda ya tunatar da matakin da shugaban ƙasa ya ɗauka a baya na biyan bashin da ake bin tsofaffin ma’aikata ta hanyar sakin biliyoyin Naira, ya nuna damuwa da cewa har yanzu wannan mataki bai haifar da gamsasshen sakamako ba ga waɗanda abin ya shafa.
SULEIMAN KAURA
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kwara Ta Horar Da Manoma Sama Da 500 Tare Da Basu Tallafi
Manoma sama da 500 daga gundumomi 15 na karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara sun samu horo kan kiwon awaki na zamani da kuma yadda ake samar da abincin dabbobi, a wani yunƙuri na rage yawan rikici tsakanin manoma da makiyaya tare da inganta rayuwar al’ummar karkara.
An gudanar da wannan horo a Idofian karkashin haɗin gwiwar karamar hukumar Ifelodun da shirin Livestock Productivity and Resilience Support Project (L-PRES).
Da yake jawabi a wurin taron, mataimakin gwamnan jihar Kwara, Mista Kayode Alabi wanda Honarabul Ganiyu Afolabi, dan majalisar jihar mai wakiltar mazaɓar Omupo ya wakilta, ya jaddada muhimmancin wannan shiri wajen magance matsalolin da manoman karkara ke fuskanta. Ya bayyana cewa shirin ba wai kawai zai rage rikici ba ne, zai kuma ƙara yawan kudaden shiga ga manoma da kuma ƙarfafa cin gashin kansu.
Ya ja hankalin mahalarta da su yi amfani da damar wajen amfani da sabbin ilimin da suka samu domin faɗaɗa sana’arsu da kuma samar da abincin dabbobi cikin sauƙi ta hanyar amfani da shara daga amfanin gona.
Shi ma da yake jawabi, shugaban karamar hukumar Ifelodun, Honarabul Abdulrasheed Yusuf, ya bayyana cewa wannan shiri zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da kuma rage kuɗin da ake kashewa wajen kiwon dabbobi ta hanyar samar da abincin dabbobi a cikin gida.
Ya kuma ƙara da cewa karamar hukumar tana aiki tare da masu ruwa da tsaki don samar da muhimman abubuwa kamar ruwa da wasu muhimman abubuwan raya ƙauyuka.
A nasa jawabin, sarkin Igbaja, Oba Ahmed Babalola (Elesie na Igbaja), ya yabawa wadanda suka shirya wannan horo, yana mai cewa an yi shi a lokacin da ya dace. Ya tabbatar wa mahalarta cikakken goyon baya domin nasara da dorewar shirin.
A baya, shugaban shirin L-PRES a jihar Kwara, Mista Olusoji Oyawoye, ya ƙarfafa matasa da su rungumi dama a fannin noma domin su dogara da kansu maimakon jiran aikin gwamnati. Ya buƙaci mahalarta horon da su rungumi shirin da cikakkiyar niyya domin su samu ƙwarewa da za ta taimaka musu da al’ummarsu gaba ɗaya.
Wannan horo wani ɓangare ne na babban shirin L-PRES da ke ƙoƙarin ƙara yawan amfanin kiwo, rage rikice-rikice, da kuma inganta ɗorewar rayuwa a ƙauyuka a faɗin Najeriya.
Ali Muhammad Rabi’u