2025-11-27@10:29:08 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4908

«Zariya Funtuwa»:

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewar an ceto dukkanin mutanen da mahara suka sace a wata coci a yankin Eruku na Jihar Kwara. ’Yan bindigar sun sace masu ibadar ne a ranar Talata, lokacin da suka kai hari cocin Christ Apostolic Church (CAC) da ke Oke Isegun a Eruku, wani gari da ke iyaka...
    Mayaƙan ISWAP sun sace wasu ’yan mata a Ƙaramar Hukumar Askira-Uba a Jihar Borno. Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Abdullahi Askira, ya tabbatar da sace ’yan matan. Ɗalibai 50 da aka sace a Neja sun kuɓuta — CAN An rufe duk makarantu a Kebbi Ya ce an sace ’yan natan ne yayin da suke...
    Ƙungiyar Ƙwadago ta Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa (NUEE) ta yi barazanar dakatar da dukkan ayyukan samar da wutar lantarki a faɗin Najeriya, sakamakon harin da ta ce jami’anta sun fuskanta a Jihar Imo. Ƙungiyar ta bayyana cewa wasu jami’an ’yan sanda ɗauke da makamai ne suka kai wa ma’aikatanta hari a Egbu 132/33kB Transmission...
    161-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku, kissoshi wadanda suka zo cikin Alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Mrtada Muttahari, ko kuma cikin littafan Mathnawa na maulana Jalaluddeen Rumi....
    Zabebben magajin garin birnin NewYork na kasar Amurka Zohran Mamdani, a haduwarsa ta farko da shugaban kasar Amurka Donal Trump a birnin Washington ya bayyana cewa HKI tana aikata kissan kiyashi a gaza, sannan mutanen NewYork basa son ganin gwamnatin Amurka tana amfani da kudaden harajin da suke biyu wajen tallafawa gwamnati wacce take aikita...
    Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun gano wurin da ’yan bindiga suka tsugunar da ɗalibai mata 25 da suka sace daga makarantar kwana ta Maga da ke Jihar Kebbi. A wani taron manema labarai a Birnin Kebbi, Matawalle ya ce a halin yanzu an tsananta aikin leƙen asiri da tsare-tsare,...
    Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are (H-JRBDA) ta yi alƙawarin ɗaukar matakan gaggawa don magance matsalar ambaliyar ruwan da ke addabar al’ummar Ƙaramar Hukumar Jahun a Jihar Jigawa. Manajan Daraktan Hukumar, Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi, ya bayyana hakan bayan karɓar roƙon da jama’ar yankin suka miƙa ta hannun Shugaban Ƙaramar Hukumar, Jamilu Ɗan Malam Mai...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce matsalar tsaro a yankin Arewa na damunsa matuƙa saboda tana kawo cikas ga zaman lafiya da ci gaban Najeriya. Ya bayyana haka ne a Jihar Kaduna, yayin bikin cikar Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), wanda Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya wakilce shi. ’Yan sanda sun daƙile harin...
    Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa za a rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya daga ranar 24 ga watan Nuwamba, 2025. A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, ma’aikatar ta ce labarin ƙarya ne, ba shi da tushe daga Gwamnatin Tarayya, Ma’aikatar Ilimi ko...
    Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta shirya fara mayar da rarar kuɗin ga maniyyata, sakamakon rage kudin kujerun Hajjin 2026 da Hukumar Alhazai ta Kasa, NAHCON, ta sanar. A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Habibu Yusuf Babura, ya rabawa manema labarai, ya...
    Fira Ministan kasar Madagascar Herintsalama Rajaonarivelo ya gabatar da jadawalin ayyukan siyasa a gaban  majalisar kasar, da a ciki ya kunshi yadda zaman gwamnatin rikon kwarya zai kasance da yadda zai kai ga yin manyan zabukan kasar a cikin shekara daya da rabi. Fira ministan kasar ta Madagascar ya kuma ce; A karshen watan farko...
    Shugaban Cocin Katolika reshen Kontagora, ƙarƙashin ya ce ɗalibai 88 da aka yi zaton sun tsere yayin harin da ’yan ta’adda suka kai a makarantar St Mary Secondary School da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Neja, har yanzu ba a san inda suke ba. A cewar majiyoyi, iyaye da dama sun garzaya makarantar...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau. Shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka shafi siyasa, tattalin, arziki, zamantakewa tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane...
    Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana 47 da ke faɗin Najeriya. Gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne bayan hare-haren da ’yan bindiga suka kai makarantu a jihohin Kebbi da Neja, inda suka sace ɗalibai da ma’aikata, suka kashe mutum ɗaya. Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya...
    Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi, ya nemi ƙarin bayani kan dalilin ɗauke sojojin da ke gadin makarantar GGCSS Maga, gabanin harin da ’yan bindiga suka kai tare da sace ɗalibai 25. Gwamnan, ya ce gwamnati ta riga ta sanar da hukumomin tsaro game da yiwuwar kai hari, amma sojojin suka bar makarantar da misalin ƙarfe...
    Jami’an rundunar ’yan sanda ta Jihar Delta sun kama wani fasto na cocin Omega da ke Sapele bisa zargin lalata, fyade da kuma cin zarafin mata uku. Ana zargin Faston, wanda aka bayyana sunansa da Daniel Ololo mazaunin garin Sapele da yin lalata da ’yan mata uku ’ya’yan uwa ɗaya waɗanda mambobin cocinsa ne. Gwamnatin...
    Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da ya koma jihar Kebbi da aiki sakamakon sace ɗalibai ’yan mata 25 da wasu ’yan bindiga suka yi a jihar. Tinubu ya umurci Matawalle, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a Kebbi domin sa ido kan dukkan matakan tsaro da...
    Rundunar ƴansandan jihar Neja ta ce tuni ta aika jami’ai yankin da aka sace wasu ɗalibai da ba a san adadin su ba har yanzu domin kuɓutar da su. Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP W. A Abiodun ya fitar, ya ce an aika jami’an tsaro da haɗin gwiwar sojoji da sauran...
    Ƙaramin kwamitin majalisar dokokin Amurka kan harkokin kasashen Afirka ya yi wani zama kan batun zargin kisan kiyashin da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya da batun yadda Shugaba Donald Trump ya ayyana kasar a matsayin “wadda Amurka ke nuna damuwa a kanta kan walwalar addini,” sai dai kawunan mambobin majalisar sun rarrabu a kan...
    Daga Ali Muhammad Rabi’u ‘Yan bindigar da suka sace masu ibada 38 a Cocin Christ Apostolic Church (CAC), Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a Jihar Kwara sun nemi kudin fansa na Naira miliyan 100 kan kowane mutum daya da suka sace. Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa masu garkuwan sun fara kiran iyalan waɗanda aka...
    Daga Bello Wakili Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan  Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, da ya koma Jihar Kebbi biyo bayan sace dalibai  ’yan mata 24  a jihar. An umurci Matawalle, wanda tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a jihar domin sa ido kan ƙoƙarin  da ake yi na kubutar da ɗaliban da aka...
    Daga Usman Muhammad Zaria Daliban makarantu daga jihohin Arewa maso Yamma da suka hada da Kano, Jigawa da Katsina sun yi kira ga masu ruwa da tsaki da su samar musu da tsaro, ingantaccen kiwon lafiya, da taftataccen ruwan sha. Daliban sun yi wannan kiran ne yayin bikin Ranar Yara ta Duniya da aka gudanar...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da fitar da Naira Biliyan 3 a matsayin  tallafin hadin gwiwa na kowace shekara  domin inganta ilimi a matakin farko, wato UBEC 2025 Matching Grant. A wata sanarwa da Kwamishinan  Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na Jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya fitar ya bayyana...
    Iyalai da ‘yan uwan wadanda aka kashe a lokacin zanga-zangar da ta kawo karshen gwamnatin tsohuwar Firaminstar Bangaledash Sheikh Hasina a bara, sun yi maraba da hukuncin kisa da wata kotun birnin Dhaka ta yanke mata. An samu Sheikh Hasina da laifin cin zarafin bil adama tare da ba ‘yan sanda umurnin kashe masu zanga-zanga,...
    Rahotanni sun bayyana cewa a zaman da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya yayi a baya bayan nan yayi kira a dauki matakin gaggawa don kawo kareshen yaduwa ayyukan ta’addanci a kasashen yammacin Afrika da kuma yankin sahel, yana gargadin cewa yankin na so ya zama cibiyar tsattsauran raayi da rikice- rikice Anasa bangaren babban...
    Kafofin yada labarai na duniya sun mayar da hankali kan taron majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar Shanghai SCO na 24 da aka gudanar kwanan nan a birnin Moscow na kasar Rasha.  Fira ministan kasar Sin Li Qiang ya yi kira ga kungiyar SCO da ta aiwatar da shawarar inganta tsarin shugabanci na duniya da  kasar...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esmail Baghaei yayi tir da shigar isara’ila kasar Siriya ba bisa kaida ba, yayi gargadin cewa ci gaba da kai hare-hare da fadada siyasarta ta mamaya babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaron yanki. Haka zalika tahren ta yi gargadin cewa matakin baya bayan nan da isra’ila ta...
    Shugaban Cocin Katolika na Duniya, Fafaroma Leo XIV, ya musanta zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya. Babban limamin, ya bayyana cewa duk da cewa akwai damuwa dangane da matsalar tsaron Nijeriya, amma babu wani mabiyi na kowanne addini da matsalar ta ƙyale. Sai da Kwankwaso APC za ta iya samun nasara...
    Ƙungiyar ɗalibai ’yan Jihar Kano ta roƙi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, gwamnoni da ’yan Majalisar Tarayya da su kawo ƙarshen taƙaddamar Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU. Ƙungiyar ɗaliban ta ƙasa reshen Jihar Kano (NAKS) ta roƙi shugabannin da su gaggauta aiwatar da duk mai yiwuwa domin warware taƙaddamar da ke tsakanin gwamnati da ASUU....
    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sami jagoran haramtacciyar ƙungiyar neman kafa kasar Biyafara ta IPOB, Nnamdi Kanu, da laifukan ta’addanci da aka zarge shi da aikatawa. Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, Mai Shari’a James Omotosho, ya amince da batutuwa uku da aka gabatar a shari’ar, inda ya yanke hukunci a kan...
    Mutum uku da wani yaron babbar motar kaya sun rasa ransu bayan wayar wutar lantarki kashe su a lokacin wani bikin nadin sarauta a unguwar Idimu da ke Ƙaramar Hukumar Alimosho ta jihar Legas, bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar Talata, 11 ga watan Nuwamba, kuma an gano cewa yaron motar, wanda...
    Mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya jagoranci manyan jami’an Gwamnatin Nijeriya zuwa Amurka don tattaunawa game da zargin kisan ƙare dangi da ake yi wa Kiristoci. Lamarin ya samo asali ne bayan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya goyi bayan kafa ƙasashe biyu na Isra’ila da Gaza....
    Gwamnatin Tarayya ta ɗora alhakin dawowar hare-haren ta’addanci, ciki har da sace dalibai mata a jihar Kebbi da kai hari a coci a jihar Kwara, kan kalaman da Amurka ta yi kwanan nan a kan Najeriya. Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya ce sakonnin da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa, inda ya zargi Najeriya...
    Gwamnan Jihar Binuwai, Hyacinth Alia, ya ce babu wani addini ko mabiyansa da ake yi wa kisan ƙare dangi a jiharsa ko a Najeriya baki ɗaya. Ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba a wani taron da Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Ƙasa (NHRC) ta shirya a Abuja kan kare haƙƙoƙin mutanen da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mata da dama da aka yi garkuwa da su na shiga wani irin mawuyacin hali yayin da suke hannun wadanda suka sace su, suna fuskantar rayuwar kaskanci, da cin zarafi, da muzgunawa da wasu irin yanayi wanda sai ka tausaya musu. Irin wadannan mata a wasu lokutan basa...
    Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 15 ga watan Janairun 2026, don fara shari’ar shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru; Mahmud Usman da Abubakar Abba. Ana zargin su da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, kuma Hukumar DSS ce ta kama su tare da gurfanar da su a kotu. Ribadu ya jagoranci tawaga...
    Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya jagoranci wata tawagar gwamnati zuwa Amurka domin mayar da martani kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya. Wannan zargi ya samo asali ne bayan mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya nuna goyon bayansa wajen kafa ƙasashe biyu tsakanin Isra’ila da...
    Tauraron ƙwallon ƙafar ƙungiyar PSG da ƙasar Morocco, Achraf Hakimi, ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana.  
    Fitaccen ɗan wasan gaba na Najeriya da ke taka leda a ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya, Victor Osimhen, ba zai halarci bikin karrama gwarazan ‘yan wasan Afirka na 2025 ba. Osimhen, wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Afirka a 2023, ya bayyana cewa ya koma Turkiyya ne domin duba lafiyarsa, bayan raunin da ya samu...
    An shiga jimami a garin Zugai da ke Ƙaramar Hukumar Roni ta Jihar Jigawa, bayan da wani tankin ruwa ya faɗo tare yin sanadin rasuwar mutum da jikkata wasu. Daga cikin waɗanda suka rasu har da wata mace mai juna biyu. An yanke wa shugaban ISWAP hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari Gwamna Abba...
    Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa wani shugaban ISWAP Hussaini Ismaila, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bayan samun sa da aikata laifukan ta’addanci. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya yanke hukuncin ne bayan Ismaila, wanda ake kira Mai Tangaran, ya amsa tuhume-tuhume guda huɗu da Hukumar DSS ta...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin 2026 na kuɗi Naira tiriliyan 1.36 a Majalisar Dokokin jihar. Kasafin wanda aka yi laƙabi da “Kasafin Gine-gine, Ci Gaban Kowa da Ɗorewar Ci Gaba.” Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin 2026 na kuɗi Naira tiriliyan 1.36 tiriliyan a Majalisar Dokokin jihar. Kasafin wanda aka yi laƙabi da “Kasafin Gine-gine, Ci Gaban Kowa da Ɗorewar Ci Gaba.” Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe Tinubu ya fasa zuwa taron G20...
    Cibiyar Blue Sapphire ta kaddamar da wani shiri na musamman da aka kirkiro domin ƙarfafa gwiwar mata ’yan kasuwa a fannin dinkin kayan sawa da kuma harkokin kirkira a arewa maso yammacin Najeriya. Cibiyar na aiwatar da wannan shiri ne tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar ’Yan Kasuwa Mata ta Arewa (ANWE) da Jami’ar Northwest Kano,...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da tafiyarsa zuwa Birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu, da Luanda na Angola, sakamakon sace ɗalibai a Jihar Kebbi da kuma harin da aka kai wa masu ibada a wata coci da ke yankin Eruku a Jihar Kwara. Tinubu, shirya barin Abuja a ranar Laraba domin halartar taron...
    Majalisar Dattawa ta shiga cikin jimami a ranar Laraba bayan mutuwar Sanata Okey Ezea, mai wakiltar mazabar Enugu ta Arewa. Bayanai sun nuna marigayin ya rasu ne a kasar Burtaniya inda yake jinya. ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ Mai taɓin hankali ya kashe soja a Legas Ezea, wanda aka zaɓe...
    Majalisar Wakilai ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya sake kawo sabuwar dabarar da za ta kawo karshen kashe-kashe, da sace-sace da sauran ayyukan ‘yan bindiga a Jihar Zamfara da ma kasa baki daya.  Wannan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa na kula da muradun jama’a da dan majalisa mai wakiltar mazabar...
    Wani mutum da ake zargin yana fama da matsalar tabin hankali ya kai hari tare da kashe wani soja a yankin Imota da ke Ikorodu a jihar Legas. Lamarin, wanda ya faru a fili da rana tsaka a ranar Lahadi, ya sa makwabtan wurin da dama guduwa don neman tsira. Gobara ta laƙume kasuwar Katako...
    Kasar Saudiyya ta sanar cewa za ta kara hannun jarinta a Amurka zuwa dala tiriliyan daya, daga dala biliyan 600 da kasar ta zuba a baya. Yariman Saudiyyar ne Mohammed Ben Salman ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai tare da Shugaban Amurka Donald Trump a ziyarar da ya kai fadar...
    A ranar Alhamis, 20 ga watan Nuwamban 2025, ake sa ran Majalisar Wakilan Amurka za ta gudanar da zama na musamman domin bincikar zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya. Kwamitin Majalisar Wakilan kan Afirka ya sanya ranar domin bitar fasalin da Shugaba Donald Trump ya yi kwanan nan na sanya Nijeriya a matsayin...