Gidauniya Ta Rabar Da Buhun Takin Zamani 6,000 Ga Manoma A Bauchi
Published: 14th, August 2025 GMT
“Kowa ya sani wadatar abinci yana ɗaya daga cikin alamun da ke nuna kyautatawar tattalin arziki na ƙasa baki ɗaya, don haka ne muka himmatu wajen ba da namu gudunmawar ta wannan fannin.”
Ya kara da cewa, an kafa gidauniyar ne domin taimakawa a ɓangaren kiwon lafiya, ilimi, tattalin arziki wanda rabon takin na daga cikin shirin gidauniyar na bunƙasa tattalin arziki, da kuma kyautata ci gaban al’umma.
“Wannan shi ne karo na huɗu da wannan gidauniyar ta ke rabon taki duk shekara ga manoma masu ƙaramin ƙarfi da ba za su iya sayen takin a irin wannan lokacin da gona ke buƙata ba.”
“An ware buhun taki guda 6,000 da za a rabar wa manoma masu ƙaramin karfi a dukkanin faɗin jihar Bauchi,” in ji shi.
‘Yanmaza ya nuna cewa an yi tsari na musamman domin tabbatar da asalin waɗanda aka zaɓo ne za su amfana da takin, ya yi gargaɗi kan cewa duk wanda aka kama da kauce wa asalin tsarin da aka samar da takin domin su zai ɗanɗana kuɗarsa.
Shi ma da ya ke ƙarin haske, jami’i a gidauniyar, Isyaka Isma’i Wunti, ya ce bayan ƙaddamar da rabon a cikin garin Bauchi za a zaga sauran shiyyoyin Bauchi da sauran yankuna domin yin rabon domin tabbatar da takin ya shigo hannun manoma a lungu da sako a na jihar.
Ya yi gargaɗin cewa kada waɗanda aka raba musu takin su je su sayar, ya nemi su tabbatar sun yi amfani da su ta hanyoyin da suka dace domin bunƙasa harkokin abinci da wata jihar da kayan abinci.
Ya kuma ce an yi adalci sosai wajen zaɓo masu cin gajiyar shirin a kowani lungu da sako. Inda ya ce an yi tsarin sosai na yadda asalin manoma kuma masu ƙaramin karfi ne za su amfana da tallafin.
Emmanuel Samson, daga cikin masu cin gajiyar tallafin, ya gode wa wanda ya assasa gidauniyar, Alhaji Bala Maija’ama Wunti bisa wannan tallafin, ya ce tallafin zai taimaka musu matuƙa wajen amfanin gona.
Salisu Muhammad Maidawa, ya ce, “Ba abin da za mu ce sai godiya ga wanda ya assasa wannan gidauniyar, yadda yake faranta wa jama’a rai ta fuskokin rayuwa daban-daban muna roƙon Allah ya faranta masa rai, abun da ya ke nema na alkairi Allah ya cika masa.”
“A zahirin gaskiya wannan tallafin ya zo a kan gaɓa domin kamar muna tsananin halin buƙatar takin zamani sai kuma ga shi Allah ya sa zan samu kyautarsa.”
Da yawan waɗanda suka ci gajiyar sun sha alwashin amfani da takin ta hanyoyin da su dace ba tare da sayarwa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa
Fitaccen malamin addinin Musulunci nan daga Jihar Bauchi, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya rasu.
Ɗansa, Sayyadi Ali Dahiru Usman Bauchi ne, ya tabbatar wa Aminiya rasuwar malamin.
Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban AmurkaYa ce sun karɓi wannan ƙaddara tare da gode wa Allah bisa rayuwar da malamin ya yi.
“Tabbas Sheikh ya koma ga Mahaliccinsa. Daga Allah muke, kuma gare Shi za mu koma,” in ji Sayyadi.
“Lokacin Sheikh ya yi. Mun gode wa Allah Maɗaukaki. Ya bai wa Sheikh tsawon rai, kuma rayuwarsa ta yi kyau. Alhamdulillah,” in ji shi.
Sayyadi, ya ce zuwa yanzu ba su yanke inda za a yi jana’izar malamin ba.