Cikakken jadawalin rukunin Gasar Kofin Duniya ta 2026
Published: 6th, December 2025 GMT
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), ta kammala fitar da jadawalin Rukunin Gasar Kofin Duniya ta 2026.
Za a gudanar da gasar ne a Amurka, Kanada da Mexico daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yulin 2026.
Ina nan a PDP duk da sauya sheƙar ’yan majalisar Ribas — Wike DSS ta kama likitan da ke duba ’yan bindiga a dazukan KwaraRabon jadawalin ya gudana ne a birnin Washington na ƙasar Amurka a ranar Juma’a, inda Ingila ta samu kanta a rukuni ɗaya Croatia.
Brazil za ta kara da Maroko, yayin da Amurka za ta kara da Australia.
Faransa za ta ɓarje gumi da Senegal, sannan Argentina za ta fafata da Austria.
Ga jerin yadda kowane rukuni na gasar Kofin Duniya na 2026 ya kasance:
Rukuni A: Mexico, Afirka ta Kudu, Koriya ta Kudu, ƙasar da ta samu gurbin zuwa gasar.
Rukuni B: Kanada, ƙasar da ta samu gurbin zuwa gasar, Qatar, Switzerland
Rukuni C: Brazil, Maroko, Haiti, Scotland
Rukuni D: Amurka, Paraguay, Australia, ƙasar da ta samu gurbin zuwa gasar.
Rukuni E: Jamus, Curaçao, Ivory Coast, Ecuador.
Rukuni F: Netherlands, Japan, ƙasar da ta samu gurbin zuwa gasar, Tunisia.
Rukuni G: Belgium, Masar, Iran, New Zealand.
Rukuni H: Spain, Cape Verde, Saudi Arabia, Uruguay
Rukuni I: Faransa, Senegal, ƙasar da ta samu gurbin zuwa gasar, Norway
Rukuni J: Argentina, Aljeriya, Austria, Jordan.
Rukuni K: Portugal, ƙasar da ta samu gurbin zuwa gasar, Uzbekistan, Colombia
Rukuni L: Ingila, Croatia, Ghana, Panama
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gasar Kofin Duniya Jawadali Ƙwalllon Ƙafa ƙasar da ta samu gurbin zuwa gasar
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka ta soke bada mafaka ga ‘yan kasashen Afirka 10
Gwamnatin Amurka ta sanar da soke bada mafaka ga wasu kasashen duniya 19 wadanda suka hada da na Afrika guda 10.
Wannan matakin, ya zo ne bayan harin da aka kai a Washington kwanan nan, kuma ya shafi kasashe 19, da suka hada da Chadi, Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Libya, Somalia, Sudan, Burundi, Saliyo da kuma Togo, a cewar wata sanarwa da Hukumar Kula da ‘Yan Kasa da Shige da Fice ta Amurka (USCIS) ta fitar.
Sauran kasashen su ne Afghanistan, Burma, Haiti, Iran, Yemen, Cuba, Laos, Turkmenistan, da Venezuela.
Sanarwar ta umarci ma’aikatan hukumar da su “rike duk fom din bukatar Zaman Mafaka, ba tare da la’akari da kasar da bakon yake ba, har sai an sake duba shi.”
Matakin ya shafi ‘yan kasashe 19 da suka shiga Amurka a ranar 20 ga Janairu, 2021 ko bayan haka don tantance duk barazanar da ke akwai ga tsaron kasar da tsarin jama’a.”
Wannan shawarar ta zo ne bayan da Shugaba Donald Trump da Sakataren Tsaron Cikin Gida Kristi Noem suka yi kira da a tsaurara matakan tsaro kan shige da fice bayan harbin da aka yi wa wasu jami’an tsaron National Guard guda biyu a makon da ya gabata a Washington, D.C.
Wanda ake zargin, dan kasar Afghanistan ne mai shekaru 29 wanda aka ba shi mafaka a watan Afrilu, ya shiga Amurka a shekarar 2021 bayan janyewar sojojin Amurka daga Afghanistan kuma ya taba yin aiki a wasu hukumomin gwamnatin Amurka, ciki har da CIA, a cewar kafofin watsa labarai na Amurka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masar Ta Sanar Da Tattaunawa Da Amurka Don Shirya Sake Gina Gaza December 3, 2025 Isra’ila Ta Hana Motocin Agaji 6000 Shiga Gaza Duk Da Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta December 3, 2025 Kasar Qatar Ta Gargadi Isra’ila Game Da ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza December 3, 2025 Sharhi: HKI tana fama da karancin sojoji a dukkan rassan sojojin kasar December 2, 2025 Shugaba Pizishkiyan: Goyon Bayan Al’ummar Iran Ga Tsarin Musulunci Ne Ya Hana Abokan Gaba Cimma Manufa December 2, 2025 Shugaban Kasar Najeriya Ya Nada Janar Chiristopher Musa ( Ritaya) A Matsayin Ministan Tsaro December 2, 2025 Nigeria Ta Bai Wa Dan Takarar Shugabancin Kasar Guine Bissau Mafakar Siyasa December 2, 2025 Palasdinu: Sojojin “Isra’ila” 3 Su Ka Jikkata Sanadiyyar Taka Su Da Mota December 2, 2025 Hamas Ta Caccaki Isra’ila Game Da Hana Shigar Da Kayayyakin Agaji A Yankin Gaza December 2, 2025 Ministan Tsaron Najeriya Ya Mika Takardar Ajiye Aiki Ga Shugaban Kasa Ahmad Tinubu. December 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci