Duk da samun koma baya: Najeriya ce kasa mafi arzikin danyen mai a Afirka —OPEC
Published: 15th, April 2025 GMT
Rahoton Kungiyar Kasashe Masu Samar da Man Fetur (OPEC) ya nuna cewa Nijeriya ta ci gaba da riƙe matsayinta na ƙasa mafi yawan samar da ɗanyen man a nahiyar Afirka a watan Maris.
OPEC ta ce hakan ya faru ne duk da raguwar yawan man da ƙasar ta samar a watan da ya gabata.
Sabon rahotonta na wata-wata da ta fitar a ranar Litinin ya ce yawan man da Nijeriya ta samar ya ragu zuwa ganga miliyan 1.
A cewar rahoton, duk da raguwar, yawan man da Nijeriya ta samar shi ne mafi yawa a Afirka, inda ya zarce Algeria da Congo.
An yi garkuwa da masu ibada a Kogi Noman rake: Najeriya da China sun kulla yarjejeniyar kasuwancin $1bn Isra’ila ta kashe Palasdinawa 17 ta jikkata 69 a awa 24 a GazaOPEC ta kara da cewa ta hanyar ci gaba da ƙarfin da ta samu a watan Fabrairu, Nijeriya ta zarce Algeria, wacce ta samar da ganga 909,000 a kowace rana, da kuma Congo, wacce ta samar da ganga 263,000 a kowace rana.
Ta ci gaba da da cewa Nijeriya ta samar da ganga miliyan 1.51 a kowace rana a watan Maris, idan aka kwatanta da ganga miliyan 1.54 a kowace rana a watan Fabrairu.
Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Sama ta Nijeriya (NUPRC) ta ce yawan man da ƙasar ta samar ya ragu zuwa ganga 1,400,783 a kowace rana a watan Maris.
Duk da raguwar yawan man da aka samar a watan Maris, NUPRC ta ce matsakaicin yawan ɗanyen man da aka samar ya kai kashi 93 cikin ɗari na adadin ganga miliyan 1.5 da OPEC ta ware wa Nijeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Najeriya a kowace rana a watan ganga miliyan 1 a watan Maris yawan man da Nijeriya ta
এছাড়াও পড়ুন:
Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Karatun Baya Dangane Da Tarihi Shi Ne Abun Da Ya Kamaci Japan
CGTN ta gabatar da kuri’un jin ra’ayin jama’ar ne ta harsunan Turancin Ingilishi, da Sifaniyanci, da Faransanci, da Larabci, da harshen Rasha. Inda masu bayyana ra’ayoyi 10,451 suka fayyace mahangarsu cikin sa’o’i 24. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA