Aminiya:
2025-12-04@12:26:19 GMT

NAPTIP ta daƙile yunƙurin safarar mutum 7 daga Kano zuwa Saudiyya

Published: 4th, December 2025 GMT

Hukumar Hana Safarar Mutane (NAPTIP) shiyyar Kano, ta kama wani mutum da ya yi yunƙurin safarar wasu mata bakwai zuwa Saudiyya.

Jami’an NAPTIP sun kai samame wani gida a Kano a ranar 2 ga watan Nuwamba, 2025, bayan samun bayanan sirri, inda aka ɓoye matan da ake shirin safararsu.

Na gana da Tinubu kan Kanu ba batun sauya sheƙa ba — Gwamnan Abia ’Yan Najeriya suna da ƙwarin guiwa a kaina, ba zan ba su kunya ba — Ministan Tsaro

A cewar Mohammed Habib, Jami’in Hulɗa da Jama’a na NAPTIP a Kano, an ajiye matan a gidan ne yayin da ake shirin tura su Saudiyya domin yin aikatau.

Ya ce, “Bincike ya nuna cewa biyu daga cikin waɗanda aka ceto ’yan Nijar ne, yayin da biyar kuma ’yan Najeriya ne.”

Ya ƙara da cewa, “An kai matan Accra a Ghana, inda aka yi musu biza. Kuma duka aikin da za a musu bashi ne, inda kowacce za ta biya Naira miliyan 10, idan sun yi aikin wahala a Saudiyya .”

NAPTIP ta bayyana cewa an riga an kammala shirin tura matan filin jirgin saman Abuja a ranar 3 ga watan Disamba, 2025, wanda a nan aka shirya tafiyarsu Saudiyya.

Hukumar ta ce an kama mutum ɗaya, yayin da sauran waɗanda ke da hannu a lamarin suka tsere.

Jami’in, ya tabbatar da cewa hukumar na ci gaba da bincike domin kama sauran da suka tsere.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Safara Saudiyya

এছাড়াও পড়ুন:

Na gana da Tinubu kan Kanu ba batun sauya sheƙa ba — Gwamnan Abia

Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, ya bayyana cewa ziyarar da ya kai wa Shugaba Bola Tinubu, ba ta shafi batun sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar APC ba, sai dai a kan shugaban ’yan awaren ƙungiyar Biyafara, Nnamdi Kanu.

Mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ferdinand Ekeoma, ya fayyace cewa ziyarar ta biyo bayan iƙirarin tsohon Kwamishinan jihar Charles Ogbonnaya.

Mutum 6 sun rasu, 13 sun jikkata a hatsarin mota a Kogi ’Yan Najeriya suna da ƙwarin guiwa a kaina, ba zan ba su kunya ba — Ministan Tsaro

Tsohon Kwamishinan, ya ce Gwamna Otti ya gana da Tinubu ne don tattaunawa shirin sauya sheƙarsa zuwa APC kafin zaɓen 2027.

“Gwamnan ya gana da Shugaban Ƙasa bayan ziyartar Kanu a gidan yarin Sakkwato a ranar Lahadi, 30 ga watan Nuwamba, 2025.

“Batun Kanu ne kaɗai aka tattauna, ba a kan harkokin siyasa ba,” in ji Ekeoma.

Ziyarar da Otti ya kai wa Kanu, na zuwa ne bayan da wata Kotun Tarayya a Abuja, ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai.

Ekeoma, ya bayyana cewa ganawar ta shafi batun yadda za a tattauna kan yiwuwar yi wa Kanu afuwa maimakon hukuncin ɗaurin rai da rai da kotu ta yi masa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Na gana da Tinubu kan Kanu ba batun sauya sheƙa ba — Gwamnan Abia
  • Mutum 6 sun rasu, 13 sun jikkata a hatsarin mota a Kogi
  • Tsaro: Gwamnonin Arewa na shirin dakatar da haƙar ma’adinai
  • ’Yan sanda sun kama mutum 28 kan zargin lalata mata da yara a Yobe
  • Tsaro: Gwamnatin Kano za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa a iyakokinta
  • CBN ya kara yawan kudin da mutum zai iya cirewa a mako zuwa N500,000
  • DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro
  • An kama ’yan bindiga 4 a Kano
  • MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar