Nigeria: Har Yanzu Da Akwai Daliban Makaranta 250 Da Suke Hannun Masu Garkuwa Da Su
Published: 6th, December 2025 GMT
Makwanni biyu bayan da masu garkuwa su ka sace kananan yara ‘yan mamaranta an bayyana cewa;har yanzu da akwai 250 a hannun barayin mutanen.
A ranar 21 ga watan Nuwamba ne dai masu dauke da makamai su ka kutsa cikin wata makaranta ta majami’ar Roman Katolika, su ka yi awon gaba da dalibai 300 da kuma malamai.
Mahukuntan makarantar sun ce dalibai 50 sun iya tserewa daga hannun wadanda su ka yi garkuwar da su, don haka har yanzu da akwai wasu 250 da suke a hannun barayin.
Sace daliban da aka yi na bayan nan, shi ne mafi muni,tun wanda aka yi wa daliban makarantar Chibok a 2014 da adadinsu ya kai 276 a hannun Bokoharam.
Jami’an tsaron kasar ta Najeriya sun ce ana ci gaba da kai gwauro da mari domin ganin an ‘yanto da daliban dake hannun barayin, sai dai iyayen yaran suna ci gaba da zama cikin damuwa a zullumi.
Satar mutane domin samun kudin fansa, ya zama ruwan dare a kasar Najeriya,musamman a arewacinta, inda barayin daji suke kama mutane da zummar samun kudin fansa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Putin Na Rasha Ya Ce; Kasarsa Da India Za Su Kara Girman Kasuwancinsu December 6, 2025 Na’im Kassim Ya Yi Suka Akan Shigar Kasar Cikin Kwamitin Tattaunawa Da “Isra’ila” Kai Tsaye December 6, 2025 Gwamnatin Iraki Ta Kore Saninta Da Shigar Da Sunayen Hizbullah Da “Ansarullah” A Cikin Na ‘Yan Ta’adda December 6, 2025 Limamin Tehran: Idan Abokan Gaba Su Ka Sake Yin Kuskure Akan Iran Za Su Sake Cin Kasa December 6, 2025 Iran Da Pakisatan Sun Amince Da Farfado da Layin Dogo Tsakanin Istambul, Tehran Zuwa Islamabad December 5, 2025 Iran Ta Raya Ranar Haramta Takunkuman Bangare Guda A Duniya December 5, 2025 Trump Ya Yabawa Rwanda Da Kongo DMK Kan Sulhuntawa A Yakin Gabancin Kongo December 5, 2025 Najeriya: Tinubu Ya Nada Wasu Karin Jakadu 65, Sanatoci Da Tsoffin Gwamnoni Na Daga Cikinsu December 5, 2025 Shin Ziyarar Putin a Indiya alama ce da ke nuna cewa New Delhi na yin watsi da gargadin Trump? December 5, 2025 Iran Ta Mayar Da Martani Kan Sanarwar Bayan Taron Majalisar Kasashen Yankin Tekun Fasha December 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Gurfanar da Iyayen Yaran da Ba Sa Zuwa Makaranta
Daga Aliyu Muraki
Hukumar Ilimi Matakin Farko ta Jihar Nasarawa (NSUBEB) ta yi barazanar kamawa tare da gurfanar da iyayen da ‘ya’yansu ba sa zuwa makaranta a jihar.
Shugaban Hukumar, Dr. Kasim Mohammed Kasim ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a matsayin wani bangare na ayyukan babban taron inganta ilimi da hukumar ta shirya.
Dr. Kasim Mohammed Kasim ya ce, ilimin boko matakin farko haƙƙin kowanne yaro ne, ba gata ba, kuma ya sha alwashin tabbatar da cewa ba a bar wani yaro a baya ba.
Shugaban Hukumar ya bayyana cewa hukumar ta yanke shawarar gudanar da gagarumin wayar da kan jama’a ta hanyar tarurrukan jin ra’ayoyin jama’a, da kafofin watsa labarai domin jaddada muhimmancin ilimin boko na a matakin farko ga kowane yaro a jihar.
Dr. Kasim Mohammed Kasim ya ce sun sayi motocin bas guda bakwai da za a gudanar da wayar da kan jama’a a dukkan sassan kananan hukumomi 13 na jihar, domin fadakar da iyaye muhimmancin kai ‘ya’yansu makaranta.
Game da babban taron, Dr. Kasim Mohammed Kasim ya ce wannan taro zai hada manyan masu ruwa da tsaki ciki har da masana ilimi, jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, masu tsara manufofi, iyaye, malamai da sauransu.
Ya ce, mahalarta taron za su tattauna hanyoyin magance matsalolin ilimi, musayar kwarewa da sabbin dabaru domin kara inganta koyarwa da koyo a jihar.
Ya lissafo wasu daga cikin matsalolin da suka hada da ginin makarantu marasa inganci, karancin kujeru, karancin malamai, yawan rashin zuwa aiki daga ma’aikata, da rashin daidaitaccen tsarin tura malamai, da sauransu.
Ya ce hukumar ta maida malamai 1,900 wadanda a da ke aiki a ofis-ofis zuwa azuzuwa domin koyarwa, kuma nan ba da jimawa ba za a dauki sabbin malamai 1,000 domin cike gibi a makarantun jihar.