2025-09-17@23:26:21 GMT
إجمالي نتائج البحث: 376
«Jam iyyar PDP»:
Sanatocin jihar Kebbi guda uku da suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC, tare da Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu, sun bukaci hadin kai tsakanin mambobin jam’iyyar domin samun nasara a zaben 2027. Sanata Adamu Aliero, wanda ya yi jawabi a madadin sauran sanatocin, ya bayyana haka a wani...
Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Edo, Misis Maria Oligbi-Edeko, ta ajiye muƙaminta. Ta bayyana murabus ɗinta ne a zaman majalisar da aka yi a ranar Litinin a Birnin Benin, babban birnin jihar. Zulum ya roƙi Gwamnatin Tarayya ta kai wa Marte ɗauki Hajji: Gwamnan Gombe ya yi bankwana da maniyyata 966, ya bai wa kowa...
Wasu mawaƙan jam’iyyar APC da ke Jihar Jigawa, sun bayyana ɓacin ransu kan yadda gwamnatin jihar ta yi watsi da su, duk da irin gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar jam’iyyar a zaɓen 2023. Mawaƙan wajen su 35, sun gudanar da wani taro, inda suka bayyana damuwarsu da kuma sanar da cewa sun janye...
Wasu mawaƙan jam’iyyar APC da ke Jihar Jigawa, sun bayyana ɓacin ransu kan yadda gwamnatin jihar ta yi watsi da su, duk da irin gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar jam’iyyar a zaɓen 2023. Mawaƙan wajen su 35, sun gudanar da wani taro, inda suka bayyana damuwarsu da kuma sanar da cewa sun janye...
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara ta yi kakkausar suka ga gwamna Dauda Lawal kan kalaman da ta bayyana a matsayin bata gari dangane da kokarin gwamnatinsa na magance ‘yan fashi da makami da kuma bayar da tallafi ga wadanda ‘yan fashin suka kashe. Hakan ya biyo bayan wani faifan bidiyo ne...
Jiragen na sojojin HKI sun kai hari ne dai a yau Lahadi a kan hanyar da ta raba tsakanin garin Beit-Yahun da Bent-Jubail dake kudancin kasar. A garin Kafar-kalla ma wani jirgin saman marar matuki ya jefa bama-bamai masu sauti a kusa da wani gida da dama an rushe shi. Harin na sojojin HKI yana...
Babbar Jam’iyyar hamayya ta PDP ta ce, ta soma ɗaukar matakan ɗinke ɓarakar da ta dabaibaye ta a ’yan shekarun nan. Matakin baya-bayan nan shi ne na taron masu ruwa da tsaki da jam’iyyar ta gudanar. Guguwar raba Masarautar Katsina ta kunno kai Tinubu ya isa Rome don rantsar da sabon Fafaroma Shin ko hakan...
Da safiyar yau Juma’a ne dai jami’an tsaron kasar Chadi su ka kai wani farmaki na kama tsohon fira minista kuma jagoran ‘yan hamayyar siyasar kasar Succès Masra. Jam’iyyar hamayya da Masra yake jagoranta, ta bayyana abinda jami’an tsaron su ka yi wa jagoran nata da cewa, garkuwa ce. Ita kuwa hukumar kasar ba ta...
Shugaban jam’iyyar NNPP na ƙasa, Dokta Agbo Gilbert Major, ya tabbatar da cewa tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso, ba ya tare da jam’iyyar tun watan Yunin 2023. Ya ce Kwankwaso ya fice daga NNPP tare da mabiyansa na Kwankwasiyya. Tinubu zai halarci rantsar da sabon Fafaroma Leo Cikin makonni kaɗan...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Jam’iyyar NNPP wadda Dakta Boniface Aniebonam ya kafa a shekarar 2001, ta samu ƙarfi sosai a Jihar Kano bayan tsohon Gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga cikinta a shekarar 2022 tare da mabiyansa na Kwankwasiyya. Shigowarsa ta farfaɗo da jam’iyyar, inda ta samu gagarumar nasara a zaɓen...
Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci zauren Majalisar Wakilai a ranar Alhamis domin ganewa idanunsa ficewar wasu mambobi biyu na Jam’iyyar adawa ta NNPP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC. ’Yan majalisar biyu, sun haɗa da: Dan Majalisar Wakilai, Abdullahi Sani Rogo mai wakiltar mazaɓar Rogo/Karaye da kuma Ɗan Majalisar Wakilai...
Ƴan majalisar tarayya guda biyu daga jihar Kano, Kabiru Usman da Abdullahi Sani, sun sanar da barin jam’iyyar NNPP zuwa APC a yayin zaman majalisar ranar Alhamis, suna mai nuni da rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyar. Shugaban majalisar Tajudeen Abbas ne ya karanta wasiƙun ficewarsu a zaman majalisar, inda ya bayyana cewa Usman na wakiltar...
Ya ƙaryata zargin cewa an ci zarafin waɗanda ake zargin, yana mai cewa an bi doka da ƙa’idoji na ƙasa da na duniya a duk matakan binciken da aka gudanar. Ya ƙara da cewa bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta an shirya shi ne domin yaudarar jama’a da neman tausayi tare da ɓata...
“Amma idan yanzu aka sake bai wa Arewa takara, wannan tsari tsakanin Arewa da Kudu zai ruguje.” Wike, wanda tsohon gwamnan Jihar Ribas ne, yana daga cikin fitattun jiga-jigan PDP da ke goyon bayan daidaito da karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa. A baya dai, rikici...
Ɗan majalisar jihar Kano mai wakiltar mazabar Sumaila, Hon. Zubairu Hamza Masu, ya bar jam’iyyar NNPP ya koma APC. A cikin wasiƙar murabus da ya aika wa shugaban majalisar, Hon. Ismail Falgore, Masu ya bayyana cewa rikice-rikice da shari’o’in cikin NNPP a matsayin dalilin ficewarsa. Tsohon Dan Takarar Gwamna A NNPP A Jihar Ondo Ya...
Yayin da a wannan Litinin ake bikin ranar jami’an jinya ta Duniya ta shekarar 2025, hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce akwai kashi 42 cikin 100 na ma’aikatan jinya a Afirka, dake cike da burin ficewa daga nahiyar saboda rashin cikakkiyar kulawa da kuma albashi mara tsoka. A jawabin da ya gabatar akan ranar...
Kungiyar Kurdawan Turkiya PKK ta sanar da cewa za ta ajiye makamanta ta kuma rusa kanta. Kamfanin dillancin labarum “Furat” mai kusanci da kungiyar ta PKK, ya nakalto cewa; Kungiyar ta yanke zartar da wannan matakin ne a yayin taron da ta yi kaso na 12 da ta yi kwanaki kadan da su ka gabata....
Shugaban Asibitin ido dake Gaza, Dr. Abdussalam Sabah, ya sanar da cewa, adadin Falasdinawan da su ka rasa ganinsu sanadiyyar yaki sun kai 1500. Dr. Abdussalam ya kuma yi gargadin cewa da akwai wasu Falasdinawa da sun kai 4000 da suke fuskantar barazanar rasa idanunsu saboda rashin kayan aiki a asibiti da kuma magani. Likitan...
Saraki, shi ne zai jagoranci kwamitin sai kuma ƴan kwamitin da suka haɗa da gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare; gwamnan jihar Filato, Caleb Muftiwang da kuma gwmanan jihar Enugu, Peter Mba. Sauran ƴan kwamitin sun haɗa da Sanata Seriake Dickson da Sanata Ibrahim Dankwambo da tsohon gwamnan jihar Abia, Chif Okezie Ikpeazu. ...
Sai dai a cikin takardar murabus din, Edema ya bayyana rashin tsarin jam’iyyar a matsayin dalilin da ya sa ya fice daga jam’iyyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
Da safiyar yau Asabar Falasdinawa 7 sun yi shahada sanadiyyar harin da HKI ta kai a yankin Gaza. Sojojin HKI sun kai harin ne a kan sansanin ‘yan hijira na unguwar ” al-Sabrah” a cikin birnin Gaza, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 5 a iyalai daya na Dulaibh. Shahidan su nel Saqar Ahmad...
Da safiyar Alhamis ɗin nan ne Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya halarci zauren Majalissar Wakillai ta ƙasa domin sheda ficewar Ƴan Majalissa uku na Jihar Katsina daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC Ƴan majalissar sun haɗa da Ɗan majalisa mai wakiltar (Mashi/Dutse) Hon. Salisu Yusuf Majigiri, da na (Bakori/Ɗanja) Hon. Abdullahi Balarabe Dabai,...
Har ila yau, kwamitin zai bada shawara akan hukuncin da Jam’iyar za ta dauka Idan har aka sami wanda ake zargi da laifin almundahana da kuma zagon Kasa ga LP a lokacin da yake Shugabantar jam’iyar. Sanata Usman ta zargi Abure da mukarrabansa da aikata laifufuka dake janyo rabuwar Kai ga ‘ya’yan Jamiyar...
Har ila yau, kwamitin zai bada shawara akan hukuncin da Jam’iyar za ta dauka Idan har aka sami wanda ake zargi da laifin almundahana da kuma zagon Kasa ga LP a lokacin da yake Shugabantar jam’iyar. Sanata Usman ta zargi Abure da mukarrabansa da aikata laifufuka dake janyo rabuwar Kai ga ‘ya’yan Jamiyar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk wanda ya shekara arba’in zuwa sama ya san irin tarbiyyar da ya samu daga wurin iyayensa a da, da irin mu’amalar da ke tsakaninsa da iyaye da kuma irin shaƙuwar da ke tsakanin ’ya’ya da iyaye. A yanzu kuwa, abubuwa sun canza daga yadda aka san su,...
Sumaila, tsohon mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin majalisar dokokin kasar, ya bayyana jam’iyyar NNPP a matsayin “jam’iyyar da ke da rabe-rabe da tabarbarewar al’amura, inda ya ce, rikicin da ya dabaibaye Jam’iyyar a fili yake babu mai musantawa, wadanda suka hada da shari’o’i a kotuna da dama da kuma gwagwarmayar...
Friedrich Merz na jam’iyyar CDU ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus. Majalisar Dokokin Jamus ta Bundestag ta zabi Merz a matsayin sabon shugaban gwamnati lokacin zaɓen zagaye na biyu, bayan ya gaza samun ƙuri’un da yake buƙata a zagayen farko na zaɓen. A zaɓen farko Merz ya samu ƙuri’u 325 na jam’iyyun ƙawance daga majalisar...
Kakakin Gwamnan Jihar Adamawa, Humwashi Wonosikou, ya ƙaryata jita-jitar cewa Gwamna Ahmadu Fintiri na shirin barin jam’iyyar PDP, yana mai cewa shugaban jihar ya cikin jam’iyyar kafada daram. A wata hira da manema labarai a Yola, Wonosikou ya bayyana cewa Gwamna Fintiri ya mai da hankali kan ayyukansa na shugabancin kwamitin taron jam’iyyar PDP, ba...
Wata kotu a kasar Tunisiya ta daure tsohin fira minsitan kasar Ali al-Aridh zaman kurkuku na tsawon shekaru 34 Shi dai al-Aridhi wanda dan jami’iyyar masu kishin musulunci ta ‘al-Nahdha’ ya zama fira minista ne daga shekarar 2013 zuwa 2014. Kotun ta zargi tsohon Fira ministan da hannu a ayyukan ta’addanci, lamarin da shi da...
“Ka san idan za ka yi la’akari da sauran jihohin da suke barin jam’iyyarsu su shiga wata jam’iyya ni a tunanina tsoro ne karawa da babban jam’iyyar adawar da ke jihar ba, yanzu misali a Jihar Delta shi gwamnan jihar ya san daker ya ci zabe a 2023 sannan kuma yana da yakinin idan bai...
Saleh ya ce, kaddamar da injin kyankyasar, musamman saboda jajircewar ma’aikatan sashen kan wannan aiki, tuni Jami’ar ta fara ganin sakamako mai kyau. Ya kara da cewa, samar da wannan inji, ya kara nuna irin mayar da hankali da Jami’ar ta yi, wajen habaka fannin aikin noma ta hanyar amfani da kimiyyar zamani da...
A yayin da jam’iyyun hamayya ke ci gaba da shirye-shirye tunkarar babban zaɓen shekara ta 2027, a bayabayan nan an ga yadda suke haɗuwa da juna, inda tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya tabbatar wa duniya cewa, suna tattaunawa domin ganin sun yi haɗakar da za ta kayar da Jam’iyyar APC mai mulki a...
A cewar kakakin shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, “Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ba ta fitar da jadawalin ayyuka na babban zaben shekarar 2027 ba, inda ta kayyade lokacin da jam’iyyun siyasa za su yi yakin neman zabe a bainar jama’a, don haka bai dace ba, kuma ya saba wa doka, a ce...
Sai dai kuma, idan Atiku da sauran ‘yan adawa suka ji tsoro, wanda hakan mai yiwuwa ne, kuma Tinubu ya sake cin zaven 2027, wanda shi ma zai iya yiwuwa, hakan ba zai zama saboda sauya sheka ba ne; domin kuwa tuni Atiku ya share fagen ruguza PDP, don kuwa ya nuna shi ne yake...
“Murkushe ‘yan adawa tare da musguna musu, musamman jam’iyyar PDP, wata alama ce karara da ke nuna cewa; zangon karshen mulki na karatowa; domin kuwa tarihi ya sha nuna hakan”, in ji Lamido a tattaunawarsa da BBC Hausa. “Ya kamata Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya kasance mai adalci, domin shi ne shugaban dukkanin...
Ƙungiyar matasan jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta ce guguwar sauyin sheƙa ta jiga-jigan ’yan siyasa da ke ficewa daga jam’iyyar NNPP alama ce da ke nuna cewa tasirin tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso a siyasance na ƙara disashewa. Cikin wata sanarwa da ƙungiyar matasan ta KASASCO ta fitar a ranar Talata, ta ce...
Haka kuma ya nemi kotu da ta bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsoffin takardun kuɗi na Naira 200, 500 da kuma 1000. Baya ga haka, ya buƙaci a umarci su da su nemi gafara ta hanyar wallafa bayani a manyan jaridu biyu na ƙasa. Amma a zaman kotu na ranar Litinin, wanda...
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, ya bayyana cewa sauyin jam’iyyar da manyan ‘yan suke yi zuwa jam’iyyar APC ana kamba ma shi fiye da yadda ya kamata, yana cewa wannan sauyin ba zai shafi kokarinsa na neman mafita ga matsalolin Nijeriya ba. Ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da manema labarai a Kano yau...
Mai magana da yawun Gwamnan, Mamman Mohammed ya bayyana sakon a matsayin kirkirarre kuma marar tushe da makama, wanda yayi hannun riga da gaskiya, ta wane bangare a cikin wannan shaci-fadi. Ya ce ba a taba yin makamancin wannan sakon ba, kuma mai wannan maganar bai taba zama makusancin Gwamna ba, ballantana ya iya...
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa zaɓen 2027 zai kasance ne kai tsaye tsakanin Shugaba Bola Tinubu da ’yan Najeriya da gwamnatinsa ta jefa su cikin mawuyacin yanayin rayuwa. Shugaban riƙo na PDP, Umar Damagum, ya jaddada cewa zaɓen “Tsakanin Jam’iyyar APC ne da ’yan Najeriya,” yana mai nuni da wahalar da talakawa ke fuskanta a...
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa duk waɗanda ke son barin jam’iyyar PDP su tafi yanzu, domin a bai wa masu kishin jam’iyyar damar sake gina ta. Saraki ya fitar da wannan bayanin ne a martani ga yawan sauye-sauyen jam’iyya da ake yi a PDP, ciki har da ficewar Gwamnan Jihar Delta,...
Tsoffin kwamishinoni na Jihar Kano kamar su Hon. Diggol, Hon. Abbas Sani da Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Baffa Bichi su ma sun koma APC. Hakazalika, Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada wanda ya tsaya takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar ADP a zaɓen 2023, ya sauya sheƙa zuwa APC. Ana kallon wannan sauya sheƙar a matsayin wani...
Jam’iyyar NNPP reshen Jihar Kano, ta mayar da martani da nuna jin daɗi ga ficewar Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, zuwa Jam’iyyar APC kwanan nan, inda ta ce ficewarsa za ta kawo zaman lafiya a jam’iyyar. Daily Trust ta ruwaito cewa hakan na zuwa ne sa’o’i 24 bayan Sanata Kawu Sumaila ya bayyana ficewarsa daga Jam’iyyar...
Muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ya umarci jami’an jam’iyyar da su yi karɓi Arch. Setonji Koshoedo a matsayin mukaddashin sakataren jam’iyya na ƙasa. Gwamnonin PDP, a taron da suka yi a Ibadan, Jihar Oyo, sun amince da Koshoedo a matsayin mukaddashin sakatare har sai lokacin da shugabannin shiyyar Kudu maso Gabas...
Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa na jihar sun sun sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Daga cikin jiga-jigan da suka sauya sheƙa har da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa, shugaban jam’iyya, da sauran masu ruwa da tsakin jam’iyyar reshen jihar. Abin da ya sa na bi sahun mahaifiyata a Kannywood —...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ba su da niyyar gudanar da tattaunawa da Amurka a fili Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana ta shafinsa na Twitter a takaitaccen jawabin da aka shirya yi a taron manufofin nukiliya na kasa da kasa na Carnegie, yana mai jaddada cewa, “Iran sam ba...
Haka kuma, ya soki jam’iyyar Galadima wato NNPP, yana mai cewa tana cike da rikice-rikice, saɓanin APC a ƙarƙashin shugabancin Ganduje wadda ke tafiya cikin daidaito. Okpala ya kammala da cewa Ganduje ya mayar da hankali wajen ciyar da jam’iyyar APC gaba, kuma ba zai tsaya sauraren “maganganun marasa tasiri” kamar na Galadima ba. ...
A yau Litinin shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya fitar da sanarwa ta nuna aljinin rasuwar Papa Roma Farancis,sannan kuma ya mika sakon ta’aziyya ga Mabiya darikar Roman Katolika na duniya. Shugaban kasar ta Iran ya rubuta cewa; Daga cikin matsaya da ta kasance fitacciya wacce Papa Roman ya dauka a lokacin rayuwarsa ita ce...
Gwamnaton kasar Kongo Democradiyya ta bada sanarwan haramta jam’iyyar Josept Kabila tsohon shugaban kasar. Shafin yanar gizo na labarai, Africa News ya nakalto ma’aikatar harkokin cikin gida na kasar tana bada wannan sanarwan. Labarin ya kara da cewa, Josept Kabila ya shugabanci kasar ta kwango har zuwa shekara ta 2019, karkashin Jam’iyyarsa ta ‘the People’s...
Bala’in Kogin Congo: Kwale-kwale ya kama wuta, ya kashe mutane 143 A wani mummunan lamari da ya afku a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, akalla mutane 143 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka bace bayan da wani kwale-kwale ya kama da wuta a kogin Kongo da ke arewa maso yammacin kasar. Akalla mutane 143 ne...