Microsoft Za Ta Fuskanci Hukunci Kan Waimaka Wa Isra’ila A Laifukan Da Take Aikatawa Kan Falasdinawa
Published: 5th, December 2025 GMT
Microsoft na fuskantar matsin lamba da kuma matakin shari’a saboda samar wa Isra’ila fasahar da ake amfani da ita wajen take hakkin Falasdinawa a Gaza da Yammacin Kogin Jordan.
A cikin wata budaddiyar wasika da aka aike wa kamfanin a ranar 2 ga wannan watan, wata kungiyar lauyoyi ta kasa da kasa ta yi gargadin cewa Microsoft da shugabanninta za su iya fuskantar hukunci na shari’a kan taimakawa da kuma tallafawa laifukan da aka aikata wa fararen hula Falasdinawa.
Eric Saib, mai kula da harkokin ci gaban kafofin watsa labarun kasa da kasa na Cibiyar Larabawa don Ci gaban Kafafen Yada Labarai, ya jaddada cewa watannin baya-bayan nan sun nuna karara cewa ana amfani da ayyukan kamfanin wajen take hakkin dan adam a Falasdinu, yana mai kira ga masu hannun jari da su fahimci hadarin da ke tattare da ci gaba da wannan hadin gwiwa.
Wasikar ta bayyana cewa Microsoft tana bai wa sojojin Isra’ila na kasa, sama, da na ruwa bayanai masu mahimmanci duk da amincewa tsakanin kungiyoyin kare hakkin dan adam da kwararru cewa Isra’ila tana aikata kisan kare dangi a Gaza.
A cikin wani rahoto da aka fitar a ranar 30 ga Yuni, Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta Musamman kan Kare Hakkin Dan Adam, Francesca Albanese, ta nuna cewa kamfanoni sama da sittin daga sassa daban-daban sun ba da gudummawa wajen rusa Gaza, tallafawa ayyukan gina matsugunan Yahudawa a Yammacin Kogin Jordan, da kuma tilasta wa Falasdinawa yin hijira, ciki har da manyan kamfanonin Amurka kamar Amazon, Google, IBM, da Microsoft.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Amurka Tana Sake Yin Bitar Alakar Da Ke Tsakaninta Da Tanzania December 5, 2025 Fadlallah Na Hizbullah Ya Yi Kiran Hadin Kai A Tsakanin Musulmi Da Larabawa Domin Fuskantar Kalubale December 4, 2025 Jiragen Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kai Hare-hare A Kudancin Lebanon December 4, 2025 An Kira Yi Gwamnatin Canada Da Ta Kama Olmert Da Livini Na “Isra’ila December 4, 2025 An Kashe Shugaban ‘Yan Dabar Gaza “Abu Shabab” Da Isra’ila Ke Goyon Baya December 4, 2025 Iran : Jagora Ya Bayyana Ra’ayin Musulunci Kan Hakkokin Mata December 4, 2025 Taron IMO : Tehran Ta Yi Watsi Da Zarge-zargen Isra’ila Marasa Tushe December 4, 2025 MDD ta nemi a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma Tuddan Golan December 4, 2025 Rundunar Ruwa ta IRGC na Gudanar Da Atisayen Soja a Tekun Fasha December 4, 2025 Dan wasan Taekwando Na kasar Iran Ya Samua Lambar Yabo Ta Zinariya December 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
MDD ta bukaci a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma janyewa daga Tuddan Golan na Siriya
Babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wasu kudurori guda biyu da ke kira da a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma Tuddan Golan na Siriya.
Djibouti, Jordan, Mauritania, Qatar, Senegal, da Falasdinu ne suka gabatar da daftarin kuduri game da Falasdinu.
Kasashe 151 ne suka kada kuri’a a kan hakan, yayin da kasashe 11, ciki har da Amurka, suka ki amincewa da hakan, sai kuma wasu 11 da suka ce ba ruwansu.
Kudirin da aka amince da shi ya sake tabbatar da alhakin Majalisar Dinkin Duniya game da batun Falasdinu tare da yin kira da a kawo ƙarshen mamayar Isra’ila a yankunan da aka mamaye tun 1967, yayin da yake goyon bayan samar da kasashe guda biyu a matsayin mafita.
Babban taron ya kuma amince da wani kuduri, wanda Masar ta gabatar, yana kira ga Isra’ila da ta janye daga Tuddan Golan na Siriya tare da bayyana mamayar a matsayin haramtacce.
An amince da kudurin da kuri’u 123, sai 7 da suka ki, da kuma 41 da suka ce akai kasuwa. Amurka tana cikin waɗanda suka yi adawa da shi.
Wannan kuduri ya bayyana cewa mamaye da kuma kwace Golan da Isra’ila ta yi ya saba wa kuduri mai lamba 497 na Majalisar Tsaro, wanda aka amince da shi a shekarar 1981. A cikin sharhin farko da ta yi bayan amincewa da kudurin, Ma’aikatar Harkokin Wajen Siriya ta bayyana cewa “tana kira ga Isra’ila da ta janye daga dukkan tuddan Golan da ta mamaye.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Taron IMO : Tehran Ta Yi Watsi Da Zarge-zargen Isra’ila Marasa Tushe December 4, 2025 Rundunar Ruwa ta IRGC na Gudanar Da Atisayen Soja a Tekun Fasha December 4, 2025 Dan wasan Taekwando Na kasar Iran Ya Samua Lambar Yabo Ta Zinariya December 4, 2025 Hamas Za ta Mikawa Isra’ila Samfurin Da Aka Samu A Karkashin Burabutsai A Gaza December 4, 2025 Iran: Tsaron Yankin Tekun Fasha Jan Layi Ne Da Za’a Fuskanci Mayar Da Martani Adan Aka Taba Shi December 4, 2025 Kungiyoyin Kare Hakkin Dan Adam Sun Kira Ga Kasar Kanada Ta Kama Olmert Da Livni December 4, 2025 Majalisa Ta Tabbatar Da Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro December 4, 2025 Jagora: Musulunci Ya Daukaka Mata Matukar Dauka December 3, 2025 MDD Ta Amince Da Kudurori Biyu Masu Yin Tir Da HKI December 3, 2025 An Ga Sojojin Ruwa Na Amurka A Kasar Puerto Rico A Shirinta Na Mamayar Venezuela December 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci