Aminiya:
2025-12-04@13:46:06 GMT

Tinubu ya naɗa tsohon kantoman Ribas da Dambazau a matsayin Jakadun Najeriya

Published: 4th, December 2025 GMT

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya naɗa tsohon shugaban rundunar sojin ruwa kuma tsohon Kantoman jihar Ribas, Ibok-Ete Ekwe Ibas a matsayin Jakadan Najeriya.

Tinubu ya kuma naɗa Ita Enang, tsohon sanata da uwargidan tsohon gwamnan jihar Imo Chioma Ohakim da tsohon ministan cikin gida kuma tsohon shugaban rundunar sojin ƙasa Abdulrahman Dambazau, a matsayin jakadun.

’Yan sandan Borno sun kama matashin da ake zargi da kashe makwabciyarsa da wuƙa Jirgin fadar shugaban ƙasa ya ƙi sayuwa wata 5 bayan saka shi a kasuwa

Sunayensu nasu na zuwa ne ’yan kwanaki bayan Tinubu ya aike wa Majalisar Dattijai jerin farko na waɗanda yake son nadawa a matsayin jakadun.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya karanta wasikar sabbin naɗe-naɗen a gaban majalisar a yayin zamanta na ranar Alhamis.

A cikin wasikar, shugaban ƙasa ya roƙi ’yan majalisa da su yi gaggawar duba sunayen domin bai wa gwamnati damar cike muhimman guraben jakadun.

Akpabio ya mika jerin sunayen ga kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ƙasashen waje, tare da umarnin cewa kwamitin ya kammala tantancewa ya kuma dawo da rahoto cikin mako guda.

Shugaban ƙasa a baya ya naɗa tsohon mai ba da shawara na fadar shugaban ƙasa Reno Omokri da tsohon ministan sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode da tsohon shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin jakadu.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Ministan Tsaron Najeriya  Ya Mika Takardar Ajiye Aiki Ga Shugaban Kasa Ahmad Tinubu.

Rahotanni da suka fito daga Najeriya sun nuna cewa ministan tsaro Alh mohammadu Badaru Abubakar a ranar 1 ga watan Decemba ya mika takardar ajiye aiki a matsayinsa na ministan tsaron kasa, saboda wasu dalilai da suka shafi lafiyarsa,

Kamar yadda kakakin shugaban kasa Bayo Onanuga ya bayyana cewa shugaba tinubu ya amince da takardar neman ajiye aikin,  kuma ya gudemasa game da gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kasarsa, tuni kuma aka fara lalubo wanda zai maye gurbinsa domin mika sunansa ga majalisa don a tantance shi.

Badaru Abubakar dan shekara 63 da haihuwa shi ne gwamnan jihar jigawa har na tsawon zango biyu wato daga shekara ta 2015 zuwa ta 2023 kuma shugaban kasa tunubu ya  nada shi a mukamin minister a ranar 21 ga watan Agusta shekara ta 2023

Ya ajiye aikin ne adai dai lokacin da shugaba tunubu ya sanya dokar ta baci kan tsaro a fadin kasar,da zimma kawo karshen matsalar tsaro da kasar take fama da shi .

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Bata Taba yin Watsi Da Diplomasiya Ba Amurka Ce Ke Kai Mutane Bango December 2, 2025 Shugaban Kungiyar ECOWAS  Ya Gana Da Shugaban Mulki Soji Na Kasar Guinea Bissau December 2, 2025 An Bude Taron Bikin Cika Shakaru 41 Da Kafa Kungiyar Tattalin Arziki Ta ECO A nan Tehran December 2, 2025 Araghchi: Halayyar Amurka ce yin matsin lamba maimakon diflomasiyya a dangantaka ta kasa da kasa December 2, 2025 Aljeriya: Taron Kasashen Afirka Don Amincewa Da Mulkin Mallaka A Matsayin Laifi December 2, 2025 Lebanon: An Gudanar Da Taron Musulunci da Kiristanci a Beirut tare da halartar Paparoma December 2, 2025 Chuck Schumer: Trump Ba Shi da Ikon Kaddamar da Yaki Kan Venezuela December 2, 2025 Najeriya: Matatar Dangote Za Ta Mika Tataccen Mai Lita Biliyan 1.5 A Watan Disamba December 2, 2025 Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Trump na ware Afirka ta Kudu daga G20 December 2, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 165 December 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jirgin fadar shugaban ƙasa ya ƙi sayuwa wata 5 bayan saka shi a kasuwa
  • Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Sabon Shugaban Hukumar Kidaya, Kwamishinoni da Manyan Sakatarori
  • Yau Majalisar Dattawa za ta tantance sabon Ministan Tsaro
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Nada Janar Chiristopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro
  • Shugaba Tinubu Ya Nada Janar Christopher Musa Sabon Ministan Tsaro
  • Tinubu ya naɗa Janar CG Musa sabon Ministan Tsaron Nijeriya
  • Ministan Tsaron Najeriya  Ya Mika Takardar Ajiye Aiki Ga Shugaban Kasa Ahmad Tinubu.
  • Tinubu ya gana da Janar Christopher Musa bayan Ministan Tsaro ya yi murabus
  • Tinubu ya gana da Janar Christopher CG Musa bayan Ministan Tsaro ya yi murabus