2025-10-16@06:26:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 911
«Hamayya»:
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu sun bayyana alhini kan kisan gillar da aka yi wa Somtochukwu ‘Sommie’ Maduagwu, waata ’yar jarida mai gabatar da labarai a gidan Talabijin na ARISE TV. A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, shugaba Tinubu da uwargidansa sun yi Allah-wadai da kisan, suna...
Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ba wa Gwamnatin ƙasar Qatar haƙuri kan harin da ƙasarsa ta kai a birnin Doha, wanda ya yi ajalin wani jami’in tsaron Qatar. Netanyahu ya bayar da haƙuri ne a yayin wata tattaunawa da shugaban Amurka, Donald Trump ya shirya tsakaninsu da Fira Ministan Qatar, Mohammed Al-Thani. A saƙon...
Gwamnatin Nijeriya ta ayyana ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025 a matsayin ranar hutu albarkacin cikar ƙasar shekaru 65 da samun ’yancin kai. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya fitar a madadin Gwamnatin Tarayya. Ɗalibar jami’ar IBB ta faɗi ta rasu FERMA ta ƙaddamar da...
Wata ɗalibar aji biyu a sashen nazarin ƙwayoyin halittu da sunadarai na Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU), Lapai da ke Jihar Neja ta riga mu gidan gaskiya. Aminiya ta ruwaito cewa, Fatima Adamu Muhammad, ta rasu ne bayan ta yanke jiki ta faɗi a wani matsuguninta da ke wajen makarantar. ASUU ta bayar da wa’adin...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya ya bayyana cewa bukatun gwamnatin Amurka daga kasar Iran ba abar amincewa ba ne. Shugabany a bayyana haka ne a ranar Asabar kafin ya bar birnin Newyork zuwa Tehran bayan ya halarci taron babban zauren MDD na shekara shekara. Yace: Bamu daidaita da su kan snapback ba, sai Amurka tace...
Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi, ya sallami Kwamishinar Harkokin Mata da Ci-gaban Yara, Zainab Baban Tanko. Sanarwar da kakakin gwamnan, Mukhtar Giɗaɗo, ya fitar ta bayyana cewa sallamar ta fara aiki ne nan take. Ya bayyana cewa hakan ta faru ne a sakamakon sauye-sauye a majalisar zartarwa ta Jihar Bauchi. Ya bayyana godiyar...
Tabbas, ko a zamanin yau ma, aikin raya tattalin arziki ba ya rabuwa da wahalhalu. Misali, a cikin gidajen da ake kiwon jatan lande, dole ne mutane su jure yanayi mai zafi da ya kan kai sama da digiri 40 na ma’aunin Celcius, da kuma tarin sauro dake cizon mutum. Har ila yau, akwai...
Wane irin farin ciki za ku ji a matsayinku na iyaye, a cewa ’ya’yanku biyu sun kammala jami’a da Digiri Mai Daraja ta Ɗaya (First Class) a lokaci guda kuma daga wani kwas mai farin jini a wannan zamani na kimiyyar zamani? Wani labari mai sha’awa shi ne yadda wasu ’yan uwa biyu suka kammala...
Jami’an ’yan sanda a Jihar Ondo sun kuɓutar da wata yarinya ’yar shekara huɗu da ta ɓace tare da gano wasu masu fataucin yara da ke gudanar da ayyukan su a yankunan Jihohin Ondo, Delta da Anambra. An fara shari’ar ne a ranar 3 ga Fabrairu, 2025, lokacin da Sunday Kingsley da ke yankin Alagbaka...
Gwamnatin Jihar Katsina ta kori ma’aikata 3,488 daga ƙananan hukumomi 34 da hukumomin ilimi na ƙananan hukumomi (LEA) bayan wani binciken tantance su ya bankado badakala. Gwamnan jihar, Dikko Radda, wanda ya karɓi rahoton kwamitin a ranar Laraba, ya ce an tantance ma’aikata 50,172, inda aka tabbatar da sahihancin 46,380, yayin da sauran suka bayyana...
Kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa Dr. Danladi Jatau ya bayyana matukar kaduwarsa dangane da labarin rasuwar tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja, Barista Solomon Aku Ewuga. Kakakin majalisar a wata sanarwa da sakataren yada labaran sa Jibrin Gwamna ya fitar, ya bayyana rasuwar mataimakin gwamnan jihar a matsayin babban rashi ga jihar da ma...
Gwamnatin jihar Kwara ta jaddada kudirinta na sake gyarawa da samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya a matakin farko. Sakatariyar zartarwa na Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Kwara (KWPHCDA), Farfesa Nusirat Elelu, ta bayyana hakan a lokacin da ta karbi bakuncin kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM) da...
Da yake magana a gaban babban zauren majalisar dinkin duniya Yarima mai jiran gado na kasar Kuwait shaikh sabah khalid al-hamad Al-sabah ya bayyana yanayin da ake ciki a yankin gaza a matsayin babban bala’I, yace alumma faladinu da basu da wani mai basu kariya suna fuskantar wahalhalu mafi muni a tarihi. Har ila yau ...
Shugaban Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, yayin da Shugaba Bola Tinubu, ya gana da tsohon shugaban riƙo na Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok Ete Ibas (mai ritaya). Ya fadar ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya gana da...

Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Mutane Sun Yaba Da Gina “Tsarin Xinjiang” A Turbar Zamanantarwar Kasar Sin
Yayin da ake cika shekaru 70 da kafuwar yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa a bana, CGTN ta gudanar da wani bincike na kuri’ar jin ra’ayoyi a duniya a kwanan baya tsakanin mutane 7,446 daga kasashe 38. Sakamakon binciken ya nuna cewa masu bayyana ra’ayoyinsu sun yaba da nasarorin da aka samu a...
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce a matsayin Sin na babbar kasa mai tasowa dake sauke nauyin dake wuyanta, ba za ta nemi wani sabon matsayi na musamman, ko fifiko yayin tattaunawar cimma matsaya ta yanzu, da ma ta nan gaba, dangane da harkokin kungiyar cinikayya ta duniya WTO. Li, ya yi wannan tsokaci...
Wata Kotun Soji ta yanke wa wasu sojoji uku hukuncin ɗaurin rai da rai kan sayar da makamai da harsasai ba bisa ka’ida ba a Maiduguri, Jihar Borno. Kotun sojin ƙarƙashin jagorancin Birgediya-Janar Mohammed Abdullahi, ta bayyana cewa an yanke wa mutum uku daga cikin sojojin huɗu hukuncin ɗaurin rai da rai yayin da aka...
Ana zargin wata matar aure, Rabi Nuhu da ke garin Magama Gumau a ƙaramar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, da cin zarafin wata yarinya ’yar shekara biyar ta hanyar ƙone mata al’aura, saboda zargin tana yawan yin fitsarin kwance. Wakilinmu ya gano cewa yarinyar marainiya ce wadda mahaifiyarta ta rasu kusan shekara ɗaya da ta...
Ana zargin wata matar aure, Rabi Nuhu da ke garin Magama Gumau a ƙaramar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, da cin zarafin wata yarinya ’yar shekara biyar ta hanyar ƙone mata al’aura, saboda zargin tana yawan yin fitsarin kwance. Wakilinmu ya gano cewa yarinyar marainiya ce wadda mahaifiyarta ta rasu kusan shekara ɗaya da ta...
Kwamitin da ke kula da tsare-tsare da manufofin kuɗi na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya zaftare maki 60 daga nauyin kuɗin ruwa da ke kan masu karɓar basussuka. Wannan dai shi ne karo na farko cikin shekaru biyar da aka samu babban bankin ya yi rangwamin kuɗin ruwa a ƙasar. CBN ɗin ya ce kwamitin a...

He Lifeng: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Karfafa Dangantakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Mai Dorewa Cikin Lumana
Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng ya gana da tawagar ‘yan majalisar wakilan Amurka karkashin jagorancin Adam Smith a yinin yau Litinin 22 ga wata a birnin Beijing. He Lifeng ya ce, a ranar 19 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaba Donald Trump sun yi wata tattaunawa ta wayar tarho, kuma sun...
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ayyana gobe Talata, a matsayin ranar ɗaya ga watan Rabi’ul Thani, 1447 bayan hijira, wanda ya kawo ƙarshen watan Rabi’ul Awwal, 1447, daidai da ranar 23 ga Satumba, 2025. Sanarwar ta fito ne a wata takarda da Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, wanda shi ne shugaban kwamitin da...
Haddadiyar Kungiyoyin Makiyaya na kasashen Africa (CORET) ta bayyana cewa an samu karin yawan ɗalibai a makarantun makiyaya cikin watanni goma da aka fara shirin ciyar da ɗalibai. Babban Sakataren CORET, Muhammed Bello Tukur, ya bayyana haka a taron kwana ɗaya da aka gudanar a Kaduna domin ƙara wa ma’aikata da abokan hulɗarsu...
Ƙaramar Hukumar Gombe, ta raba wa mata masu juna guda 400 kayan haihuwa kyauta, domin kare lafiyarsu da rage mace-mace a yankin. An gudanar da rabon ne a Cibiyar Haihuwa ta Gombe a ranar Alhamis, inda shugaban Ƙaramar Hukumar, Barista Sani Ahmad Haruna, ya jagoranci rabon. Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 4, 16 sun...
Firay ministan kasar Burtaniya da tokwarorinsa na kasashen Canada da Australia duk sun bayyana amincewar gwamnatocinsu da samuwar kasar Falasdinu mai zaman kanta. Wanda ya nuna sauyi babba a al-amuran diblomasiyya wadanda suka sha fi HKI da kuma Falasdinawa. Kafin haka dai, idan an masu maganar samar da kasar Falasdinu sai suce sun barwa HKI...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kungiyar Hizbullah ta fitar da wata sanarwa ta gayyata domin halartar taron tunawa da zagayowar ranar shahadar Sayyid Hassan Nasrallah wanda za yi a ranar 27 ga watan nan na Satumba. Tunawa da Shahid Sayyid Hassan Nasrallah da sauran wadanda su ka yi shahada a lokacin, kamar su Shahid Sayyid Hashim Safiyuddin, zai kasance a...
Wata mata ta haifi jarirai huɗu — maza biyu da mata biyu — a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya ta Kimiyyar Kiwon Lafiya (FUHSTHA) da ke Azare, a ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025. Sakataren yaɗa labarai na asibitin, Abdu Mohammed, ya shaida wa Aminiya cewa Malama Hauwa ta haifi yaran ne ta hanyar tiyata,...
Hukumar Sibil Difens (NSCDC) a Jihar Gombe, ta kama mutum shida bisa zargin tono gawar wani mutum a kabari tare da cire sassan jikinta domin yin asiri. Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, Kawuji Sarki, mai shekaru 39, ya amsa laifin. Wata mata ta ƙona al’aurar ’yarta da wuta kan zargin maita a Bauchi Janye...
Idan aka yi ɗan nazari kan tafiyar siyasar Seyi Makinde a Jihar Oyo da kuma yammacin Nijeriya gaba ɗaya, za a fahimci sosai wane ne Makinde da kuma dalilin da ya sa ya dace kowanne ɗan siyasa mai hangen nesa ya yi hattara da shi kafin 2027. Ko da yake Gwamnan Jihar Oyo, wanda ake...

Ci Gaban Tattalin Arzikin Sin Na Taimaka Ga Bunkasa Al’adunta Da Mu’amalar Al’adu Tsakaninta Da Kasashen Duniya
Hukumar Kididdiga ta kasar Sin ta samar da alkaluman tattalin arziki na watan Agusta a kwanan nan, alkaluman da suka nuna cewa, tattalin arzikin Sin yana ci gaba da bunkasa ba tare da tangarda ba, musamman a fannin sana’o’in ba da hidima, inda ma’aunin ISP game da ayyukan ba da hidima ya karu da kashi...
A kokarin ta na ci gaba da zaburar da ma’aikatan ta, Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce za ta shirya taron bitar sanin makamar aiki ga jami’an ta dake dawainiya da alhazai a gida da kuma kasa mai tsarki. Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed umar labbo ya bayyana haka bayan kamala...
Sabuwar mutum-mutumi ta fasahar AI da aka kirkira kuma aka nada mukamin minista a ƙasar Albania ta yi jawabi a karon farko a gaban majalisar dokokin kasar. A ranar Alhamis ce dai ministan ya bayyana gaban majalisar, inda ya kare rawar da zai taka a gwamnati, yana mai cewa, “Ban zo don na maye gurbin...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Zamanin kebe kai ya ƙare, Haɗin gwiwar Iran da Rasha ya cimma abin koyi mai nasara A yayin ganawarsa da ministan makamashin kasar Rasha Sergei Tyswell da tawagarsa, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Nasarar da aka samu na hadin gwiwa tsakanin kasashe masu cin gashin kai...
Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi, Wale Edun, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa Naira biliyan 330 a matsayin tallafi. Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce an raba kuɗin ne ta Ofishin Tsare-tsaren Jin-ƙai na Ƙasa (NASSCO), domin rage wa talakawa wahalar cire tallafin mai da...
Masu bincike a Turai sun yi amfani da fasahar ƙirƙirariyyar basira ta AI don yin hasashen matsalolin lafiya da ɗaiɗaikun mutane za su iya fuskanta cikin shekaru goma masu zuwa ko fiye na rayuwarsu. Sun ce fasahar na amfanin da bayanan rashin lafiyar da mutum ya yi a baya, domin hasashen cutuka fiye da dubu...
Gwamnatin Jihar Zamfara ta roki Hukumar Raya Kasashen Waje ta Kasa (FCDO), Premier Urgence Internationale (PUI), da sauran masu ruwa da tsaki da su kara tallafa wa ‘yan gudun hijirar da ke jihar. Kwamishinan Bada Agaji na Jiha Alhaji Salisu Musa Tsafe ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi ga mahalarta...
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar wa kungiyar mafarauta/Yanbulala reshen jihar Jigawa na rundunar a shirye ta ke ta shirya wani horo na kara musu karfin gwiwa ga mambobinsu. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Dahiru Muhammad ya bayar da wannan tabbacin ne a yayin wani taro da aka yi da mafarauta/Yanbulala na yankin wanda Lamido...
Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mani Malam Mumini ya jajanta wa al’ummar karamar hukumar Gumi kan mumunan al’amuran da suka salwantar da rayukan mazauna kauyen Fas su 19 a makonnin da suka gabata. Malam Mumini ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci wasu jami’an gwamnati da suka kai ziyarar jaje ga al’umma, inda...
Daga ranar 14 zuwa 15 ga wata, an gudanar da sabon zagayen shawarwari kan harkokin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka a birnin Madrid, babban birnin kasar Spaniya, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra’ayoyi a kan harkokin cinikayya da ke janyo hankalinsu, tare da cimma daidaito ta fannin daidaita batutuwan da...
Fitattun dalibai akalla 12 ne daga makarantun gwamnati suka samu guraben tallafin karatun sakandare a ƙarƙashin Asusun Tallafin Karatu na Jihar Kwara (Kwara-ETF). A wajen taron gabatarwa ga waɗanda suka fara cin moriyar shirin, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana cewa ci gaban harkar ilimi a Najeriya abu ne mai tsada kuma ya zama wajibi kowa...
Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani guda 20, tare da riguna ruwa (life jackets) 2,000, domin rage haɗurran da ke aukuwa sakamakon ambaliya da nutsewar jirage a sassan jihar. An ƙaddamar da jiragen ne a ƙaramar hukumar Wamakko a ranar Laraba, inda gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki na...

Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce alkaluman baya bayan nan da aka fitar cikin Mujallar Economist, sun shaida yadda hada-hadar cinikayyar fitar da hajoji ta kasar Sin ke kara bunkasa cikin sauri a shekarar nan ta bana, inda fannin ke samun karuwar abokan hulda, da daidaiton matsayi cikin tsarin samar da...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye dokar ta-baci a Jihar Rivers daga ƙarfe 12 na daren 17 ga watan Satumban 2025. Shugaban Ƙasar, a wata sanarwa da ya sanya wa hannu, ya ce dokar ta-bacin da ta dakatar da Gwamna, Mataimakiyarsa, da ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida ta cimma...

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban
A yau Laraba ne aka bude bikin baje koli karo na 22, na Sin da kasashe membobin kungiyar ASEAN ko (CAEXPO), da kuma taron dandalin kasuwanci da juba jari na Sin da ASEAN ko CABIS, a birnin Nanning na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai dake kudancin kasar Sin. A shekarun baya...
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yabawa Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jiha bisa ƙirƙirar Kyautar Malami Mafi Nagarta, yana mai bayyana hakan da ɗaya daga cikin manyan manufofin da za su ƙarfafa koyo da koyarwa a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Yaɗa Labaran sa, Hamisu Mohammed Gumel, ya...
Gwamnatin kasar Iran ta bayyana wasu abubuwan da bata amince da su ba, a jawabin bayan taro na musamman na kungiyar kasashen musulmi ta (OIC) wanda aka gudanar a birnin Doha na kasar Qatar a ranar litinin 15 gawatan Satumba da mukeciki. Sannan ta kara tabbatar da goyon bayanta ga gwagwarmayan da Falasdinawa suke yi...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sojojin Najeriya sun kashe aƙalla mayakan ƙungiyar ISWAP 8, ciki har da manyan kwamandojinta biyu a Jihar Borno. Wata majiyar leƙen asiri daga rundunar haɗin kai ta OPHK ta bayyana cewa an kashe ’yan ta’addan ne a wata arangama da suka yi da sojojin a kan hanyar Maiduguri zuwa Baga a safiyar ranar Litinin. DSS...
Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano ta haramta shirya duk wata muƙabala tsakanin mawaƙan yabon Annabi (S.A.W), tare da gayyatar mawaƙa Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi su bayyana a gabanta. Hukumar ta kuma gayyaci mawaƙan ne tare da sauran waɗanda suka jagoranci muƙabalar da fitattun mawaƙan biyu suka yi ranar Litinin,...